BUDURCIN 'YA MACE
Wacce ta rasa Budurcinta wato kamar bazawara ko kuma budurwa da akayiwa ( fyade ) ko kuma Wata hanya daban. Mata da yawa suna aure cikin fargaba idan suka hadu da ( kaddara ta fyade KO kuma saduwa da namiji ) kuma hakan yayi sanadin rabuwarsu da budurcinsu don sun san maza da yawa sun fahimci hanyoyin da zasu gane mace idan ta rasa Budurcinta kuma Daga ( DAREN FARKO ) ango zai iya Fara canjawa amarya soyayyar sa harma wasu suna fadawa zuciyar su bazawara suka auro wato wani ya rigashi kwanciya da ita"_ Inda wannan ta faru dake Zaki iya tsarki da* Ruwan dumi Bagaruwa Na tsawon Wata guda sai kuma matsi shi kuma zakiyishi saura sati biyu aurenki
KAYAN HADIN
ki daka garin zogale ki tankadeshi. Ki samu man ka danya ( Ana samu a wajen masu maganin gargajiya. Ki samu man zogale ( Ana samu a wajen masu *_Islamic-medical-centre_*. Ki samu Karo shine wanda ake tawada dashi kuma ana wanke hula dashi ( Ana samun sa wajen masu kayan koli ). Ki samu man shanu ( anansamunsa a wajen masu sa yarda nono). *duk ki hada su wajen daya ki kwaba su suyi kamar sa'oi 5 zakiga sun hade sai Kiyi Matso dashi kuma Zaki iya rabashi uku gida 3 wato Kiyi matsi dashi Sau uku a cikin sati biyu.
ILIMI NA MUSAMMAN
kamar yanda kowa yasani gaban mace baya rabuwa da jika ko na ni ima ko kuma na cuta ya danganta da irin ruwan idan akace farin ruwa ana nufin fari kal me kamar ruwan famfo shine yake zama na ni ima kuma yanada yauki sannan yanada dandano wani kamar gishiri ya danganta da irin abunda mace kesha saidai mata da yawa farkon saduwa akwai wani farin ruwa me kamar nono dan kadan yana fitowa wannan wani ruwane wanda ba kowacce mace ke samuba domin da yawa mace daga ta fara haifuwa shikenan kuma wannan ruwane na musamman farar mace wani ruwan kuma yauki zakaga yanayi kuma haka kawai mace ko zance tayi da namiji zataganshi kuma me irin wannan ruwan bata taba bushewar gaba kuma daban take acikin mata
shikuma ruwa na cuta haka kawai yake zuwa agaban mace kuma bayan farine me kamar majina zakaganshi guda guda wani kuma kamar zare zare kuma ruwan yana iya canja kala daban daban wani yakoma Green wani brown kuma sauda dama warinsa yana zama kamar na danye kifi akwai kuma me warin danyen kwai wani ruwan kuma kamar mace me ciki tana yawan ganinsa musamman bayan gama saduwa ko kuma bayan ta gama fitsari wannan shikuma dattine na mahaifa shima ba matsala bane dalilai da yawa suna saka mata kamuwa da ciwon sanyi saboda idan namiji yanada dashi zai iya sakawa mace ga kuma shiga kowanne toilet ko wajen tsugo a toilet sannan kuma koda mata hudune agida aka samu daya me wannan cutar tana iya sakawa sauran shiyasa mata masu hikima basa rabuwa da riga kafin cutar 
MENENE BUDURCI?
Wannan wani darasine mai muhimmanci da ya kamata mutane su sanshi musamman samari da yan mata, amma da zaran an fara irin wannan sai a kama jin kunya, ko shi mai koyarwar ya ji kunya ya ki yin bayani yanda ya kamata ko su masu sauraro su sa kunya su qi nutsuwa su koya. Don haka ya kamata mu gane wurin neman ilimi ba a jin kunya.
Nana Aisha (RA) tace: "Madalla da matan madina wadanda kunya bata hanasu tambaya game da abinda ya shafi addininsu ba. "
Sannan a wani hadisin Ummu Salamah tace ma Manzon Allah (SAW ) "Lallai Allah baya jin kunya game da gaskiya. Shin akwai wanka kan macen da tayi mafarki?" sai yace "Eh! idan ta ga ruwa (ma'ana idan ta fitar da maniyyi)". [Bukhari da Muslim].
Indai wurin neman ilimi ne musamman ma na gyaran ibada da rayuwa to ba a jin kunya. Wannan dalilin ne yasa naga ya kamata na yiwa yan'uwana wasu bayanai akan budurci, bayani ba irin na posts na rashin kunya da batsa ba da suke yawo a social network. A'a bayani akan yadda budurci yake da darajar budurci don yan mata su san me suke dauke dashi.
Allah cikin ikon sa da tsari na halitta Irin naSa Yasa kowace mace da budurci ake haifanta, shi ake kira da "HYMEN" A turance.
Ita dai HYMEN wata fatace mai dauke da jini a cikinta tana farjin kowace mace amma ba tada wuyar fashewa. Sannan ba wai hymen bane kadai a cikin farjin mace ba a'a. Akwai fata biyu sune LABIA MINORA da VESTIBULE Su wainnan sune suke farjin mace amma shi ainihin budurcin yana daga ciki, ma'ana kenan sune suke kare miki ainihin budurcin ki na ciki.
Shi wannan zafin da ake ji lokacin jima'i na farko sune suke budewa suke fitowa da jini, Sune idan babu su to zaki ga babu wannan jan jinin a jima'in farko saboda sun rigaya sun narke ne a gabanki, sai ya zamana koda kin yi aure mijin ki ya sadu dake to zai ga baki fitar da jini ba sai ya dauka ko kin taba bin maza ne, bayan kuwa ke baki taba yi ba, kuma mata dayawa suna shiga cikin matsala saboda mazan su suna jin su a bude yayin da suka shiga gidajen auren su.
Sannan su wainnan fatan uku ba makawa idan daya ya yage a cikin su to dukkan sauran zasu yage, don ita ba tada karfi, kuma yawan kai hannu wurin zai bude shi. Mafiya yawan yan mata suna loosing virginity nasu ba tare ma da sun sani ba, saboda wasu abubuwa kamar haka:
1. Guje guje da tsalle tsalle, da tafiya da sauri kamar gudu koda yaushe.
2. Rawa mai karfi ko motsa jiki mai karfi.
3.Bude kafa, ya zamana mace tana zama da karfi sosai, kuma kullum in ta zauna zata bude kafa, bata kama jikinta.
4.Hawa bishiya, da keke, da daukan abu mai nauyi.
5.Tsallake rami mai fadi sosai ko yin abin da zai sa sai ta bude kafanta sosai.
7.Nishi mai karfi.
8.Magana ko ihu mai karfin gaske, don akwai mata shashashai, ita mace tana magana ne with class da kamala irin ta mace.
9.Yawan saka hannu a wurin na rashin dalili.
10.Dadewa ba aure da yawan shekaru ma yana sa mace ta rasa budurcin ta.
11. Mikewa tsaye da karfi, idan zaki mike tsayema ya kamata a matsayinki na macce ko matar aurece ki yishi a nutse balle budurwa da tasan darajar ajiyar ta.
11.Wata kuma budurwar yawan cushe cushe ko matse matsen abubuwa da yawan sit bath ba tada aure zai iya kawo kaucewar budurcinta.
12.Sannan wasa da kansu da wasu mata ke yi saboda matsanancin sha'awa gashi ba su da aure, yana kawar musu da budurci. Dama sauran su.
Kenan dole ne ki fahimci matsayin ki na mace budurwa, kuma ki dauki aniyar gyarawa, Idan ka tattauna da matan aure da dama zasu ce wallahi idan har namiji ya sami mace budurwa to ta riga ta gama amsan ma kanta girma da daraja, kuma duk lokacin da yaso ya ci mata mutunci zata tashi tsaye tace wallahi kasan dai yanda ka same ni, ni ba mutumiyar banza bace, suka ce sai ka ga sun shiga hankalin su, saboda sun San ke mai mutunci ce.
Don haka babu wani dalili da zai sa ki bari ki watsar da budurcin ki musamman ta hanyar zina. Wallahi budurcin ki shine daraja da kimarki a gidan mijinki, Kenan shine yancinki, kada ki sake wani sakaran saurayi ya hure miki kunni ki bashi budurcin ki a bulus, kuma ko nawa ya baki to bai kai 'dan kadan din sadakin da mijinki ya bada ya auro ki cikin daraja ba, wanda kowa yasan ya bada.
ABIN DA YA KAMATA MAZA SU FAHIMTA SHINE:
Hakika mun san cewa budurci abu ne mai 'kima da daraja saboda wannan shi yake nuna mace bata taba sanin wani namiji ba, namiji yana farin ciki da murna ace shine ya fara sanin matar sa, amma ina so ku sani cewa Idan ka shigi mace baka ga jini ba, ba yana nufin babu budurci bane, ko yana nufin shikenan ta san namiji ba a'a duk shekarun Mace kuma koda ta rasa budurcin ta to dole a matse take, Saboda babu abun da ya taba bin wannan hanyar. Sai dai kawai babu wannan jinin.
Sannan akwai wacce ma jinin baya fita sai bayan ka gama taje futsari sannan zata ganshi, kenan ba hujjah bane ka rinka yiwa mace wulakanci na cewa wai bata kawo budurcin ta ba, don mace budurwa taste din ta daban yake wallahi.
Mace gaskiya bata ganewa, kuma ba ta sanin lokaci da ta rasa shi, kenan ita ma da tasan bashi to zata zo gidan ka cikin tashin hankali, amma ka same ta a matse da kyar ma wani zai shigeta but still zai canza fuska, tun a daren ma wani zai ce wai ya naga haka?
Zinace zinace ya yawaita yanzu shiyasa maza suka dogara sosai da wannan ganin jinin, saboda suna ganin koda ma ba budurwa bace zata nemi abubuwan matsi ta matse kanta, shiyasa shiyasa an sha fahimtar dasu amma basa samun nutsuwa muddin basu ga jinin ba. Kenan tun da abun ya koma haka dole ne ki bude ido, ki rinka kula da budurcin ki kamar kwai, don gujewa matsalolin gidan aure.
SHIN JININ HAILA YANA BUDE BUDURCIN MACE?
Allah cikin hikimarsa ya kaddara komin girman jinin da ke fitowa yayin jinin hailar mace to baya kawar mata da budurcin ta, duk da dai wasu manyan matan sun ce yana dan bude mace kadan idan ta gama jininta, amma likitoci sun ce baya bude mace, Shiyasa suke bawa yan mata shawarar sanya almiski don wurin ya koma kamar da.
Wannan shine kadan daga cikin bayani akan budurci, amma ban gama rubutun ba, nan gaba zan yi bayani akan hikimar da yasa Allah yayi budurci. Sannan da darajojin mace budurwa a musulunci, sannan da hanyoyin da mace zata bi wacce kaddara yasa ta rabu da budurcin ta, sannan da bayani akan fake hymen.
No comments:
Post a Comment