Amfanin Habbatus sauda Guda 31 ga Lafiyar Bil'adama
Ana kiran Habbatus-sauda da sunaye
da yawa, misali ana kiranta da"Habbatul Baraka" da larabci, wato
kwaya mai albarka. Da turanci kuma ana kiran ta da 'the blessed seed', Black
Cumin, Nigella Sativa, Black Caraway da sauransu.
Binciken ya dangata habbatus-sauda
da matukar amfani wajen magance cututtuka daban-daban, sannan ta na taka
muhimmiyar rawa wajen kiwon lafiya, cikin yardar Mai Duka.
Ana samun Habbatus-sauda daga
'ya'yan tsiron "Nigella sativa".
Hakanan an gano cewa, Shekaru aru-aru da suka gabata dubun-dubatar
al'ummar nahiyar Asia da Afirka ke amfani da ita a fannin kiwon lafiya da kuma
magance wasu cututtuka dake addabar
jikin dan-adam.
Ba tare da bata lokaci ba, ga jerin
magunguna 31 da ake samu daga wannnan
tsiro mai albarka, da fatan a sha karatu lafiya, sannan da fatan za'a jarraba
domin gane wa ido amfaninta.
1.
Matsalar Tsakuwar Koda/Mafitsara;
Ana amfani da Habbatus Sauda domin fitar da tsakuwar koda ko ta
mafitsara. Yadda za a hada wannan maganin shine, a samu habbadus sauda mai
kyau, da kuma zuma marar hadi, sai a cakuda su sannan a zuba ruwan zafi a rinka
sha. Da yardar Allah za a samu waraka. Hakanan za a iya amfani da wannan hadin
don kawar da matsalar fitsari musamman ga maza tsofaffi dake fama da wannan
matsala.
2.
Maganin Ciwon Kai; An tabbatar da cewa, ta na magance ciwon kai. Domin
samun wannan fa'ida sai a hada garin habbatus-sauda da ruwan Kal, ake sha
sannan kuma a dinga digawa a hanci don samun afuwa daga matsanancin ciwon kai.
3.
Samar Da Isasshen Ruwan Nono Ga Mace Mai Shayarewa; Wani lokacin akan
samu mace ta haihu amma kuma ta rasa isasshen ruwan nonon da za ta shayar da
jaririnta, idan har haka ta kasance, sai
a samu garin habbatus-sauda a hada ta da madara, mace mai shayarwar ta rinka
sha, idan Alllah Ya yarda za ta samu isasshen ruwan nonon da za ta shayar da
jaririnta.
4.
Maganin Tsutsar Ciki; Habbatus-sauda na maganin tsutsar ciki. Ga duk mai
fama da wannan matsala sai ya samu garin habbattus sauda ya gauraya ta cikin
ruwan kal ya ke sha.
5.
Kara karfin Garkuwar Jiki; Wani bincike da wasu masana su ka gudanar kan
habbatus-sauda ya tabbatar da cewa, yawan amfani da ita na da matukar
muhimmanci wajen karawa garkuwar jikin dan adam karfi.
6.
Rigakafin Kamuwa Daga Cututtuka; Wani bincike ya gano cewa, yawan amfani
da Habbattus-sauda wata hanya ce ta magance duk wata cuta da ka iya yiwa jikin
dan Adam barazana. Ta na yin wannan aiki ne ta hanyar samar wa da jikinmu
garkuwa mai karfi ta yadda cutukan da kan kai wa jiki hari ba za su iya tasiri
gare shi ba.
7.
Dakile Yaduwar Kwayoyin Cuta Cikin Jiki; Hakanan wani bincike da aka
gudanar kanta ya bayyana cewa, ta na dakile girman kwayoyin ccuta a jikin
mutum, baya ga haka ta na hana yaduwar kwayoyin cutar ga sassan jikinmu.
8.
Idan mutum na fama da yawan rashin lafiya, ya samu madara kofi daya,
kyakkyawar zuma marar hadi babban cokali uku, da kuma garin habbatus-sauda
babban cokali daya, sai a hada su a cakuda su sosai, sannan ake sha kullum,
Insha Allahu zai samu afuwa daga ciwon, baya ga haka kuma jikin mutum zai samu
kuzari.
9.
Maganin Gyambon Ciki; Ga wanda ke fama da wannan larura sai ya samu
garin hulba , da garin habbatus-sauda , da zuma, ya hada su waje guda ya
gauraya su , sannnan ya dinga sha da safe , kafin ya ci komai, kuma idan ya sha
kar ya karya sai bayan awa daya. Haka zai yi da rana , da dare. Hakanan idan ya
so zai iya samun man hulba ya dinga sha da zuma. In sha Allahu zai sami waraka.
10.
Maganin Asma; don samun wannan fa'ida sai a zuba man habbattus-sauda
digo 5 zuwa 15 (gwargwadon shekarun wanda zai amfani da ita), a cikin shayi ko
tafashashen ruwa a ke sha.
Ku Karanta: Amfanin Karas Ga Lafiyar
Bil'adama
11. Ciwon Kunne; Ana amfani da
habbatus-sauda wajen magance ciwon kunne. Abubuwan da mutum zai tanada sune,
kwayar habbatus-sauda, man habbatus-sauda da kuma man zaitun.
Yadda za ka hada shine, tun da farko
za ka soya kwayar habbatus-sauda sama-sama sannan sai ka nike ta don ka sami
garinta, sai ka hada da rabin cokali na man habbatus-sauda da kuma rabin cokali
na man zaitun ka gauraya su da kyau. Bayan ka tabbatar sun hadu, sai ka adana
wannan hadi cikin mazubinka mai tsafta wanda kuma yake da murfi gudun kar ya
zube.
Yadda za kai amfani da shi kuwa
shine, sai ka samu sirinji ka ke yin amfani da shi wajen digawa a kunne sau
biyu a rana.
12. Maganin Zubewar Gashi; Wasu matan kan fuskanci matsalar zubar gashin
kansu. Ga masu fama da wannan matsala za su iya yin amfani da habbatus-sauda
wajen magance wannan matsala. Sai dai a nan za a yi amfani da man habbatus
sauda ne ba da garinta ba. Yadda za a yi shine a samu man habbatus sauda da man
zaitun ma su kyau, sai a hade su waje guda. Sai ki tsefe gashin ki shafe kan da
wannnan hadi na man habbatus sauda da na zaitun, sai ya na da kyau ki tabbatar
man ya samu gindin gashin sosai.
13. Gayaran Fata; Habbatus sauda ta shahara
kwarai da gaske wajen gyaran fata. Tuni aka jarraba wannan hadi mai sauki kuma
aka ga fa'idarsa. Wannan hadi ba shi da wata wahala kamar yadda muka ambata a
sama. Za ki samu garin habbatus sauda ki hada da man zaitun ki cakuda su waje
huda, sai ki shafa wannan hadin a fuskar ki, za ki jira har misalin awa daya
sannan ki wanke. Matukar ki ka juri yin amfani da wannan hadi na habbatus sauda
to fuskarki za ta yi sumul, sheki da kuma taushi.
14. Inganta Karfin Garkuwar Jikin
Dan-adam; Habbatus sauda na taimakawa wajen kara karfin garkuwar jikin bil
adama. Ga mai son samun wannan fa'ida ta habbatus sauda, sai ya samu man
habbatus sauda mai kyau ya adana, ya juri shan rabin cokali a kullum.
15. Maganin Tsutsar Ciki; Habbatus
sauda na magance matsalar tsutsar ciki, don samun wannan fa'ida mutum zai samu
garin habbatus sauda ya hada da ruwan khal, ya ke sha sau uku a kullum.
16. Maganin Rauni Ko Ciwo; Domin
samun wannan fa'ida ta habbatus sauda, mutum zai shafa a saman ciwon ko
raunin, da iznin Allahu( S.W.T) za’a
samu waraka.
17.Maganin Kunan Wuta; Kamar yadda
take amfani da ita wajen warkar da rauni ko ciwo haka kuma ake amfani da
habbatus sauda wajen warkar da kunan wuta. Idan har tsautsayi ya faru mutum ya
kone zai yi amfani da habbatus sauda kamar yadda zai yi akan rauni ko jin ciwo,
wato ya shafa a saman kunan.
Wasu magungunan da Habbatus-sauda ke
yi sun hada da:
18.
Maganin matsalar Jinin al’adar Mata.
19. Habbatus-sauda na samar da
kuzarin jiki.
20.
Ana amfani da ita wajen gyaran Fata.
21.
Maganin matsanancin tari Da Mura.
22. Maganin Ciwon Ciki; Anan za ayi
amfani da man Habbattus-sauda ne.
23. Tana maganin ciwon shanyewar
bangaren jiki.
24. Ana sarrafa ta wajen maganin
yanar ido.
25. Maganin rage nauyin jiki ga masu
kiba ko teba.
26. Maganin ciwon zuciya.
27. Habbattus-sauda na saukar da
hawan jini.
28. Gyaran Gashi.
29. Kara yawan maniyyi.
30. Magance Cutukan Fata.
31. Man Habbatus sauda na magananin
ciwon ciki.

No comments:
Post a Comment