Monday, May 25, 2020

BIRRAI SUN KORI WASU JAMA'A DAGA GARINSU

Abin al'ajabi:  BIRRAI SUN KORI WASU JAMA'A DAGA GARINSU

Shigowar Birai cikin wani yanki na jihar Legas ya tilasta wa mazauna garin Soluyi/Sosanya Gbagada, guduwa daga garin. A ranar Litinin din nan ne wasu daga cikin mazauna garin suka shaidawa manema labarai a jihar Legas cewa baza su iya cigaba da zama a garin ba.
Mazauna garin sunyi kira ga gwamnatin jihar data kawo musu dauki domin ceto su daga matsalar da suke ciki, inda suke bayyana cewa dabbobin suna karya kofofin su ta karfi suna shiga dakunan su lalata musu kayan abinci da sauran abubuwan amfani na rayuwa.
Shugaban mazauna kauyen Mista Adigun Olaleye ya ce a yanzu haka zaman garin ya zame wa da yawa daga cikin al'ummar garin matsala, saboda barnar da suke yi musu.
Ya ce shigowar dabbobin kauyen nasu yana da alaka da irin kusancin da suke dashi da wani daji wanda yake dauke da muggan dabbobi. Sannan ya kara da cewar, Biran sukan shigo kauyen ne a kowanne lokaci da suke so sannan kuma sukan karya kofofin su shiga dakunan su suyi musu barna.
Mista Olalaye ya shaidawa manema labarai cewa mazauna garin sun rubuta wa Ma'aikatar Aikin Gona ta jihar Legas wasika akan irin halin da suke ciki, amma har yanzu ba wanda ya kawo musu wani dauki.
"Sun ce sai mun biya su sannan zasu zo su kwashe biran da suka addabe mun," inji shi. Ya kara da cewar yanzu kusan shekara daya kenan suna fuskantar wannan matsalar, inda a yanzu haka abin ya fi karfin su.
A karshe Mista Olaleye ya roki gwamnatin jihar Legas data kawo musu dauki akan matsalar da suke ciki.


No comments:

INA MAFITA

Maganin Maza

ASSALAFY ISLAMIC MEDICINE CENTER