Sunday, May 31, 2020

ALOE VERA DON GYARAN GASHI

ALOE VERA A GASHI
aloe vera na dauke da abunda a turance ake kira da prolytic enzymes su wannan enzymes din suna gyara matattun cells din da ke saman fatar kan mutum ta hayar rage bushewa, yawan kaikayi da kuma yawan man dake taruwa a saman fatar kan mutum. wanda shi wannan man ke haduwa da datti ya chakude ya toshe kafofin gashi tare da hana gashi fitowa.

MAN ALOE VERA
wannan farin ruwan mai kauri da yake cikin aloe vera bashi bane man aloe vera shi wannan sunan sa ALOE VERA GEL sanan akwai wani ruwan dorawa dorawa (yellow) a jikin sa da ake kiran sa da ALOE VERA LATEX wanda shi wannan latex din yana da matuqar daci kuma yana bata ciki sosai.
Aloe vera ba kamar sauran shuka bane ba'a iya fitar da mansa shi kadai dole sai an hada da wani mai kamar zaitun, man kwakwa da sauran su.

YANDA ZA'A HADA MAN ALOE VERA (ALOE VERA OIL)
Abubuwan bukata sune ___
- aloe vera rabin kofi
- man kwakwa ko zaitun rabin kofi
- lavenda, jojoba, jasmine, peppermint ko rose oil digo (drops) biyu ko uku 
1-ki bare aloe vera din sai kisa chokali ki kwashe farin ruwan ciki (aloe vera gel) idan kin Ci karo da wani ruwaruwan dorawa to ki gujesa dan bashi da kyau. ki kwaba shi sosai da man kwakwan. ki jujjuya sannan ki rufe ki barshi na tsawon kwana biyu ( ki ajiye a wuri mai duhu kuma marar zafi sannan kuma ba mai sanyi da yawa ba. )
2-ki juye hadin a cikin tsaftatacciyar tukunya
3-dora tukunyar a wuta na tsawon minti goma kina yi kina juyawa kuma kar ki cika wuta 
4-sauke ki bari yayi sanyi sannan ki diga man lavender ko wanin sa sau biyu tal ko uku (kamshi yake sawa musamman dan aloe vera oil na tausa za'a hada)
wannan hadin ana amfani dashi a ilahirin jiki da kuma gashi sai dai ba zai wuce tsayin sati biyu ba. Sannan kada a ajiye shi a waje mai zafi da yawa.

MAN WANKE GASHI NA ALOE VERA (ALOE VERA SHAMPOO)
Abubuwan bukata sune 
-aloe vera gel rabin kofi
-liquid castile soap (abun hada sabulu na ruwa) kwatan kofi
-man zaitun chokali daya
-man rosemary digo (drops) 10
-man peppermint digo 10
-man bergamont digo 10
-roban shampoo wanda ba komai aciki

YANDA ZA'A HADA
za'a zuba duk wadannan kayan hadin cikin roban shampoo din a rufe da kyau sannan ayi ta jijjiga shi sosai na tsawon lokaci.

ALOE VERA HAIR MASK
Abubuwan bukata
-aloe vera gel kofi daya
-man cika-gida (castor oil) chokali 2
-garin hulba chokali 2
1-ki zuba a blender a markada shi sosai 
2-juye a roba a shafa maki shi tamkar relaxer (man famin)
3-ki rufe kan da leda sannan ki daura dan kwali ki kwanta dashi sai da safe ki wanke zai taimaka wurin tsawon gashi insha Allah.

ALOE VERA HAIR MASK (NA MAGANIN KARYEWAN GASHI)
Abubuwan bukata
-zobo chokali 2
-aloe vera kofi daya
Nikasu wuri daya a shafa a gashi na tsawon awa daya sannan a wanke.

ALOE VERA HAIR MASK ( NA TSAWON GASHI)
Abubuwan bukata
-kwoi guda biyu
-aloe vera gel kwatan kofi
-man kwakwa chokali daya
-man rosemary digo 6
ki zuba su a roba tsaftatacce a sa maburgi mai tsafta ko kuma whisker a burge shi da kyau. 
sannan a shafa daga fatar kai zuwa karshen gashi. 
a nannade gashin da hulan wanka ko leda bayan hakan na tsawon minti 15-30 sannan a wanke.
wannan shine takaitaccen abunda na sani game da aloe vera a gashi.da wannan nake fatan duk mai wata tambaya zai kokarta ya turo tambayar sa kafin wucewar sati biyu. ALLAH SHINE MASANI......... ALLAH YASA MU DACE Amin.


HANYOYIN DA ZA KI BI DOMIN MAGANCE BUSHEWAR GASHIN KAI

“Kwalliya ba ta cika sai da kai gyararre. Duk irin jan baki da hodar da za ki shafa, da jagira da zizaren da za ki saka ko ki goga, in har gashin kanki ba a gyare yake ba, to, fa har yanzu da sauran kwalliya” ‘Yan uwana mata, ina me yi muku sallama irin ta addinin musulunci Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu

A yau za mu yi duba ne kan hanyoyin warware wata matsala mai cin tuwo a kwaryarmu mu mata. Matsalace da za mu iya kira da karama kuma babbar matsala. Karamar matsala ce in har an san hanyar da za a maganceta, kuma babbar matsala ce in ba a san hanyar da za a bi wajen magancenta ba. Za mu tattauna ne a kan hanyoyin da zamu bi don magance matsalolin bushewar gashin kai.

Mata da dama na fama da wannan matsalar, wasu da zaran sun ji kan su ya bushe, maimakon su fara hada kwabin gashin kai don magance wannan matsalar, sai kawai su dauko man gashi su shafe kansu da shi, wanda yin hakan na iya zama sanadiyar dankarewar gashi, toshe kofofin gashi da hana fitowarsa, musamman idan gashi ya dade ba’a wanke shi ba. Sannan hakan zai iya bawa amosanin kai damar fitowa.

Hanyoyin da za ki bi domin magance bushewar gashin kai sune kamar haka:

1.Kwabin Ayaba

Kayan hadi
  • Zuma cokali daya,
  • Nunanniyar Ayaba.
Yadda ake hadawa
Za ki bare bawon Ayaba sai ki markada a injin nika (blender) ta markadu sosai.
Ki zuba zuma cokali daya ki gauraya su su hadu, sannan ki shafa a gashi tun daga karkashin sa har baki.
Ki rufe kan da hular leda (shower cap). Bayan mintuna 15- 20 sai ki wanke kan da sabulun wanke gashi (Shampoo) da na karawa gashi maiko (conditioner).
 
2.Kwabin man Zaitun da man Kwakwa.
  • Man zaitun
  • Man kwakwa

Yadda ake hadawa

1.Man zaitun za ki hada da Man kwakwa, sai shafa hadin tun daga karkashin gashi

Ki tufke gashin waje daya, sannan ki sa hular leda

Bayan mintuna 15-30 sai ki wanke da sabulun wanke gashi da na karawa gashi maiko

Ga masu laushin gashi yana da kyau su yi amfani da na Ayaba, domin tana kunshe da sinadarin “ potassium” wanda ya ke taimakawa gashin kai wajen sa shi ya yi karfi, yayi kyau.

Sannan yana da kyau don samun kyakkyawan sakamako, ki yi kamar sau biyu a sati. Allah yasa mu dace.


Yadda Za Ki Kula Da Gashinki

Kowane Irin gashi ke gareki yana bukatar wankewa akai-akai da sabulun wankin gashi wanda ya dace da irin gashin da kike dashi (za a ga bayanin haka a rubuce a jikin sabulun) Duk da cewa mata ba su fiye son wanke gashinsu ba saboda gudun kada ya kankance, amma akwai bukatar akalla a wanke shi sau daya a cikin makonni biyu. Tun kafin a wanke gashin, idan akwai amosani, ya kamata a kankare shi, don kada sai an wanke ya rika tasowa yana bata gashin. Sannan akwai bukatar a nemi maganin amosani na musamman.

Bayan wanke gashi sai a bar shi ya bushe, ba a son taje jikakken gashi, sannan sai a shafa masa mai wanda ya yi dai dai da gashin. Idan kitso kika fi so, bayan kin wanke kin shafa masa mai sai ki rangada wanda kike so. Sai dai kuma kada ki bar kitson ya wuce makonni biyu ba tare da kin kwance ba. Idan kuwa baki son kitso, a kullum dole ne ki zauna ki taje gashin tare da shafa masa mai, sannan sai ki daure shi da madaurin gashi (Ribbon) dai dai yadda kike so.

Idan da hali, Zai yi kyau duk bayan wata daya kije salun ki yi masa abin da ake kira steaming, wannan ne zai hana shi karkadewa. Idan kuma ke mai sha’awar yi wa gashi shamfo ce (retourching) shi ma akwai bukatar ki rika maimaitawa a duk bayan watanni biyu. Idan kuma gashinki mai karfi ne za ki rika yi kamar sau daya a wata.Yawan yin shamfo a cikin kwanakin da suka gaza wata guda, masana sun ce akwai yiwuwar zubewar gashi saboda yawan kone shi da ake yi.

Bayan duk kin gama wadannan akwai turaren gashi da za ki rika feshe gashin ki da shi, don ya rika sa shi kamshi na musamman kuma ya kamata ki sani cewa mayukan da ya yi wa wata aiki ba lalle ya yi miki ba, don haka ki kula sosai wajen zabar wanda zai dace da naki gashin.


GYARAN GASHI
Kafin ki fara gyaran gashi akwai buqatar sanin kalan gashin ki ina nufin type dinsa ba wai fari ne ko baqi ba

DRY HAIR
Zaki ganshi ko da yaushe a bushe daga kin shafa mai nan da kwana daya ya bushe fatar kanki fari tas sometimes yana sa dandruff mai gari idan rashin kulawar tayi yawa sanna gashin baya tsawo yana saurin kakkaryewa. Wannan gashin yafi kowane buqatar gwata sai kinyi da gaske in har ba sou kike ki zama kwakwido ba at least koda gashin bazai karu ba dai tou ba'a so ya ragu

OILY HAIR
Zaki ganshi ko da yaushe cikin maiqo sannan yana saurin jiqewa idan kin shiga rana irin wannan gashin wari yake yi idan ba'a yawan kula dashi especially idan akwai amosari ko kuraje akan... Domin idan ciwo ya shiga cikin gashin nan ruwa yake yi wanda hakan ke sanya wa gashin wari

NORMAL HAIR
Wannan bashi da wani matsala zaki ganshi ba a bushe ba kuma ba'a jiqe ba yana da kyau sosai very fresh

COMBINATION HAIR
Wannan gashin yawanci zaki same sana qasan (wato daga keyan ki xua kasa) yana da maiqo ta saman kuma abushe ko kuma normal shima wannan gawhin sosai yake buqatar gyara.
SENSITIVE HAIR
Wannan gashin bashi da kyau sam... Kuma rashin gyara ne yake kawo shi tare da too much iyayi komai kika samo ki laftawa gashin ki sai yazo ya lalace kullum yay ta karyewa ga yawan kuraje da amosari wani lokacin ma gashin zai zama dai dai dai dai kamar dai mutum ya zauna ya irgasu. Hakan yana faruwa a kowame launin relaxer na lissafa a sama.
Wadannan suna kalolin gashin da muke dasu gaba daya wanda akwai hanyoyi da yawa da zaki gane irin su gareki da kuma yanda zaki magance sa cikin sauki amma fa zai dauki lokaci sannan kafin ki fara akwai buqatar ki san wannan
BANBANCIN SHAMPOO DA RELAXER
Mutane da yawa sun san banbancin su kazalika mutane da yawa basu sani ba dan haka akwai buqatar ayi masu uzuri. 
SHAMPOO kamar sabulu ne na ruwa wanda ake wanke kai da shi baya qara komai baya rage komai sai dai idan anyi shi mussamman dan yayi din. Wanda idan hakan ya kasance zaki ga an rubta a jiki. 
RELAXER wannan kuma wani mai ne mussaman da aka kirkire sa don gyaran kai musamman ga baqaqen fata mai gashi a cushe idan suna buqatar gashin su ta kwanta tayi kyau kamar na fararen fata sai suyi amfani da ita.
NATURAL HAIR
Idan akace natural hair ana nufun wadanda basa sa relaxer (famin ko kumfar los.. Mama jugu jugu da sauran su). Sabida rashin lokaci yau zanyi bayanin yadda mai natural hair zata kula da gashin ta idan Allah ya kaimu next week sai muyi na masu sanya relaxer. 
Da farko dai shin gashin mu na baqaqen Africa gashi ne wanda yafi na ko wane ginsi kyau lisabab... yana buqatar gyara sosai sabda adunkule yake wanda hakan ke hana asalin maiqon dake fatar kanki (natural sebum) wazuwa har bakin gashin ki rashin faruwan hakan kuma yana taimakawa wajen kakkarye gashin wato sabo na fitowa tsoho na karyewa.
SHAMPOO
Zai dace ki bar amfani da ko wane irin shampoo musamman wandanda suke dauke da sinadarin SULFUR.. PETROLEUM DA SODIUM domin suna dauke da sinadarin busarwa irim wanda ake amfani da su a sabulan wanki omo da sauransu don haka duk lokacin da zaki saya sai ki duba ingredients din idan kuma yq zama dole sai kinyi amfani dashi tou sai ki surka shi da ruwa daidai adadin sa. 50-50 kenan ko kuma ki nemi MILD SHAMPOO wannan bashi da chemicals masu zafi sosai. Amma organics is the best option
ORGANICS
abun da ake nufi da organic shine natural abu wanda ba'a yi amfani da wani harsh chemicals (kemikal masu qarfi) wurin sarrafa su ba kamar dai wasu nau'ika da nau'in abinci da ake sarrafawa acire wani abu daga cikin sa
Yafi dacewa abun da ya kama daga man shampoo conditioner man kitso da duk wani abun da zakiyi amfani dashi a kanki ya zama natural ko kuma organic Domin duk man da kika shafa a fatan kanki yana shanyewa sannan jini ya tafi dashi zuwa hantar ki daga nan kuma ya cigaba da wanzuwa ko ta ko ina don haka yake da matuqar mahimmanci kisan irin abubuan da zaki na sawa a kanki saboda tsaro.

CONDITIONER
Shi conditioner ana amfani dashi ne dan a dawo da taushin da aka rasa na gashi. Yanda ake amfani dashi kuwa shine bayan kin gama shampoo kin dauraye tas! Sai ki shafa conditioner tun daga qasan gashinki zuwa bakin sannan ki samu leda ki rufe gashinki ki daura dankwali ki barshi na tsawon lokacin da suka rubta a roban. Bayan nan sai ki wanke ki tabbatar baki barko kadan a cikin gashin ki ba don kar yayi maki illa. 
Amma sau daya ake yin hakan a wata daga nan du ranar da zaki wanke kanki baza ki sha shi a fatar kanki ba gashin kawai musamman karshen gashin (ina nufi. Inda kike kamawa da ribon)
Ga wadanda suke wanke gashim su kusan kullum yana da kyau ya kasance duk lokacin da zaki sa ruwa a kanki to kiyi amfani da conditioner ki dauraye hakan zai sa gashin yayi maintaining moisture dinsa sannan idan ya bushe sai kiyi oiling (oiling yana nufin shafa mai lungu da saqo)

COMB
ki riqa amfani da qaton kum mai manyan haqora ko kina da gashi ko baki dashi domin karamin kumb yana tuge gashi
Sannan ki sayi daya safaya ki ajiye wajen sa da ban saboda baki idan ba haka ba kullum aikin ki baya xai riqa dawowa duk wani abun fa kike amfani dashi a gashi ya zama naki ke kadai ko ke da yaran ki. (Idan kina kula da gashin kansu kenan)

OILING
Yanda zaki fiqa shafa mai akan ki shine ki riqa sagawa kanana kina shafa mai daga fatar kanki zuwa qarshen gashin har ki gama sannan ki zauna kiyi ta massaging gashin kamar kina susa kaikayi amma a hankali dan man ya natsu a ciki idan na tsawon minti 30 ko awa daya ma idan kin gama ki tace sannan ki qara shafawa bakin gashin mai sosai. 
Rashin shafa mai a bakin gashi shi yake kawo karyewan gashi sabo na fitowa tsoho na karyewa gashi baxai taba yin tsawo ba kenan.

PROTIEN TREATMENT
Yana da kyau ko wani wata ki riqawanke kanki da kwai misali bayan kin wanke kai kin tsane ruwan tas ya fara alaman bushewa sai ki fasa kwai wasu suna amfani da farin ne kawai wasu kwaiduwan (york) wasu kuma both duk dai wqnda kika zaba sai ki shafa bayan awa daya ki wanke ki dauraye da conditioner zai sa gashinki shining (kyalli) da kyau . zaki iya hada kwan da ayaba da madara wannan ma yana da kyau sosai ya kuma qara bakin
Gashi. Amma fa kar kiga ya qarbe ki kije kiyi tayi toh ba ruwana idan ya kakkabe gashin..... Sau daya tak! A wata

SALOON 
Ki dainq yawan zua saloon ana kona maki gashin ki abanza yana karyewa gara kina gama wanke kanki kiyi kalaba ki barshi yabushe washe gari ki tsefe ki shafa masa mai
Idan kuma ya zama miki jiki amfani da kayan wuta a gashi don warware gashi tou gara ki shiga dryer (draya) yafi sauqi da rqwhin karya gashi sannan kuma ki siya HEAT PROTECTION SHAPOO, MOISTURIZER, SPRAY KO KUMA SERUM ki fara sawa a gashinki kafin a fara qonawa.




 

No comments:

INA MAFITA

Maganin Maza

ASSALAFY ISLAMIC MEDICINE CENTER