Saturday, May 23, 2020

Yadda za a iya narkar kitsen da ya taru a cikin mutum

Yadda za a iya narkar kitsen da ya taru a cikin mutum


Teba tamkar wata matsala ce da kiba ke haddasa wa. Kungiyar WHO ta bayyana cewa, kiba na iya kawo illa ga koshin lafiya, sannan tana sa mutum ya tsufa da wuri. An tabbatar da cewa, ya zuwa yanzu, akwai cututtuka a kalla guda 15 da kiba ke haifar wa, wadanda ke iya haddasa mutum ya mutu nan take.
Bisa sabon nazarin da aka yi an nuna cewa, maza su kan gamu da kiba ne sakamakon kwayoyin halitta da suka gada daga kakani, yawancin mai na taruwa a cikinsu. Ko shakka babu, dalilan da sukan haddasa yin kiba sun sha bamban sakamakon kwayoyin halitta daban-daban da maza suka gada. A hakika dai, ko an samu isheshen barci ko a'a wannan dai shi ne muhimmin dalilin da ke saka maza yin kiba. Idan shekarun maza na haihuwa ya karu, ba za su iya samu isheshen barci ba, sakamakon haka, yawan kwayoyin halitta masu sa girma da sauri da za a haifar zai ragu, ta yadda kitsen da ke jikin maza za su karu kuma za su taru a ciki. Bayan haka kuma, mazai magidanta su kan dade suna zaune a ofis, ba su son motsa jiki, wannan zai sa kitse ya taru a ciki. Bugu da kari, a yayin da maza suke samu matsin lamba daga aiki, wasu su kan ci abinci da yawa, a sanadiyyar haka abincin ba zai narke kamar yadda ya kamata a ciki ba, wannan ma wani dalilin ne da ke haddasa yin kiba.
Yaya za a iya narkar kitsen da ya taru a cikin mutum? Yanzu ga shawarwarin da kwararru suka ba mu.
Saboda aikin da ake fama da shi, da kuma bukatar da ake da ita ta Da safe lokaci ne da kayan cikin mutum ke soma ayyukansu, idan ba a yi karin kumallo ba, to za a lahanta su. Saboda haka, bai kamata a yi watsi da karin kumallo ba, ban da wannan kuma dole ne a ci abinci masu inganci har a koshi.
Ana iya cin abinci iri daban daban da tsakiyar rana. Amma, abin da ya kamata a lura da shi shi ne, kada a koshi sosai, a ci abincin da ya kai kashi 70 cikin kashi dari. Bayan awa daya da cin abinci da tsakiyar rana, to yana da kyau a sha shayi kadan.
Mutane su kan mayar da hankali kan abincin dare. Amma, ya fi kyau a rage cin abinci kamar su shinkafa da alkama da sauransu. Kamata ya yi a kara cin 'yayan itatuwa, da kwai, da kifi, da sauransu, sannan yana da kyau a kara shan kwano daya na miyan da ake yi da laimar kwadi, ita ma wata dabara ce mai kyau wajen rage cin shinkafa da alkalma da sauransu.
Kazalika, kada a ci kayayyaki kamar su shinkafa da alkalma bayan karfe 8 a dare, saboda wannan na iya kawo illa ga ciki wajen sarrafa abinci, ta yadda zai sa kitse ya taru a ciki, gami da haddasa wasu cututtukan ciki.(Bilkisu)

https://youtube.com/c/assalafyislamicmedicinecenter



No comments:

INA MAFITA

Maganin Maza

ASSALAFY ISLAMIC MEDICINE CENTER