Sunday, May 24, 2020

MAGANIN SANYI (Gonorrhea ) NA MAZA DA MATA

MAGANIN SANYI MAZA DA MATA

 

1.  ALAMOMIN CIWON SANYIN MARA NA MATA  / SANYIN MATA WANDA AKE YAƊAWA TA JIMA'I*

📗📗📗📗📗📗📗📗📗📗📗

Waɗansu daga cikin alamomin ciwon sanyin mata da ake samu ta hanyar saduwa da namiji ko mace mai ɗauke da ciwon : (STD/STI):
1. Fitar ruwa daga farji, ruwa mai kauri ko silili, kalar madara ko koren ruwa daga farji.
2. Kuraje masu ɗurar ruwa da fashewa a farji , musamman wurinda pant ya rufe.
3. Feshin ƙananan ƙuraje a farji ko cikin farji
4. Raɗaɗin zafi a lokacin yin fitsari
5. Jin zafi cikin farji lokacin jima'i
6. Zubar jinin al'ada mai yawa ko zuwan jinin al'ada mai wasa, wato akan lokacinda ya saba zuwa ba
7. Ciwon mara
8. Zazzaɓi
9 . Ciwon kai
10. Murar maƙoshi/maƙogwaro
11. Kasala/raunin jiki
12. Zubar jini lokacin saduwa
13. Dakushewar sha'awa, ko rashin sha'awa ko ɗaukewar ni'ima
14. Bushewar farji
15. Ƙaiƙayin farji
16. Warin farji (ɗoyi) mai ƙarfi
17. Kumburin farji da yin jawur
18. Gudawa
18. Ko rashin ganin wata alama daga cikin wadannan alamomin da muka bayyana a sama.

Insha Allahu nan gaba zamuyi cikakken bayani akan wannan matsala, amma kafin nan ga wasu magunguna da zamu baku shi sadaka, wanda zaku magance wannan matsalar cikin sauqi





Abubuwan da ake bukata:

LEMUN TSAMI =21

2.    TAFARNUWA=21

3.    NAMIJIN GORO= 50

4.    CITTA DANYA-15

5.    KANUMFARI=COKALI (10)

6.    KIRFAH=COKALI (10)

7.    ZUMA (roban ever water (1)


YADDA ZA A HADA:

Lemun tsamin za a yayanka shi ne sai a matse ruwan sa, sannan bawonsa din sai shima a yayanka shi kanana a zuba cikin ruwansa, sai ayi blendin din tafarnuwa da namijin goro da citta a zuba cikin ruwan lemun tsamin sannan a dauko garin kirfa a zuma, sannan a dora kan wuta mara karfi a bashi akan wuta har tsawon 10, sai a kashe wutan sannan a zuba Zuma a ciki.

NOTE: Za a zuba ruwa litta biyar a cikin wannan hadin sai a tafasa da maganin.

a rika sha rabin kofi da safe, rabi kuma da yamma, amma bayan an tace maganin.

Allah yasa mu dace



No comments:

INA MAFITA

Maganin Maza

ASSALAFY ISLAMIC MEDICINE CENTER