Magunguna 9 Da Kanumfari Ke Yi a Jikin Dan Adam

Magunguna 9 Da Kanumfari Ke Yi a Jikin Dan Adam.

 

Allah (S.W.T) ya sanya waraka cikin abincin da muke ci yau da kullum. Amma da yawa daga cikinmu ba su san da haka ba. Wannan dalili ya sa Mujalla ta dukufa don wayar da kan jama'a su rungumi wannan hanya ta samar da magani daga abincin da muke ci yau da kullum

Duk lokacin da muka tashi yin rubutu da ya shafi abincin da muke ci don warkar da cututtuka ko don samun riga kafin kamuwa da su, ko kuma don kara inganta lafiyarmu, mu kan ce "Abincinka maganinka". Ina jin dadin maimaita wadannan kalmomi, kuma da gaske mu ke wannan batu, ko tantama babu  abincinmu maganinmu ne.

Saboda haka ne yau za mu duba fa'idar da Kanumfari ke da ita kan lafiyarmu. Hakika Kanumfari ya yi fice wajen bayar da riga kafin kamuwa daga wasu cututtuka, da waraka da kuma inganta lafiya ta wajen yawaita amfani da shi.

Shekaru aru-aru da suka wuce, al'ummar kasashe da yawa irin su Indiya, Indonesiya, Amurka da wadansu daga cikin kasashen Afrika da na Larabawa da yawa, ke amfani da shi don samun waraka, ko riga kafin wasu cututtuka.

 Kodayake, mai karafu zai ce, ai shi kanumfari ba wani abinci ne da za'a ci a koshi ba, anan sai mu ce, amma dai sanadari ne da ake hada nau'ika dabam dabam na abincin da muke ci yau da kullum. Misali a kasar Amurka Sukan yi amfani da shi wajen girki da kuma yin Biredi. Yayin da a kasar Netherland sukan yi amfani da shi wajen hada wainar Fulawa.

Haka dai al'amarin yake gwargwadon kasa da al'adar mutanenta, gwargwadon yadda su ke amfani da wannan  tsiro mai matukar amfani.

Kanumfari nada Amfani ga lafiyar dan Adam domin yana Maganin cututtukan da kan addabi dan adam, hakanan ya na iya rigakafin wasu da dama.

Saboda haka ga wasu daga cikin amfanin da Kanumfari kan yi ga lafiyarmu, da fatan mai karatu zai bi a hankali kuma ya gama karanta wannan makala har karshe don ya amfana. Da fatan kuma za ai "sharin" don sauran 'yan uwa su amfana.

 

1.    Maganin  Makero Ko Kurajen Fata.

Kamar yadda mu ka ambata a sama tun da farko, ana amfani da kanumfari a kasashe da yawa wajen magance tare da riga kafin wasu cututtuka, kuma misalan kasashe ya gabata. Game da gyaran fata da magance cutukan fata, kasashen Chana da Japan kan yi sabulu da Kanumfari domin magance cutukkan da ke shafar fata.

Saboda haka game da makero, ana amfani da man kanumfari ne, a shafa a wurin da matsalar ta ke,  musamman bayan fitowa daga wanka.

Karanta: Hanyoyi 9 Na Gyaran Fata.

2.        Maganin Mura.

Yana maganin mura. Yadda za ai amfani da shi, shi ne, Idan murar ta shafi magogwaro ne, sai a dafa shayi a zuba kanumfari da citta da tafarnuwa a ke sha, safe da yamma. Idan kuma murar ta haddasa ciwon kai, bayan amfani da shayin sai a samu man kanumfari ake shafawa a goshi, zai taimaka matuka gaya.

3.      Maganin Warin Baki.

Ya na maganin warin baki kwarai da gaske. Ga mai son amfani da shi ta wannan sigar, tun da farko zai samu kanumfarinsa, sai ya zuba a ruwa ya dafa shi, ya kyale shi ya tafasa, sannan ya sauke, ya bar shi ya huce, sai ya ke wanke baki da ruwan dumin a kalla sau uku a kullum. A jarraba za a ga fa'ida, In sha Allahu.

4.   Kara Girman Mazakuta.

Tun da farko za'a samu garin kanumfari, sai a cakuda shi da mansa, sannan a zuba man zaitun,  idan za a kwanta barci, a shafe ilahirin gaba da wannan hadi. Hakanan za'a shafa wannan hadi bayan fitowa daga wanka.  A  juri yin haka, in Allah ya so, za a ga fa'idarsa.

5.   Maganin Ciwon Hakori.

Akwai hanyoyi biyu da ake amfani da kanumfari wajen magance ciwon hakori, imma dai a yi amfani da mansa ko kuma garinsa.

Idan da man a ke son yin amfani, sai a samu auduga a zuba man daidai misali a lika a kan hakorin da ke ciwo, a danne da hakori har zuwa wani lokaci.

Idan kuma garin ne, tun da farko za a samu kanumfari, sai a nike shi har sai ya zama gari, sannan a zuba ruwa a kwaba shi gwargwadon bukata, sai a lika a jikin hakorin da ke ciwo.

6.        Maganin Amai.

 Ga Mata masu juna biyu dake fama da amai, sai a samu garin kanunfari daya bisa hudu na cokalin shayi, wato karamin cokali, a hada da babban cokali daya na zuma a cakuda, sannan a sha.

Ga amai da ya kasance na larura kadai, a samu kanumfari, daya bisa hudu na karamin cokali da  kofi daya na ruwa, sai a tafasa shi, sannan a saka sikari cokali daya a sha.

7.      Kara Karfin Mazakuta.

Ga duk Mai son kara karfin mazakutarsa don gamsar da iyali kuwa, sai ya samu Man kanumfari ya shafe gabansa da shi awa guda kafin ya fara jima'i da iyali.

8.     Maganin Ciwon Kunne.

Za a samu man kanumfari sai a hada shi da man Ridi a ke digawa a kunne mai ciwo duk lokacin da za'a kwanta barci.

9.    Maganin Kurajen Harshe.

Don Magance Kurajen Harshe, sai a samu garinsa, sannan a saka a jikin harshen ko kuma a zuba a ruwa a dinga kurkure baki da shi. Hakanan idan da dare ne, sai a bari har lokacin da  za'a kwanta sai a zuba a baki, za'a ga amfaninsa kafin wayewar gari, In sha Allahu.




No comments:

INA MAFITA

Maganin Maza

ASSALAFY ISLAMIC MEDICINE CENTER