Tuesday, June 9, 2026

Amfanin Kanamfari Guda 11

Amfanin Kanamfari Guda 11


YADDA ZA'A YI AMFANI DA KANUMFARI WAJEN NEMAN LAFIYA

1.CIWON KAI
(A), Yana maganin ciwon kai. A shafa
man kanimfari a goshi, Yana taimakawa
wajen ciwon kai wanda ke faruwa sanadiyar mura.

(B), Idan kuma ciwon kan bana Mura bane, za'a iya samun Kanumfari guda biyar a saka a cikin ruwa kofi guda, a saka a wuta su tafasa sosai sai a saka Suger kamar Rabin cokali a ciki idan
ya dan huce sai a sha ayi haka sau 2 a yini In shaa Allahu kan zai daina ciwo koda kuwa baya jin Magani ne.


2. CIWON HAKORI
Yana maganin ciwon hakori. Zaka
iya amfani da man-kanimfari (clove oil)
ga hakori mai-ciwo ko kuma kanimfarin
(dakakke) , a jikashi kadan da ruwa a
lika wajen hakori mai-ciwo. Idan mai
( clove oil) kake amfani dashi sai asamu auduga a zuba man kadan a lika wajen hakori mai-ciwo (ka danne da hakora).


3.WARIN BAKI
Za’a iya amfani dashi a matsayin abun wanke baki. Yana maganin warin baki (a tafashi a yawaita wanke baki dashi sau 3 a rana).


4.MAGANIN AMAI
(A), Domin Tsayawar amai ga Mata masu ciki, a daka kanunfari biyu a sa babban cokali daya na zuma a sha yana maganin Amai ga macce mai ciki.

(B),Don magance amai baga mai juna biyu ba kuwa, a saka kanumfari 4 a cikin ruwa kofi daya a tafasa idan ya tafasa a saka sugar cokali daya a sha.


5.TYPHOID
A samu ruwa littr biyu sai a saka kanumfari kamar guda 5 a cikin ruwan a tafasa ruwan kada a sauke sai ruwan sun koma sauran littr daya sai a sauke idan suka huce sai a riqa sha Wannan yana Maganin typhoid.


6. Ciwon Kunne;
A hada Man kanun fari da Man Ridi diga a kunne mai ciwo duk lokacin da za'a kwanta wannan yana maganin ciwon kunne.

7.MAGANIN MURA
Ga masu su mura A tafasashi da citta/jinja (ginger) a sha shayi.


8. MAGANCE MAKERO/KYANDA
Ana goga Man kanumfari a wurin da matsalar tace wannan yana maganin Makero.

9. GIRMAN MAZAKUTA
Asamu nikakken kanumfari ko adakasa sai ajikasa da mansa ahada da man zaitun, sai ajika "gaba" dashi,idan za'a kwanta,da rana kuwa duk bayan anyi
wanka sai ashafa, wannan yana sa girman Azzakari.

10. KARFIN MAZAKUTA
A samu Man kanumfari duk za'a yi saduwar aure awa daya kafin a fara a shafe gaba da shi.


11. KURAJEN HARSHE
Don Magance Kurajen Harshe, daka Kanumfari a saka a harshen a barshi zawon wani lokaci, ko kuma idan za'a kwanta a saka in shaa Allahu kafin safe zasuyi dama.




 



Mura mai tsanani

YADDA ZAKU MAGANCE TARI DA MURA CIKIN SAUKI.

Asamu tafarnuwa kamar sala huɗu sai abare ayayyankashi kanana.
- Asamu Ginger ɗanyen citta mai yatsu kamar kwaya biyu sai aɗan daddakashi yaɗan farfashe.
- Asamu ƴaƴan habbatussauda babban cokali biyu.
-Asamu ruwa cikin matsakaicin kofin shayi biyu.



Sai ahaɗa awaje ɗaya atafasa bayan yatafasa sosai sai asauke akan wuta atsiyaye, daga bisani sai babban mutum yasha kofi ɗaya dasafe daya dayamma bayan yasa zuma cokali hudu aciki, yaro kuma abashi rabin kofi safe dayamma, jinjiri kuma abashi cikin babban cokali biyu safe dayamma. Insha Allahu wannan haɗin zai taimaka sosai masamman awannan lokacin sanyin.



CIWON MARA NA UKU

CIWON MARA NA UKU

5. Hadin Habbatus Saudah.

Yadda za ki yi wannan hadi shine, ki samo garin habbatus sauda da garin hulba da kuma garin kusdul hindi ( kowannensu cikin karamin cokali daya) sai ki tafasa su a waje guda, sanan ki tace, daga nan sai ki samu zumar ki mai kyau wacce ba ta da mis ki hada da Khal tuffa cokali uku ki ke sha. Wannan ma hadi ne da aka jarrba kuma ya na da kyau matuka.

6. Kirfa (Cinnoma).

Za ki samu, Kirfa (Cinnamon) ki dinga tafasawa ki na sha, ta na maganin Ciwon mara alokacin alada. Kuma mujarrabi ne.

7. Man Zaitun.

Shi kuma yadda za a yi shine, a Karanta ayoyin Alqur'ani a tofa cikinsa sannan Mace ta rika shan cokali guda safe da yamma kullum har zuwa lokacin zuwan Jinin al'adarta. Kuma zata rika shafawa ajikinta har Mararta (Amma banda al'aurarta). Shi ma wannan hadin an gwada shi kuma an dace.


Na'a na'a

Amfanin Na'a na'a a jikin Dan adam.

Tana magance matsalar bacin ciki da rashin fitar bahaya mai sa tsugunno a bayi. A yi shayin na’a-na’a ko a zuba manta cikin shayi marar madara sai a sha.

Tana saukake narkewar abinci.

Ta kan taimaka wajen narkar da abinci yadda sassan jiki za su yi amfani da shi.

Tana maganin mura da tari da kuma mura mai damun makoshi. A yi amfani da man na’a-na’a ko ganyen, a tafasa ganyen a yi shayi marar madara, haka kuma, za a iya amfani da man na’a-na’a cikin ruwan zafi, a yi turiri, a lullube da mayafi. Wannan shi ma yana maganin mura ana bude baki yadda tiririn zai shiga cikin makoshi, domin shigar tasa ce za ta sa a samu saukin murarar.

In kuma akwai majinar kirji duk zai taimaka wajen fitar da ita, ya washe kirjin tare da makogwaro.

Maganin ciwon kai. A shafa manta wajen da kai ke ciwo. Maganin ciwon jiki. A shafa manta ga jijiyoyin jiki dake ciwo ko wajen dake damunka da ciwo, za a samu sauki in sha Allahu.

Maganin ciwon hakori. A yi amfani da man na’a-na’a da auduga, a diga man ga auduga , sa’annan a lika ga hakori mai ciwon.

Maganin kaikayi. Za a iya shafa manta a wajen da yake kaikayin. Korar sauro. A shafa man na’a-na’a a ga jiki hannuwa da kafafu, sauro zai gujesu. Kashe tsutsar ciki. Taimakawa hanta wajen aiki. Rage yawan damuwa.

Tana hana damuwa, a tafasa ganyen na’a-na’a a yi shayi, ko manta a zuba a cikin kofin shayi, safe da yamma.

Tana taimakawa kwakwalwa wajen rike karatu da kaifin fahimta. A yi shayi da ganyen na’a-na’a a rinka sha da zuma.

Tana sanya girki yayi kamshin filebo. A yi amfani da ganyen wajen girki. Hakan zai taimaka wajen son cin abincin musamman ga wanda baya son cin abinci.




Maganin Maza


ASSALAFY ISLAMIC MEDICINE CENTER

Masturbation (istimna'i)

ILLOLIN ISTIMNA'I WATO
(MASTURBATION)


Istimna'i wato(MASTURBATION)wata hanya ce da maza da mata suke bi domin biyawa kawuna su bukata,ta hanyar amfani da hannu,ko kuma wani nau'in abu wanda zai biya musu bukata.
Yin istimna'i ga mace ko namiji yana cutar da lafiyar mutum matuka, domin yana jawowa mutum cututtuka masu wuyar magani.
KADAN DAGA ILLOLIN SA GA MAZA.
  • 1. Kankancewar azzakari
  • 2. Saurin kawowa
  • 3. Fitar farin ruwa daga gaba
  • 4. Raunin jiki
  • 5. Yawan kokonto
  • 6. Rashin nutsuwa
  • 7. Saurin tsufa
  • 8. Yamushewar fatar jiki
  • 9. Fitsarin jini
  • 10. Jin zafi yayin fitsari.
ILLOLIN SA GA MATA.
  • 1.Lalacewar farji
  • 2. Bushewar farji
  • 3. Fatar farin ruwa daga farji
  • 4. Daukewar sha'awa
  • 5. Fìtowar kuraje daga farji
  • 6. Gusar da budurcin ya mace.
  • 7. Yamushewar fatar jiki.
  • 8. Saurin kawowa yayin saduwa.
  • 9. Yawan kokwanto da rashin nutsuwa.
  • 10.Zobewar Nono.

Hanyoyin kariya daga afkawa istimna'i
1. Dena kallon finafinan batsa
2. Rage mu'amala da matan da ba muharraman ka ba,indai ba dole ba,kamar business.
3. Dena yin duk wani abu da yake jawo wa sha'awar ka ta motsa.
Shawara ta ta karshe.
Allah ya tsaremu



Don kara karfin mazakuta

BANDA MARASSA AURE


Idan ka san baka da aure kar ma ka tsaya bata lokaci wajen karanta wannan fa'idah mai matukar amfani ga ma'aurata

Ina kuke 'yan uwana ma'aurata? ga tsaraba daga gurin 'dan uwanku Datti Assalafiy

Ga wani Mujarrab ku gwada yana da matukar tasiri da armashi a babin raya sunnah ta Ma'aiki (SAW)
Kawai ku je shago, ku sayo Fearless da Peak Milk, sai a sayo ayaba ta naira 100 kacal ya isa

Bude murfin Fearless din, a juye madaran Peak Milk a ciki, a jijjiga sosai, sai ka shanye abinka tas kar ba bawa uwargida, bayan kaci ayaba kamar guda 4 ko 2 ma ya wadatar

Ma'aurata zakuyi wannan hadin ne bayan mintuna 30 kafin a kai ga raya Sunnar Manzon Tsira Annabi Muhammad (SAW), maza kadai zasuyi banda mata

Ku gwada,

sai dai ina muku fatan alheri tuzurai maza da mata, Allah Ya aurar daku ku dandana dadi da albarkan da muke sha a gidan aure.





Mu'jizar da ke cikin Zaitu

Amfanin Man zaitun


Ciwon Ciki: Duk mutumin da yake ciwon ciki sai ya samu man zaitun kamar cikin cokali ya hada da garin habbatus sauda ya cakuda ya sha safe da yamma. Ya sa mu kamar sati daya yana sha, in sha Allahu zai bari.

CIWON KAI: Duk mutumin da yake ciwon kai to sai ya samu man zaitun yana shafawa a kansa yana kuma shan cokali daya da safe da rana da dare.

Ciwon Hakori: Duk mutumin da yake ciwon hakori sai ya samo ganyen zaitun da ‘ya’yan habbatussauda ya saka su a cikin garwashi ya buda bakinsa hayakin ya dinga shiga.

Ciwon Hanta: Duk mutumin da ya kamu da wannan ciwo sai ya dinga shan man zaitun cikin cokali daya da safe daya da rana daya da dare.

Ciwon Dasashi: Duk mutumin da yake ciwon dasashi sai ya samu man zaitun ya dinga wanke bakinsa da shi.

Ciwon Sukari: Duk mutumin da ya kamu da ciwon sukari to sai ya samu man zaitun da tsamiya yana hadawa yana sha kafin ya kwanta bacci.

Ciwon Asma: Duk mutumin da wannan ciwon ya kamashi, to sai ya samu ganyen zaitun ko ‘ya’yansa ya dinga turarawa.

Ciwon Koda: Duk mutumin da yake ciwon koda, to sai ya dinga shan man zaitun cikin cokali uku a rana.

Ciwon Baya: Duk mutumin da yake ciwon baya, to sai ya samu man zaitun da garin habbatussauda a kwaba ya dinga shafawa a bayan.

Ciwon Rama: Duk mutumin da ya ga yana ramewa, to ya dinga shan man zaitun kullum cokali uku, in sha Allahu zai yi kiba.

Zazzabi Mai Zafi: Duk mutumin da ya kamu da zazzabi mai zafi to sai ya dinga shan man zaitun cokali daya, sannan yana karanta Ayatul kursiyyu sau 7, yana tofawa a cikin yana shafe jikinsa da shi.

Kyawun Fuska: Duk mutumin da yake so fuskarsa ta yi kyau, ta yi fari wanda ba zai cutadda shi ba, to ya dinga shafa man zaitun da man habbatussauda in zai kwanta bacci bayan ya tashi da safe ya wanke da sabulun salo zai yi mamakin yadda fuskarsa za ta koma.

Zubewar Gashi: Duk maccan da gashinta baya futowa sosai ko in ya futo sai ya zube, to sai ta samu ruwan zafi ta wanne kanta da shi, sannan bayan ya dan huce sai ta zuba man zaitun a hannunta, sai ta shafe kannata da shi gaba daya kullum.

Karancin Jini: Duk mutumin da yake da karanci jini a jikinsa to sai ya dinga shan man zaitun cokali biyu a rana.

Bayan Gida Mai Kauri: Duk mutumin da yake shan wahala in ya zo zai yi bayan-gida, wani ma sai ya yi kuka saboda wahala, to sai ya samu man zaitun da garin habbatussauda ya kwaba sai ya tura shi a cikin duburarsa.

Ciwon Mara Ga Mata: Duk matar da take haila tana fama da ciwon mara saboda fitar jini in tana so ta samu saukin wannan ciwon, sai ta samu man zaitun tana hadawa da ruwan tsamiya tana sha, in sha Allahu duk lokacin da za ta yi haila ba zai mata ciwo ba.

Kurajen Karzuwa: Duk mutumin da yake da karzuwa ko wasu kuraje, to sai ya samu ganyan zaitun ya kirba shi ya hada da garin habbatussauda yana shafawa a wajan har ya warke.

Ciwon Kunne: Duk mutumin da yake ciwon kunne, to sai ya bari in zai kwanta bacci sai a dinga hada man zaitun dana habbatussauda yana digawa a kunnansa.

Cutar Kyasfi: Duk mutumin da yake da kyasfi a jikinsa, to sai ya samu ganyen zaitun busasshe, ya daka shi ya yi laushi sai ya hada shi da man zaitun ya cakuda, ya dinga shafawa a wajen lokacin da zai kwanta bacci.

Shafar Aljanu: Duk mutumin da yake so ya rabu da aljanu, to ya dinga amfani da man zaitun saboda aljanu ba sa son shi. Don haka yana da kyau mutum ya lazimci amfani da shi a kowane hali, in da hali ma ya mai da shi mansa na shafawa.

Ciwon Kakkare: Duk mutumin da ciwon kakkare ya sa me shi, to sai ya samu man zaitun, sannan a samu lalle a kwaba, sai a zuba man zaitun din a cikin lalle a gauraya, sannan a karanta (Ayatul Kursiyyu) sau 7, a tofa a ciki sannan sai a tofa a jikin wannan karkare.

Ciwan Nono: Duk matar da take fama da ciwan nono, to ana hada man zaitun da garinsa a barbada a kan nonon saboda samun damar zuba, dan kofofin su bude.

Ciwon Saifa: Duk mutumin da yake ciwan saifa, sai ya hada man zaitun da garin habbatussauda da kuma zuma farar saka ya sha.

Tsutsar Ciki: Duk mutumin da yake da tsutsar ciki, to sai a samu man zaitun da garin habbatussauda da zuma ya kwaba su ya sha, wannan tsutsar za ta mutu.

Ciwon Hanji (Ulcer): Duk mutumin da yake da gyanbon ciki, to sai ya samu garin habbatussauda kamar cokali daya sannan ya samu garin kumasari da ganyan zaitun mai laushi ya jika su ya dinga sha har sai ya warke.

Fitsarin Kwance: Duk yaro da yake fitsarin kwance, to sai a samu garin zaitun dana habbatussauda a zuba a nono a dinga ba shi yana sha zai dai na.

Mutuwar Jiki (Kasala): Duk mutumin da jikinsa yake yawan mutuwa to sai ya dauwama yana shan zuma da garin habbatussauda zai ji karfin jikinsa.

Yawan Zazzabi: Duk mutumin da yake yawan yin zazzabi, to sai ya samu garin habbatussauda kamar cikin ludayi ya kwaba da ruwan zafi da kuma zuma mara hadi ya dinga sha.

Ciwon Gabobi: Duk mutumin da gabobinsa suke ciwo, to sai ya samu garin habbatussauda da zuma ya dinga sha, sannan kuma ya zuba garin habbatussauda a cikin man zaitun ya dinga shafawa a gabobi.

Kwarkwata: Duk matar da take fama da kwarkwata kuma har take son rabuwa da ita, to ta samu man zaitun da garin habbatussauda ta kwaba sannan sai ta bari sai rana ta take sai ta zuba wannan man a kanata ta bar shi ya yi kamar minti 20, sannan sai ta wanke.

TARI: Duk mutumin da ya kamu da kowani irin tari, to sai ya samu garin habbatussauda da man zaitun da ‘yar citta da tsamiya da zuma, sai ya hada su guri daya ya cakuda ya dinga ci.

Majinar Kirji: Duk mutumin da yake yawan majinar kirji, to sai ya samu man zaitun da garin habbatussauda ya hada ya dinga ci kullum sau biyu safe da yamma



CIWON HANTA

ALAMOMIN CIWON HANTA,DA KUMA MAGANINTS


Ciwon hanta na daya daga cikin manyan cututtuka da suke da wuyar magancewa a duniya amma da Yardar Allah duk Wanda yabi abun da zamu fadi za'a samu waraka da Yardan Allah.


ALAMUN CIWON HANTA


Akwai matsanancin ciwon kai da ciwon malariya da typhoid akai-akai, Haka zakaji ciwon jiki da rashin karfin jiki, ciwon ciki mai tsanani,Yawan haraswa dakuma tashin zuciya koda ruwa kasha,

Ido yakanyi yellow, da rashin dandano a baki, fitsari ya koma yellow, ko matsananci zazzabi da jin sanyi ,bayan gidan mutum yakan koma kalan kasa.


Ga duk Wanda yaji wadannan alamu sai yayi kokarin zuwa asibiti domin Gwaji A daina tsoron gwaji domin magance cutar tana farkonta yafi sauki akan sanda zata tsananta.

Masu ulcer dake yawan ciwon ciki da yawan haraswa da tashin zuciya suna magani ba sujin sauki suyi kokarin duba lafiyar hantar su domin takan hadu da masu ulcer sosai.


MAGANINTA


1. A samu garin habba cokali 10
2. Garin Sidir cokali 5
3. Garin tin cokali 5
4. Garin bawon kankana cokali 10
5. Garin Citta cokali 1
6. Garin tafarnuwa cokali 1
7. Garin Hidal cokali 5
8. Garin zogale cokali 3
9. Garin Yansun da raihan da kusdul hindi cokali 6

Sai a hadasu waje daya a samu Zuma lita biyu mai kyau sai a zuba ciki a juya a hadu sosai sai a dinga shan cokali uku sau uku a rana.

Fadakakarwa

A guji amfani da nama musamman Jan nama da sauran abun mai ciwon hanta baya bukata.



GYARAN FUSKA

Shin kin san yadda ake gyaran fuska yayi tsumul-tsumul?

Maganin kuraje pimples da habbatisauda

 

Domin magance matsalar kurajen fuska wanda ake cema pimples.

Za'a samo garin habbatisauda sai ahada da man simsim sai kuma ahada shi da garin alkama cokali daya, sai ashafa a fuska idan zaa kwanta, da safe kuma sai awanke fuska da ruwan dumi, da kuma sabulu, malam mutum zai cigaba da yin wannan har zuwa Sati daya.

 

Malam yace kash inama da ace bayan haka kuma kasamo zait habbatil baraka kana zubawa kadan acikin wani nauin abin shanka mai sanyi. Insha ALLAH dakayi mamaki.

 

MAGANIN KURAJEN FUSKA 

 

Matsalar kuraje da tabon fuska sun fi shafar matasa, mata da maza.

Wani lokaci sai an sha wahalar magance kurajen fuska, amma sai tabo ya ki bacewa.

Rashin bacewar tabo a fuska na bata kwalliya.

Sau da yawa za a ga ba a son shiga taron mutane domin wadannan tabon.

Da yawan mutane sun gwada mayukan kantin, domin rabuwa da tabon fuska.

Wasu sun yi sa’a wasu kuma ba su yi sa’a ba.

 

A yau mun zo da bayanin yadda za a magance tabon fuska. Muna son a san cewa daya za a zaba daga cikin hanyoyin da muka lissafo, kada a hada su gaba daya.

 

Domin yin hakan zai kara lahanta fuska ne..

· A samu ganyen dogonyaro, sai a hada shi da kurkum, sannan sai a shafa a fuska. A jira tsawon minti 15, sannan a wanke da ruwan dumi.

· Za a iya shafa markadadden dankalin Turawa a kan tabo.

Hakan na magance kurajen fuska, sannan ya hana su sake fitowa.

· A daka tafarnuwa sai a shafa a kan tabo. Tafarnuwa tana wari, amma tana gyara fuska, sannan ta magance tabon fuska.

· a hada karas da tafarnuwa da zuma sai a shafa a fuska na tsawon minti 20 kafin a wanke.

· A samu hodar ‘baking soda’, sai a hada ta da ruwa, sannan a shafa a fuska zuwa minti 2 ko 3, daga nan a wanke fuska da ruwan dumi

 

Yadda za a magance tabo da kurajen
fuska...
.
Matsalar kuraje da tabon fuska sun fi shafar matasa, mata da maza. Wani lokaci sai an sha wahalar magance kurajen fuska, amma sai tabo ya ki bacewa.
.
Rashin bacewar tabo a fuska na bata kwalliya. Sau da yawa za a ga ba a son shiga taron mutane domin wadannan tabon.
.
Da yawan mutane sun gwada mayukan kantin, domin rabuwa da tabon fuska. Wasu sun yi sa’a wasu
kuma ba su yi sa’a ba.
.
A yau mun zo da bayanin yadda za a magance tabon fuska. Muna son a san cewa daya za a zaba daga cikin hanyoyin da muka lissafo, kada a hada su gaba daya. Domin yin hakan zai kara lahanta fuska ne.
.
A samu ganyen dogonyaro, sai a hada shi da kurkum, sannan sai a shafa a fuska. A jira tsawon minti 15,
sannan a wanke da ruwan dumi.
· Za a iya shafa markadadden dankalin Turawa a kan tabo. Hakan na magance kurajen fuska, sannan ya
hana su sake fitowa.
.
Ko a daka tafarnuwa sai a shafa a kan tabo. Tafarnuwa tana wari, amma tana gyara fuska, sannan ta magance tabon fuska.



Gyaran jiki

GYARAN / TSAFTAR FARJINKI

tsaftar farji Ana so mace Tun tana karama iyaye su rinka yi Mata tsarki da ruwan dumi domin ruwan dumi yana Hana kwayoyin cut a shiga cikin farjinki har lokacin da Zaki mallaki hankalinki ki Dora Daga Inda iyayenki suka tsaya.
Ruwan magarya
Miski
Sannan Daga lokacin da kika Fara al'ada kuma aiki ya karu sai ki rinka amfani da ruwan magarya bayan kin gama al'ada sannan Zaki iya saka miski saboda karni wato Zaki tafasa ruwan tareda ganyen magarya danyensa ko bushashe ki saka miski sannan Kiyi tsarki dashi kamar na kwana 3 zai kashe kwayoyin cutarda Zaki iya dauka a wanna lokacin kuma zai hanaki warin gaba wanna matar aure yana da kyau ta rinka yinsa.
BUDURWA KO YAR'UWA a takaice dai kina ( budurwa ko bazawara ) babu ruwan ki da saka komai a farjinki da sunan matsi kedai ki kiyaye da wannan wato amfani da ( ruwan magarya da miski ) lokacin al'ada.





Sirrin yadda ake mallake Miji ya kauracewa zaman waje

YADDA AKE MALLAKE MIJI...

“Kyautatawa game da tsare wa maza hakkokinsu ne babbar hanyar mallake miji.” Wata mata ce ta je wajen wani malami (mai tsoron Allah) ta ce masa “Allah Ya gafarta Malam so nake ka yi min aiki domin in mallake mijina.”

Sai malamin ya girgiza kai yana mai nuni da jan aikin da ke akwai. Ya ce mata zai yi mata aiki amma da sharadin in za ta kawo masa nonon barewa wanda ta tatso da hannunta.” An ce sa kai ya fi bauta ciwo. Matar nan ta yi shirya ta nufi dokar daji kuma ta yi sa’a ta iske wata barewa ta yi sabuwar haihuwa, sai ta samu wata itaciya ta haye sama ita kuma barewar da ’ya’yanta suna kasa. Sai ya kasance duk lokacin da barewar nan ta tafi neman abinci sai matar nan ta sauka ta dauke ’ya’yan nan daya bayan daya ta aje su gefe guda ta share musu wurin, ta dauke su ta mayar da su wurinsu na asali.

Duk lokacin da uwar ta dawo sai ta iske an share wajen sai ta yi mamaki, har ta kai matar nan tana jinkirta sharar nan har barewar ta dawo ta iske ta tana wannan aiki, haka za ta sa mata ido sai ta gama ta mai da su inda suke. Yau da gobe har ta kai matar nan tana shafa ’ya’yan barewar nan in suna shan nono har tana iya cire wani daga jikin nonon ta sanya wani. In gajarce muku labari saboda kyautatawa har matar nan ta zama tana sarrafa barewar nan duk yadda ta ga dama. A karshe ta dauko ’yar gorarta ta kara jikin nonon barewar nan ta tatsa ta cika ta tattara kayanta sai gida.

Bayan ta koma gida sai ta shirya ta nufi wajen malamin nan rike da gorar nono ta mika masa. Koda ya amsa sai mamaki ya kama shi ya tambaye ta yaya aka yi kika same shi?

Matar nan ta share wuri ta fada masa duk hanyoyin da ta bi har ta samu ta cimma burinta. Sai malamin nan ya gyara zama ya ce ta saurare shi da kyau da kunnen basira.

Ya ce “Har ga Allah duk abin da zai yi mata ba zai yi tasiri ba matukar ba ta bi mijinta ba ta kuma kyautata masa kamar yadda ta yi wa wannan barewa.”

Sai mamaki ya kamata ta ce “Ka fa san maza yadda suke da wuyar sha’ani.”

Sai malamin ya ce “Ta je ya ba ta nan da wata guda idan har ta aikata kwatankwacin abin da ta yi wa barewar nan ba, ta samu kan mijinta ba to ta dawo shi kuma zai yi mata aikin da za ta mallake shi har abada.”

Suka yi ban-kwana ta yi masa godiya ta koma gida. Bayan tsawon wata guda sai ta koma wajen malamin nan rungume da jaka wadda ta shake da kayan arziki ta mika masa kuma ta nuna farin cikinta ganin mafarkinta a yau ya zama gaskiya.

Daga karshe Malam ya ce mata “Wannan shi ne asirin da har abada ba zai kare ba, sai ma karin tagomashi na yardar Allah da za ki samu.”

Domin Annabi (SAW) ya ce “Duk matar da ta mutu alhali mijinta yana mai yarda da ita to za ta shiga Aljanna.” Da wannan nake kira ga matanmu su ji tsoron Allah. Wallahi zuwa wajen boka kafirci ne kuma duk wacce ta mutu a wannan tafarki wuta ce makomarta.

Allah Ya tsare mana imaninmu, Allahumma amin. . 





Mu'jizar da dake tartare a cikin albasa

Amfanin Albasa a jikin Dan adam.

1.Tana Yaki Da Cutar Daji (Kansa) Sakamakon da aka samu daga binciken da aka yi, ya nuna cewar,albasa ta kasu daban daban, saboda an sansu da maganin cutar kansa, musamman ma yadda take girma. Bugu da kari duk dai dangane da binciken da ka yi, idan na mafani da ita akai akai, tana rage yiyuwar kamuwa da cutar kansa daban daban, kamar kansa ta colorecta, oral kansa, kansar mkogwaro, kansar ciki, kansar wurin da abinci ke biya wuce zuwa hanji, sai kuma kansar mahaifa.

2.Tana Yaki Da Cutar Daji (Kansa) Sakamakon da aka samu daga binciken da aka yi, ya nuna cewar,albasa ta kasu daban daban, saboda an sansu da maganin cutar kansa, musamman ma yadda take girma. Bugu da kari duk dai dangane da binciken da ka yi, idan na mafani da ita akai akai, tana rage yiyuwar kamuwa da cutar kansa daban daban, kamar kansa ta colorecta, oral kansa, kansar mkogwaro, kansar ciki, kansar wurin da abinci ke biya wuce zuwa hanji, sai kuma kansar mahaifa

3.Albasa na rage sikarin dake cikin jini Jini wanda ya kunshi sikari mai yawa(hyperglycemia) wannan yana kasancewa ne, lokacin da jinin da ke cikin sikari da ake kira (glucose), yayi yawa fiye da yadda jiki ke bukata, domin yin aiki da shi kamar yadda aka saba. Wannan yanayi shi ne ka sani da samar da matsala nan da nan da kuma wadda ke daukar dogon lokaci. Amfani da Albasa kusan kullun ya nuna cewar tana sa sikarin da yake cikin jini ya ragu, saboda ta kunshi wani sinadarin allyl prppyl disulfide, wanda yake taimakawa, wajen rage yawan glucose, ya kuma kara yawan sinadaran insulin.

4.Tana Kara Karfin Sinadaran dake taimakawa wajen yakar cutar Kamar yadda Anne Maune anda shi kwararre ne danagne da kayayyakin abincin, mai zama a Washington DC, ya bayyana cewar akwai poly phenolds a cikin albasa wanda yake aiki kamar sojojin da ke yakar cutar cuta da ake kira free radicals.




Shin kina da Matsalar da yake damunki?

ASSALAFY ISLAMIC MEDICINE CENTER

MATSALOLIN MATA

domin magance wannan matsala, Ana iya samun kwai daya, a buga Ya kadu sosai sai a sami ganyen ‘ugu’ a matse ruwansa, a samu ruwan ugun rabin kofi ki juye a kan ruwan kwanda ki ka fasa sai kuma ki saka zuma, cokali uku ki kuma kada wa sosai, ki zuba madarar gari cokali biyu kici gaba DA kada wa soaai sai ki Kara zuba lemun tsami bari daya don ki rage karnin ki kuma bugawa sai ki shanye idan kika yi kwana uku a jere duk bushewar gabanki sai ni’ima ta tsatsafo.

CIWON MARA KO CIWON CIKI
idan mace tana ciwon mara ko ciwon ciki
a lokacin al’ada ko jinin yari kayi mata wasa
  • zuma cokali 5
  • man tafarnuwa cokali 2
in an hada sai ta rika sha cokali 1 DA safe 1 da yamma.

MATAR DA JINI YAKI DAUKE MATA
ta rika shan man tafarnuwa rabin karamin cokali Sau 4 a rana.

MATAR DA TAKE DA KURAJE
a gabanta ko take jin kaikayi a samu man tafarnuwa cikin karamin cokali sai ta matsa lemon tsami daya a cikin sannan ta rinka dan gwala da auguga tana shafawa a gabanta kwana 5 zata warke Insha ALLAH.





ABUBUWA GUDA GOMA DA SUKE SANADIYYAR MUTUWAR AURE

ASSALAFY ISLAMIC MEDICINE CENTER

Abubuwa guda Goma da suke kashe aure

1. Rashin sanin daraja da hakkokin aure
2. Kaucewa koyarwar Manzon Allah game da zamantakewar ma'aurata
3. Girman kai ga maza, rashin kunya ga mata
4. Yin aure saboda kawai don sha'awa, dukiya ko wani son abin duniya
5. Karin aure yayin da babu ikon yi
6. Rashin adalci da wulakanta abokin zama
7. Rashin bin ka'idojin saki
8. Jahilci
9. Rashin son haihuwa
10. Baiwa al'adu muhimmanci fiye da addini

Allah ya bamu ikon kiyayewa


Amarya a gareki...

AMARE DA MASU NIYYAR AURE

wannan wani hadine na musamman wanda ake bukata amare suyi.ko masu niyyar aure.

Da farko sai asamu tatacciyar zuma mai kyau a aje gefe daya sai asamu :

  • DabiNo (ajuwa).
  • Garin hulba cokali 3.
  • Sai asamu man habbatus sauda dan misra maikyau sai garin ridi cokali 5.
  • Sai gyada itama cokali 5.

Sai a hadesu wuri daya su hadu.sai arinka sha cokali 3 safe da yamma.

Ko kuma a samu dabino (ajuwa)a hada da nonon rakumi da garin alkama cokali 4.sai a hadasu wuri daya a damasu a rinka sha sau daya arana da daddare.

Kokuma a hada kwa-kwa da dabino maikyau arinkaci sau daya arana.

bayan nan sai a hada madara da kankana mai kyau amman kankanar za'a jajjagata sai a hadata da madara a rinka sha safe da yamma.

Wacce ta rasa Budurcinta wato kamar bazawara ko kuma budurwa da akayiwa ( fyade ) ko kuma Wata hanya daban.

Mata da yawa suna aure cikin fargaba idan suka hadu da ( kaddara ta fyade KO kuma saduwa da namiji ) kuma hakan yayi sanadin rabuwarsu da budurcinsu don sun san maza da yawa sun fahimci hanyoyin da zasu gane mace idan ta rasa Budurcinta kuma Daga ( DAREN FARKO ) ango zai iya Fara canjawa amarya soyayyar sa harma wasu suna fadawa zuciyar su bazawara suka auro wato wani ya rigashi kwanciya da ita"_

Inda wannan ta faru dake Zaki iya tsarki da*

Ruwan dumi

Bagaruwa

Na tsawon Wata guda sai kuma matsi shi kuma zakiyishi saura sati biyu aurenki

KAYAN HADIN

ki daka garin zogale ki tankadeshi.

Ki samu man ka danya ( Ana samu a wajen masu maganin gargajiya.

Ki samu man zogale ( Ana samu a wajen masu *_Islamic-medical-centre_*.

Ki samu Karo shine wanda ake tawada dashi kuma ana wanke hula dashi ( Ana samun sa wajen masu kayan koli ).

Ki samu man shanu ( anansamunsa a wajen masu sa yarda nono).

*duk ki hada su wajen daya ki kwaba su suyi kamar sa'oi 5 zakiga sun hade sai Kiyi Matso dashi kuma Zaki iya rabashi uku gida 3 wato Kiyi matsi dashi Sau uku a cikin sati biyu.




Gyaran jiki a Musulunce

ASSALAFY ISLAMIC MEDICINE CENTER

WAJIBI NE UWAR GIDA KI GYARA JIKIN KI KAMAR YADDA MUSULUNCI YA TANADA

Mutane uku sune suke daukar nauyin rayuwar mace komai daraja da matsayinta dole wadannan sune kan gaba wajen mutunci da kimarta wanda wadannan mutane uku bata iya zabawa kanta koda daya daga ciki, abinda kawai take iya yiwa kanta shine kokarin rabuwa da kowanne daga cikinsu lafiya yayinda kowanne daga ciki yake tattare da nasa kalubalen,


Haka zalika kowacce mace akwai kaddararta a daya daga cikin su,


Iyayenta

Rabuwa da iyaye lafiya shine yafi komai muhimmanci a rayuwar mace domin shine tsani na farko da mace zatabi wajen samun rayuwar farin ciki


Mijinta

Miji kuwa dashi ake shinfida rayuwar duniya data lahira kuma miji shine wanda kalubalen zama dashi yafi girma awajen mace


‘ya ‘yanta

Haihuwa kuma itace mace domin a kowanne lokaci tana ajiye mace a gabar mutuwa kafin haihuwar sannan bayan haifuwa take sake shiga wata sabuwar wahala ta kula da jaririnta da kuma mijinta

A duk rubuce rubuce da nakeyi ban taba rubutu akan haihuwa ba yasa wasu jama’a ke ganin ana suya ana mantawa da albasa domin ta dalilin haihuwa mata da yawa sun fuskanci mawuyacin hali tareda miji wasu aurensu ya mutu wasu kuma da zaran sun haihu rashin yin gyara shine zaisa ayi musu kishiya kai bama yin kishiya shine matsalaba wulakancin da mace kesha idan wata matsala ta sameta har miji ya kara aure shine matsalar wasu kuma rashin haihuwar shine kalubalensu saboda haka yanzu zamu fara da wanda ita rashin haihuwar shine kalubalenta wanda kuma wasu matan toshewar mahaifa ko juyewarta ko dai matsalar maniyyi da dai sauransu shine yasa ciki yaki shiga,
Magungunan gargajiya sune kan gaba wajen Gyara wannan matsalar, dan haka ya dace da wanda ke fuskantar wannan matsalar tayi ta jarrabawa har Allah yasa ayi nasara, kuma daga cikin magungunan guda biyu da zaki jarraba

1. na farko zaki iya matsi da furen dabino wato zaki samu furen dabino ki barshi ya bushe ki dakashi ki hada da farar zuma kiyi matsi dashi da safe da yamma sai ki wankeshi wannan yana temakawa maniyin namiji shiga mahaifar mace


2. na biyu kuma zaki rinka cin kwan agwagwa wato zaki samu kwai guda daya ki soya shi amma da man tafarnuwa kuma zaki ci safe da yamma har zuwa sati daya shi wannan kuma yana wanke dattin mahaifa wanda yake hana mace haifuwa da izinin Allah

MATSALAR CIWON
NONO
koda yake kaso tamanin da biyar cikin dari (85%) na mata masu ciwon nono masu shayarwa ne amma ana samun wadanda basa shayarwa suna kamuwa da ciwon sakamakon amfani da magungunan turawa musamman na shafawa dan haka abu na farko da zakiyi dan kiyaye kanki daga ciwon nono shine rabuwa da magungunan turawa.

me shayarwa akwai hanyoyi da zatabi domin riga kafin kamuwa daga cutar misali yin bacci da nono a bakin yaro,
kodai kwanciya da rigar nono (brezia) ko kuma kwanciya rubda ciki. mace me manyan nono lokacinda take shayarwa ana bukatar ta rage duk wani abu dayake jijjiga nono kamar tsalle ko daurin kirji wadannan suna saka nono shan wahala daga bisani yayi ciwo.
bawa yaro nono daya abar daya yana kawo kankancewar daya sai kaga nono daya yafi daya ko kuma yawan kwanciya akan daya wannan shima dole mace ta kiyaye idan kuma hakan ta faru sai acigaba da maganin gyaran nono ahankali zai dawo kafin ki sake wani shayarwar.
sannan dole ki kiyaye da bawa yaro nono koda kina bada reno ki tabbatar yaronki yanasha kullum

domin rashin shan nonon yana kawo ruwan yayi yawa daga karshe yayi ciwo wannan shine kuskuren da wasu mata keyi idan sun bada reno sai ayi kwanaki ana bawa yaro madara kuma daga baya adawo bashi nono.
yawan shan nono wajen yaro yana kawo karancin ruwan nono ajikin mace daga karshe su motse ya zama fata ce kawai wannan ya kamata ki lura dashi idan kin samu wannan matsalar danyen ganyen zogale zaki dafa ki tace ruwan saiki hada alkama da waken soya da gyada kiyi garinsu kina zubawa acikin ruwan zogalen zaiyi kamar salala (sirki) saiki zuba nono ko madara kinasha kullum sannan ki dage dashan kunun kanwa dana alkama.


Domin magance matsalar ciwon nono kuma hanyoyi biyu kike bukata na farko garin hulba zaki zuba acikin ruwan zafi lokacinda zaki kwanta ki gauraya ki shafa akan nonon da safe ki wanke, ko kuma ki hada man ridi da man hulba da man kadanya kina shafawa akullum. 

To wannan shine karshen bayanin akan haifuwa da kuma matsalar ciwon nono yanzu kuma zamu koma bangaren gyaran jiki da yanda me jego zata dawo tsaf kamar bata haifuba.


KI FARA MATSE GABANKI KAFIN YIN KOMAI


Shima ganyen gamji yanada tasiri wajen tsaftar gaban mace wato yanda akeyi shine kisami ganyen gamji ki dafa saiki tace ruwan ki rika tsarki da ruwan har tsawon wata daya,


Bagaruwa ta hausa ita da tsintsiyar maza itatuwane da ake amfani dasu shekaru da yawa kina iya ki tafasa ko kuma kijika su da ruwa mai dumi kidinga tsarki dashi,


Ki sami aloevera da karo da kanumfari saiki zuba ruwa ki tafasa bayan kin tace anaso ki ajiyeshi har yayi sanyi kina tsarki dashi yana matse gaban mace

 
sannan idan kika samu ganyen aloevera ki matse ruwan saiki dauko man zaitun ki gauraya kiyi matsi dashi bayan kin wanke da ruwan dumi saiki sake sakawa har zuwa dare wannan zakiyi tayinsa shima yana matse gaban mace sosai,
 
Anaso ranar farko da jini ya  dauke saiki  hada ganyen magarya, garin hulba da  bagaruwa

Ki hadasu da tafarnuwa ki kisa ruwa amma kadan ki dafa idan ya dahu kitace saiki barshi ya huce sanan ki Samu auduga kina sawa a cikin ruwa kina wanke ko Ina na gabanki Ciki da waje ki tabbatar kin wanke ko ina anaso wannan ruwan ki rage kadan kuma ya zama yana da dumi sosai sai ki Samu wani auduga daban ki dangwala ruwan kisa a cikin gabanki ki barshi zuwa wani lokacin sai ki cire tun a nan zakiga kin ciko kin hade tsaf  wannan yanada muhimmanci ga mai jego.


warin gaba (Vaginal Odor)


Duk irin kwalliya da wasu matan suka iya idan akazo maganar al'auara saika rena tsaftarsu anaso gaban mace ya zama da kamshi budurwa ko matar aure kuma akwai dalilai bakwai dake kawo hakan

1 istimna.i wato idan sha'awarki ta motsa kiyi amfanida hannunki wajen gamsarda kanki ko kuma madugo (lesbian)

2  ya kasance bayan kin gama saduwa da miji bazaki wankeba kawai saidai kiyi kwanciyarki

3 dadewar wando (pant) ajiki ba'ason mace tarika barinsa yana dadewa

4 yin amfani da ruwan sanyi wajen tsarki Kodai da zaran kinyi tsarki bazaki gogeba ki saka wando da jikan ajiki

5 duk lokacin da zaki yi tsarkin bayan gida(kashi) ki hada shi da wannan wurin ki cakude da sunan wankewa hakan kan sanya wari ko doyi ya samu wurin zama a gabanki
 

6 tafiya ba wando ya zamana ke sanya wando (pant) ba sabonki bane kina iya zuwa ko ina haka ba tare da wando a jikinki ba wasu har unguwa suna fita ba tare da wando ba daga yan'matan har masu auren

7 ko kuma bayan kin yi wankan tsarki na al'ada ba ki wanke gabanki da sabulun tsarki ko baki amfani da miski domin gun yayi kamshi Domin magance matsalar sai a kiyaye wadannan dana fada a sama kuma ya zama ana amfanida miski akai kai


MATSI
Har yanzu dai muna nan akan maganar matse gaba dan haka me jego Akwai zunzurutun muhimmanci kisan wadannan abubuwa guda hudu:

1 alobera (aloevera)2 Karo (jirai)3 man zaitun (olive oil)
4 kanumfari (Cloves) 

ki sami alobera da Karo ki saka kanunfari ki tafasa saiki tace ki ajiye ruwan ya zama shine ruwan tsarkinki,



Idan kuma saura sa'a daya kije wajen me gida wato idan za ayi harka dama kin matse ruwan alobera saiki hadashi da man zaitun kiyi matsi dashi gam gam kenan ku jarraba 


YAJIN ME JEGO


Me jego kisan wadannan Baure da Dan kumasau da minanas domin suna daga cikin abubuwan dake temakawa mace musamman wajen cikowar gaba tareda ni ima da matsi musamman me jegoCikowar gaba da ni ima tareda matsi ciki da waje sune cikar mace,ta kasa idan kika samu wadannan to bakida matsala wajen gamsarda miji kuma wannan yajin yana amfani sosai awannan fanni musamman wadanda basuda halin ciccibin saniya kona akuya wasu kuma basa iya cin wannan naman shine ake amfanida wannan yajin wajen cin abinci kullum anaso ya zama yajinki ko a miya ko cikin abinci ko nama yana aiki 100%

kamar yanda kuka gani a sama sassaken baure da minanas sai Dan kumasau sune kan gaba wajen yajin saiki kara da sassaken gabaruwa kanunfari da sauran kayan kamshi na yaji amma dai wadancan na sama sufi yawa anaso aji alamarsu karara

Haka zalika yajin yana bukatar maggi da barkono kadan yanda bazai fitoba tabbas idan kika hadashi yanda yadace zakiga amfaninsa koda bakya jego matukar kinason cikowar gaba da ni ima tareda matsi

CICCIBIN SANIYA
 
Me jego yanada zunzuru tun muhimmanci kisan amfanin ciccibin saniya da kuma yanda ake yinsa domin ba sabon abu bane ganin ciccibi a wajen masu tallan maganin mata

Cin wannan nama yana ciko gaban mace yayi kyau tareda matse ta kana yayi ni,ima kuma ba sai lallai na saniya ba anayi dana akuya saboda haka gaban saniya kona akuya kowanne amma danyen shi saiki yanyankashi ki wanke ki dora akan wuta dama kin daka ridi wanda aka soyashi ki zuba zaki iya saka nonon akuya kona rakumi sannan kisaka garin kanun fari dan kuma sau saiki saka duk wani kayan miya yanda zai miki dadi saiki barshi saiya dafu saidai anaso kiyi yanda romon zai zama dan kadan shi wannan naman da romon duk zaki cinye

idan kuma kinaso kisoyashi saboda ki ajiyeshi wannan yafi wahala amma yafi aiki ana bukatar kisamu ridi da gyada ki soyasu sama sama saiki samu kanun fari da minanas da dan kumasau kihadasu waje daya ki dafa ruwan ya dafu sosai ki tace ruwan ake bukata lokacin soya naman domin idan kika yayankashi saiki zuba wannan ruwan saiki dora akan wuta kina jujjuyashi anaso kiyi yanda wannan ruwan yana karewa naman ya kusa soyuwa saiki saka man Man ayu ko man gyada ya karasa soyuwa shikenan kin gama kowanne lokaci kina iya cinsa

TSUMIN ME JEGO
Da farko anaso me jego kafin tayi 40 ya zama kulum zatasha tsumi akalla sau biyu a rana to amma saidai mutane da dama sanin kalar tsumi da me jego ya dace tasha yana basu wahala shiyasa nayi kokarin kawo wasu fitattun tsumi da suka shahara ki jarraba koda dayane kisha mamaki
? ki yanka rake kanana kanana kamar alawar yara sai ki saka a tukunya da ruwa ki saka kanumfari bada yawa ba fa da yar cittar ki itama ba mai yawa ba sannan ki bare dabinon ki cire kwallon ki jefar kwallon saiki dakashi ya zama gari saiki zuba aciki sai ki dora kan wuta ya dahu sosai sai ki sauke ki matse rake ki cire totuwar raken sannan ki tace ruwan sai kuma maida shi kan wuta
Ana iya saka mazalkwaila a ciki sai ta narke sai ki sauke kisa a fridge yayi sanyi shikenan kin hada
 
 Sai tsumin baure wanda akwai Hanyoyi da yawa da ake tsumin wanda mace idan tasha ita da kanta zataji tasamu ni ima kuma wannan karonma mun jarraba wani tsumi don me jego koda budurwa me shirin aure ta rikeshi kullum,zaki samu sassaken bauren da yayansa da minanas da kanunfari da dabino da malmo da kukuki
Wadannan anaso ki dafasu bayan sun dafu saiki tace ruwan sai kuma ki zuba mazarkwaila da Zuma kadan sannan kisake mayar dashi kan wuta ya tafasa saiki sauke shikenan kin gama kuma wannan koda kinada ciki zaki iya shansa

To atakaice wannan shine gyaran me jego wanda zai mayar da me jego ta dawo sabuwar amarya, Godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki da ya bamu damar kammala shi….



Videos din mu na youtube

Barkan ku da shigowar Assalafy Islamic Medicine Center





ASSALAFY ISLAMIC MEDICINE CENTER

GARIN KUSDUL (QUSTU) HINDI

ASSALAFY ISLAMIC MEDICINE CENTER

KUSDUL HINDI DA AMFANINSA:



Nau’in Itace ne da labarawa da mutanen Sin da sauran Kasashen yankunan ke amfani da shi acikin abinci tare da maganin cututtuka da dama.

Shi *Kistul Hindi* yana zuwa ne a kasashenmu na yammacin Africa a nau’i na gari, amma inda ake sarrafashi zaka same shi a nau’uka daban-daban.

Shiyasa zanyi bayani akan Garinsa saboda shi muka fi sani tareda sauqin samunsa.

Shi *GARIN KISTUL HINDI* Yana magance cututtuka dadama kamar:

*Ciwon mara yayin al’ada, daidai ta haila, magance dafi na wuka ko na maciji, kunama dss, maganin kumburi ko rauni, maganin aljani, sihiri, karfin maza, tsutsar ciki, magance matsalolin ciki.* dasauransu.

_*YADDA AKE SARRAFASA:*_

1. DOMIN MAGANCE MATSALAR HAILA, CIWON MARA, TSUTSAR CIKI, SIHIRI, DA MATSALAR ALJANI (ISKA) SAI ADEBI COKALI 5 NA GARIN KISTUL HINDI SAI GARIN HABBATUSSAUDA COKALI 3 SAI MAN ZAITUN COKALI 7 SAI GARIN ZAITUN COKALI 3 SANNAN AGAURAYESU AZUBA ZUMA KOFI DAYA KARAMI AKARA CAKUDEWA. ANEMI WURI MAI MATSAKAICIN YANAYI A AJE ARIKA SHAN COKALI 3 SAU 3 ARANA.
MAFI KARANCIN SHAN MAGANIN KWANA 3 ZUWA 7 GA MASU LARURAR AL’ADA KO MATSALAR ALJANI.



2. GA MASU SON KARIN KARFIN MAZA KUMA SU SAMU GARIN KUSDUL HINDI SU HADA DA NONON RAKUMI KO ZUMA SU MOTSE SU RIKA SHA IDAN ZASU KWANTA.
ANA KUMA ZUBA KIMANIN COKALI 1 ABAKI SAI ABI DA RUWA ASHANYE.

3. MATSALAR DAFI KUWA SHIMA ANA HADIYAR GARINNE DA RUWA KO AHADA DA ZUMA KO NONO NA SHANU ASHA.

HAKA KUMA GA MAI RAUNI KO YANKEWA ZAI IYA SHANSA KAMAR YADDA MUKA AMBATA HAKA KUMA ANA TAFASA RUWAN ZAFI DA GARIN AWANKE INDA DAFIN YAKE KO GASAWA KO KUMA ANEMI MAN ZAITUN AKWABA DA GARIN ASHAFE GURIN.

DA IZININ ALLAH ZA’ASAMU FA’IDAR MAGANCE WADANNAN CUTUTTUKA DA AMFANI DA GARIN KISTUL HINDI.

Allah yasa mu dace.


SAIWOYI DA AMFANINSU


  • MA’ANAR SAIWOYI

Saiwoyi na nufin wasu jijiyoyi ne ƙananan da manya waɗanda su ke riƙe da bishiya ko tsirrai. A koda yaushe saiwoyi kan kasance ne a ƙarƙashin ƙasa amma a wani lokacin sukan fito waje ma’ana su kan turo ƙasa. A ɓangaren magungunan Hausawa na gargajiya su ma ba a barsu a baya ba, domin kuwa suna bayar da gudunmawa ta musamman wajen warkar ko kwantar da cuta a jikin Ɗan-Adam ko dabba. Wasu daga cikin saiwoyin da ake haɗa magungunan Hausawa na gargajiya sun haɗa:

Karnta:


www.assalafyislamicmedicinecenter@gmail.com


  1. SAIWAR KUKA.

Ana haƙo saiwar kuka ta ɓangaren gabas sai a jiƙa a sha tana maganin ƙarfin maza .

  1. SAIWAR ZOGALA

Ana haƙo saiwar zogala a haɗa da saiwar bini da zugu da lemon tsami da kuma barkono a jiƙa a sha, yana maganin sanyi mai kumbura jiki.

  1. SAIWAR TAFASHIYA

Mata masu ciki na amfani da saiwar tafashiya, su jiƙa su sha domin samun lafiya cikinsu.

  1. SAIWAR GAUDE

Ana haƙo saiwar Gauɗe a jiƙa a rinƙa sha, yana maganin ƙarfin jiki.

  1. SAIWAR RAWAYA

Ana jiƙa saiwar rawaya a sha, ko kuma a shanya ta bushe a daka a rinƙa soyawa da ƙwai ana ci yana maganin shawara.

  1. SAIWAR BAKIN GAGAI

Ana jiƙa saiwar baƙin gagai da kayana ƙanshi a riƙa sha maganin ƙarfin maza.

  1. SAIWAR SABARA

Ana ɗebo ko haƙo saiwar sabara da saiwar lemon tsami da ganyen tsamiya a haɗa a daka, sannan a jiƙa rinƙa sha, yana magann tamama (shawara) kamar yankan wuƙa.

  1. SAIWAR JEMA

Ana haƙon saiwar jema a wanke a zuba a randa ko ruwan sha, tana maganin mayu.

  1. SAIWAR DAYI

Ana haɗa saiwar dayi da farin goro a tauna sannan a haɗiye ruwan, tana maganin farin jinni. Bugu da ƙari idan aka tauna saiwar dayi ita kaɗai aka haɗiye ruwan maganin sammu (Makaru).

  1. SAIWAR TAFASA

Ana haƙo saiwar tafasa a dafa da jar kanwa tana maganin ciwon nono

  1. SAIWAR KUKA

Ana haƙo saiwar kuka wadda ta ratsa kan hanya, ana haɗa maganin kwarce da kuma maganin soyayya. Akan haɗa abinci da ita a ba yarinya ta ci, maganin mallakar zuciyarta domin soyayya.

INA MAFITA

Amfanin Kanamfari Guda 11

Amfanin Kanamfari Guda 11 YADDA ZA'A YI AMFANI DA KANUMFARI WAJEN NEMAN LAFIYA 1.CIWON KAI (A), Yana maganin ciwon kai. A shafa ...