MENENE CUTAR SUGA (DIABETES) ???
Jikin 'dan adam na bukatar wani irin nau'in sinadarin suga (glucose) dake cikin jini domin aiwatar da wasu daga cikin manya-manyan ayyukan da suka shafi lafiyar jikin. Suga (glucose) na bayarda kuzari (energy) ga jikin 'dan adam wanda ake bukata wajen narkarda abinci da kuma rayuwar 'kananan halittun da suka tattaru yawa sukayi ginin jikin 'dan adam ko halittarsa tamkar bululluka [tubali] (cells).
Wannan sugan 'glucose' shine makamashin dake bawa jikin 'dan adam kuzari domin rayuwa. Kuma ana samun sa ne daga abincin da muke ci - wato nau'in abinci mai samarda kuzari (carbohydrate), kamar irinsu gero, dawa, masara ,shinkafa da sauransu. kwakwalwa (brain), ko hanyoyin sadarwar kwakwalwa a jiki (nerves) da kuma wasu jajayen halittun jini ( developing red blood cells) , duk kaninsu suna amfani da wannan makamashi (glucose) domin samun rayuwa.
Ciwon-suga (diabetes) cutace wadda suga (glucose) dake cikin jini yake haurawa sama - wato suga yayi yawa a cikin jini. Yawansa nada illa ga lafiya. Dalilin yawansa na faruwa ne sabili da jikin mutum baya samarda da wani sinadarin kemical mai suna 'insulin'
- ( = type 1 diabetes) , ko jikin ne baya amfani da 'insulin' yadda ake so, ko kuma ma jikin baya samar da 'insulin' da kyau [wato isasshe]
- ( = type 2 diabetes). Idan har babu 'insulin' tofa sugan 'glucose' zai cigaba da taruwa da yawa cikin jini har yayi illa ga lafiya. Sinadarin 'insulin' (a hormone), wata tsokace ajikin dan adam take samar dashi (pancreas).
Amfanin sinadarin 'insulin' shine daukar sugan 'glucose' dake cikin jinin zuwa cikin 'kananan halittun da suka gina jikin 'dan adam (cells) domin samun kuzari gare su da cigaban rayuwa. Idan babu 'insulin' ko baya aiki yanda ake bukata to suga fa zai cigaba da taruwa cikin jini yayi yawa har ya haddasa munanan matsaloli ga lafiya. Sugan zai iya yin illa ga idanu, koda, wasu jijiyoyin jini da kuma wayoyi/hanyoyin sadarwar kwakwalwa a jiki. Ciwon-suga zai iya haddasa cutar zuciya, mutuwar sashen jiki koma ya jaza yanke kafar marar-lafiyar. Idan ciwon yayi 'karami zai iya haddasa matsalar 'kashi da gabobi, matsalar fata, matsalar narkewar abinci, rashin karfin mazakuta, matsalar hakora da dasashi.
'Type 2 diabetes' ,wato nau'in ciwon-suga na 2 da mukayi bayani (wanda jiki baya amfani da 'insulin' yadda ya dace) shine nau'in ciwon-suga da yafi yawa ga mutane da dama fiye da nau'in ciwon-suga na 1: 'type 1 diabetes' (wanda mu kace jiki baya samarda da sinadarin 'insulin').
Alamomin Ciwon Alamomin Ciwon-suga Nau'i na
(type 1 diabetes symptoms):
- • Yawan jin kishirwa sosai
- • Yawan yin fitsari
- • Yawan jin yunwa ko gajiya
- • Raguwar nauyin mutum ba tare da mutum yayi kokarin ragewar nauyin ba
- • Dadewar ciwo/gwambo bai warke ba/warkewa a hankali
- • Rashin gani da kyauAwon jini zai iya nuna idan akwai ciwon ko sabanin haka.
Idan akwai irin nau'in ciwon , toh mutum zai cigaba da amfani da sinadarin 'insulin' da aka samar a asibiti, za'a bashi sinadarin a asibiti akan 'ka'ida da umarnin 'kwararren likita. Anfi yawan samun 'kananan yara da matasa da irin wannan nau'in ciwon-suga (Juvenile diabetes/Insulin-dependent diabetes)duk dadai cewa zai iya shafar mutane a kowani shekarun su na rayuwa. Alamomin Ciwon-suga Nau'i na 2
(type 2 diabetes symptoms):
- • Yawan jin kishirwa sosai
- • Yawan yin fitsari
- • Yawan jin yunwa ko gajiya
- • Raguwar nauyin mutum ba tare da mutum yayi kokarin rage nauyin ba
- • Bushewar fata, kaikayin fata
- • Mutum yaji kamar ba kafarsa ba ko jin tsira a kafafu
Yin awon jini a asibiti ko wata ingantacciyar cibiyar lafiya zai iya nuna maka ko kana da ciwon suga ko kuma akasin haka. Motsa-jiki (exercise), rage nauyin jiki yanda ya dace dace da koyarwar cikon lafiya, da kuma kula da tsarin cin abinci daya dace da ciwon lafiya, ko shakka babu , zasu taimaka sosai wajen shawo matsalolin lafiya na ciwon-suga. Cututtukan saifa, magunguna, kemikals, kamuwa da wasu cututtukan da gado daga mahaifan mutum na daga cikin dalilin da ake alakantawa da suke haddasa ciwon-suga.
Allah ya bamu lafiya. AMEEN.
No comments:
Post a Comment