MAGANIN NANKARWA
Assalamu'alaiki Auntyna barkada war haka Dan Allah ki taimaka min da maganin nankarwa stretch marks Nagode sosai Allah Ya Kara basira Ameen
Da farko dai shi Nankarwa wasu tabbai ne layilayi da suke fitowa mace a jiki musamman wacce ke dauke da ciki zuwa haihuwa Wanda idan anyi maganin sa da wuri wato daga fitowar sa zasu iya bacewa gaba daya amma barin shi ya dade kan hana sa bacewa gaba daye sai dai zai dushe ya zama dan kadan kadan ake iya gani
Suna fitowa ne a wurare kamar haka :-
- Cikin mace daga kasa (mara)
- Cinya
- Saman mama
- Mazauni
- Saman hannu ta wuraren hammata
- Da sauran su.
ME KE KAWO NANKARWA ?
Akwai abubuwa da dama da suke sa nankarwa kamar:-
1-daukan ciki zuwa haihuwa (wannan shine babban abinda ke kawo nankarwa)
2-ramewa tashi daya (ga mutum mai qiba)
3-yin qiba tashi guda (ga mutum mai rana)
4- gado daga mahaifiya
5-jinya na tsawon lokaci
6- damuwa mai yawa da makamantar su
MATAKAN NANKARWA
Yana da matakai guda uku gasunan kamar haka:-
1) farko fitowar sa zaki gansu sirara yana da pink kala sannan yakan yi kaikayi wannan matakin bashi da wahalar magani
2) zai zama ja ko ruwan bula sannan girman su zai karu yanzun kam babu kaikayi sai lokaci zuwa lokaci zai iya bacewa ki ya ragu ya danganta da yanayin jikin mutum
3) zai zama fari ko ruwan silva wannan kam yana da matukar wahalan magani sai an jure shims din sai dai ya ragu ba wai ya bace baki daya ba.
HANYOYIN MAGANCE NANKARWA
Ruwa
Ruwa da Kuke gani yafi komai mahimmanci a jikin dan Adam. Rashin shan ruwa yana sa jikin mutum ya bushe ya tattare tare da saurin tsufa a yayin da yawan shan ruwa kofi 8-10 kullum yake sanya taushin jiki da kyawun fata kuma da hana wasu cututtuka da dama kama fatar mutum da wuri.
MISALIN YANDA ZAKA SHA KOFI 8 ZUWA GOMA ACIKIN KO WACCE RANA
-Kofi 2 da zaran kin gama wanke baki da safe.
-Kofi daya bayan karin kumallo
-kofi Daya Kafin azahar kisha
-kofi Daya kafin abincin rana daya bayan kin gama ci.
-kofi daya da la'asar.
-kofi Daya kafin abincin dare kofidaya bayan kin gama ci.
MAN CIKA-GIDA (CASTOR OIL)
Wannan man yana da Matukar amfani wajen magungunan da suka shafi fata kamar maganin pimples, cin zanzara, tabbai da sauran su.
YANDA AKE AMFANI DASHI
Ki dibi kadan sai ki sa a wuta yayi dumi sannan ki shafa a duk inda kika san yana da nankarwa ajikin ki da dumi duminsa ba yanda zai kona ki ba. Kiyi hakan har na tsawon wata guda.
Ko kuma ki shafa man sannan ki dauko yadi mai taushi na cotton ki rufe wurin dashi ki Zuba ruwan dumi a gora ki riqa dorawa a saman yadin.
ALOE VERA
Ki tatse farin ruwan aloe vera kullum ki riqa shafawa a wurin idan ya bushe sosai sai ki wanke da ruwan dumi
Ko kuma ki diba man aloe vera din chokali daya ki hada da vitamin E oil capsule daya ki shafa a wurin.
FARIN KWAI
K fasa Kwai daya ki cire kwaiduwan kwan ki yar sai kiyi amfani da fork ko whisker kiyi ta kada farin kwan har sai yayi kauri ya yi fari tas kamar cream sannan ki shafa a wurin nankarwan ki barshi ya bushe sannan ki wanke da ruwan sanyi kiyi tayin hakan har na tsawon sati biyu.
RUWAN LEMON TSAMI
ki matse lemun tsami sai ki diba ruwan ki riqa shafawa in circle a inda nankarwan suke har sai kinga ya bushe ki barshi bayan minti goma ki dauraye da ruwan dumi.
Ko kuma ki hada ruwan lemun da ruwan nukakken cucumber sannan ki shafa.
SUGAR
Ki hada suga da almond oil ko zaitun ko man kwakwa da ruwan lemun tsami ki shafa tsawon minti goma sannan ki shiga wanka.
RUWAN DANKALI
Ki fere dankali sai ki dauki guda daya ki dan jajjaga ki shafa ruwan a inda nankarwan take idan ya bushe zaki ga yayi fari sai ki wanke da ruwan dumi ki shafa zuma ko zaitun ko man kwakwa.
MAN KADE
yawan shafa man kade a wurin ma yana rage shi sosai.
Daga karshe Ina kira ga mata da su daure da zaran sun haihu su fara neman hanyan magance wannan matsalar kuma ku sani cewa wannan hadin gargajiya ce babu kemikal acikin ta dan haka yana daukan lokaci kafin aga canji kamar Sati biyu idan baki ga chanji ba sai ki dauki wani kuma. Allah shine masani. Allah yasa mu dace.
A yayin da ta fito, ta kan zamewa mutane karfen kafa domin ta na da wahalar fita.
Ga hanyoyi guda 5 da za’a iya magance su a saukake ba tare da amfani da mayuka masu illlata fata ba
Hanya ta 1: Dankalin hausa
Dankali yana dauke da sinadarin sitaci da yake lausasa fata da kuma sinadarin da yake hana fata lalacewa wato antioxidant. Haka kuma dankali yana dauke da sinadarin vitamin c, potassium, thiamin, riboflavin, iron, zinc da sauran su.
Yanda ake amfani da shi:
A yanka Dankali sannan a shafa a hankali a kan nankarwar. Sai a barshi na tsahon mintuna 15 zuwa 20, sannan a wanke da ruwan dumi. A maimaita haka a kullum
Hanya ta 2: Aloe Vera
Ruwan da ke cikin Aloe vera yana dauke da sinadarin Collagen wanda aka san shi da gyara fatar da ta lalace da kuma kara dankonta, kyanta da kuma yarintar ta.
Yanda ake amfani dashi:
A karya ichen Aloe vera guda sai a shafa ruwan a kan nankarwa. A barshi tsahon awa 2 zuwa uku sai a wanke da ruwa. A maimata hakan a kullum har sai an samu sakamako mai kyau
Hanya ta 3: Man kadanya da Koko butter
Hadin Man kadanya da Koko butter yana dauke da sinadarin vitamin E da kuma sinadaran da ke hana fata lalacewa
Yanda ake amfani da shi
Za’a samu koko butter karamin cokali 2, da man kadanya shima karamin cokali 2, sai sinadarin vitamin E karamin cokali 1. Za’a narka man kadanya da kuma man Koko butter sai a kara vitamin E din a ciki a gauraya. Za’a dura gabadaya a cikin mazubi a ajiye a na shafawa a kan nankarwar kullum.
Hanya ta 4: Lemon tsami
Acid din dake cikin lemon tsami yana taimakawa wajen warkar da ciwo, kurajen fuska da kuma nankarwa.
Yanda ke amfani da shi:
A yanka Lemon tsami gida 2 sai a shafa shi a gurin da nankarwar take. A barshi na tsahon mintuna goma sai a wanke da ruwan dumi. Ko kuma a hada ruwan Lemon tsamin da ruwan kokwamba a shafa a wajen. A yi hakan a kullum idan ana san samun sakamako mai kyau
Hanya ta 5: Man zaitun
Man zaitun yana dauke da sinadaran vitamin A da E wanda suke kara gudun jini zuwa karkashin fata da kuma kara laushin jiki. Suna kuma hana lalacewar fata.
Yanda ake amfani dashi:
A dan dumama Man zaitun a wuta, kar yayi zafi da yawa yanda zai kona fata. Sai a shafa a gurin da nankarwar ta ke. A yi hakan da safe da yamma a kullum.
No comments:
Post a Comment