MAGANIN RASHIN GAMSAR DA IYALI
Abubuwan da suke yin sanadiyyar mutuwar al'aurar 'Da Namiji suna da yawa sosai. Ga wasu daga ciki:
1. HAWAN JINI :
idan kana fama da hawan jini zaka iya samun raunin al'aura saboda rashin gudanawar jinin jikinka yadda ya kamata.
2. CIWON SUGAR (DIABETES)
idan kana fama dashi shima yana mutukar kashe al'aurar namiji.
3. SHAFAR ALJANI KO SIHIRI :
idan kana tare da Aljanar soyayya, ko kuma matarka tana fama da JINNUL ASHIQ (namijin dare, Aljanin soyayya) zaku iya gamuwa da matsaloli kala-kala ta bangaren jima'inku.
4. SHAYE SHAYE:
shaye shayen Abubuwan da suke sa maye ko kuma shan kwayoyi masu nauyi ga jikin mutum.
5. RASHIN HUTU :
Rashin isashen hutu shima babban jigo ne wajen haddasa matsalolin Rashin gamsar da juna ta fuskar mu'amalar auratayya.
Don haka idan kana fama da wani daga cikin abubuwan nan dana lissafa, dole sai ka nemi Hanyar warware tushen chutar sannan Karfinka zai dawo.
Idan kuma duk babu, kawai dai rashin karfin ne Allah ya jarrabceka dashi, to ka nemi Kwazbara cokali 5, Garin Habbatus Sauda Cokali biyar, Ka hadasu waje guda ka nikasu.
Arika diban garinsu cokali guda ana zubawa cikin Kwan kazar gida, ko na Zabuwa. ana soya maka kamar guda 4 kana ci kullum. insha Allah karfinka zai dawo fiye da da.
No comments:
Post a Comment