Thursday, May 28, 2020

AMFANIN ZOGALE DON KARIN NI'IMA

AMFANIN ZOGALE DON KARIN NI'IMA


Ruwan Zogale:

Amfanin ruwan zogala ba zai lissafu ba a maganin cututtukan da ya ke yi ma na a jikinmu. Amma zan yi bayanin amfaninsa a bangaren karin ni’ima a jikkunanmu ne kawai. A- ki tsinke zogale ki wanke ki tafasa sosai ki tace ruwan zogalen ki zuba kaninfari da citta ki tafasa. Sai ki sauke ki dinga kurba da zafinsa kamar shayi. Ya na gyara jiki ya saukar da ni’ima sosai. Ya na karawa mace kuzari a jikinta sosai,

sannan ya na karawa mace juriya wajen saduwa. Ki tsinke zogale ki wanke ki markada ganyen a ‘blander’ ko ki mutstsika da hannunki ki kara ruwa a kai ki tace ki matse dusar. Ki zuba madarar ruwa gwangwani daya a cikin ruwan zogale cikin jug daya. Ki sa zuma ta ji sosai. Ki juya ya hadu ki dinga sha. Gaskiya ba shi da dadin sha, sai dai akwai shi da aiki; ni’ima lutsutsu! Domin duk bushewar gabanki da rashin ni’imarki sai ni’ima ta zo,

kuma ya na sa jin dadi sosai. A nan ganyen zogalen da ki ka tafasa sai ki zuba a faranti ki yanka tumatir manya guda uku ,ki yanka gurji (cocumber) babba guda daya, ki saka magi, gishiri kadan, mai kadan. Kar ki sa kulikuli. Zai yi miki maganin basir da cikowar gaba. Zai kara mi ki ni’ima da dandano gurin maigida.



No comments:

INA MAFITA

Maganin Maza

ASSALAFY ISLAMIC MEDICINE CENTER