SIRRIN RAGE TUMBI NA MAZA DA MATA
RAGE TUMBI 1
- Man habba.
- man albasa.
- man jirjir
- .man danya.
a hadsu a zuma a rika sha sau 3 a rana yana sacce tumbi,yana rage kitsen dake cikin dan adam.
RAGE TUMBI 2
- garin hulba.
- ganyen na'a na'a.
- kanunfari.
- zuma farin kwalli.
- lemon man na'a na'a
a hada a tafasa sai a saka farin kwallin idan yayi kamar5mnts sai acire asanya zuma asha idan rage kiba ne sai asanya lemon tsami.
RAGE KIBA
babba cokali na H/sauda,babban cokali na zuma farar saka,dakakkiyar tafarnuwa cokali1
.ruwan zafi rabin kofi,ahada aruwan zafin agauraya sosai sannan asha kafin ayi breakfst da kuma kafin akwanta barci da 20mnts;ko arika shan ruwan zogale kullum.
YADDA ZA A RAGE TUMBI
Kamar yadda muka sani da yawa akwai mutane suke fama da girman tumbi wasu na halitta ne wasu kuma suke jawo shi da kansu wajen cin abubuwan da suke kawo shi, dan haka ga duk wanda suke fama da wannan matsalar to ga hanya mafi sauki kuma sadidan wacce aka jarraba aka tabbatar da zaku bi domin rabuwa da ita, da fatan Allah yasa a dace.
ABUBUWAN DA AKE BUKATA
- 1- Man sanyi na (ABONIKI BALM).
- 2- Cinnamon powder (Garin Kirfa).
- 3- Bicarbonate of Soda (Baking Soda).
YADDA AKE HADAWA
Da farko a samu man sanyi na (ABONIKI BALM) ana samun sa a wajen masu saida kayan sanyi kamar su (Mentholato, Robb, Tiger, Camfo) da sauransu, nasan da yawa kun san man sanyi na LOKO saboda zafinsa yayi suna to shi ma wannan kamarsa yake sai dai bai kai LOKO zafi ba kuma a cikin karamar kwalba yake kalarsa ruwan dorawa ne
To za a debi wannan ABONIKI BALM din cikin babban cokali daya sai a saka a karamin kwano sannan a dauko cinnamon powder wato garin kirfa kenan sai a zuba cikin karamin cokali daya, sai kuma a dauko bicarbonate of soda wato baking soda kenan sai a zuba cikin babban cokali daya sai a kwaba su sosai a tabbatar sun hadu gaba daya sai a ajiye a gefe
Sai a cire riga a dauko wannan hadin a shafe tumbin gaba daya a tabbatar an shafa shi sosai ko ina yaji to ana gama shafawa sai a samu leda fara za a ganta mai fadi ce irin wacce ake nannade sabuwar television ko computer ko sababbin abubuwa, to sai a dauko ta a nannade tumbin gaba daya, za a fara nadowa daga gadon baya sai a zagayo ta ciki a kuma zagayawa baya har sai an zagaya kamar sau uku ko hudu sannan sai a sa reza a yanke sannan a dauko riga a saka a barshi har na tsawon mintuna 20 zuwa 30.
Sannan sai a warware wannan nadin ledar za a gaya duk tumbin da ledar sun jike da gumbi to sai a shiga wanka shikenan. Za a iya yin wannan hadin sau biyu ko sau uku a sati to insha Allahu zuwa wata daya za a samun biyan bukata sosai.
Tsumin Da ake Amfani da Shi Wajen Zazzage Katon Tumbi
Katon Tumbi yanayi ne da ke damun mutane da dama, ba maza ba mata. Sau dayawa akan kashe makudan kudade wajen sayan magunguna ko shayi na musamman da zai rage tumbi ba tare da an samu sauki yadda ake bukata ba.
Abubuwan da ake bukata
Ana amfani da:
- Ganyen na’a na’a kamar guda 10 zuwa 12
- Kokumba guda daya dan madaidaci
- Lemon tsami guda daya
- Danyar citta markadadde cikin karamin cokali
- Ruwa lita biyu
Lemon tsami dai dama an san shi da kade kiba ko wace iri ce, kokumba na wanke dattin da ke cikin jikinmu kuma ta taimaka wajen rage kiba. Citta na kara fadin jijiyoyin mu wanda ke taimakawa jini ya kara gudu a jiki, hakan kuma na taimakawa wajen rage kiba. Ganyen Na’a na’a na rage kwadayi yana kuma kwantar da ciki bayan an ci abinci.
Idan aka hada karfin wadannan ‘yayan itace guda hudu aikin su yafi karfin wani shayi ko abinci ko maganin rage tumbi. Amma sai an jarraba za’a gani
Yadda ake hadawa
Za’a Jika gaba daya kayan hadin a cikin ruwa da daddare ya kwana. Washe gari ayi ta shan sa a matsayin ruwa.
Ayi ta maimaita hakan har sai an samu yadda ake so.
No comments:
Post a Comment