Sunday, September 28, 2025

Shin kun San amfanin lemun tsami

Amfanin lemon Tsami a jikin Dan adam.

Lemun tsami yana da mutukar amfani ga lafiyar dan’adam. Ga wasu daga cikin amfanin lemun tsami da kuma yadda ake amfani da shi.

-Gyara Fuska: Ana amfani da Lemun tsami wajan kauda kurajen fuska, fimfus da kyasfi, yana saka fuska ta kara kyau. Yadda ake amfani da shi, araba 1-2, rabin za a goge fuska da shi, za a yi haka na wasu lokuta, amma a kiyaye idanu, kuma kar a shafa a shiga rana sai an wanke tukunna.

-Dattin Hakori Da Warin Baki: A yi amfini da burushin wanke baki da ruwan lemun tsami a wanke hakora zu su fita kar, baki zai bar wari, amma kar a rika wankewa akai-kai sai lokaci saboda zai iya raunana karfin hakori.

-Warin Kashi (Hammata): Idan ana fama da ciwon warin kashi, ko rashin tsaftace hammata yadda ya kamata, idan an shafa lemun tsami a hammata zai kauda wannan warin.

-Rage Kiba Da Timbi (Teba): Wanda ke bukatar hakan, ya samu lemun tsami daya a ruwan sha da bai wuce kofi daya ba, lokaci-lokaci, kiba da taiba za su tafi.

-Rauni (Ciwo): Sabon raunin da bai wuce hankali ba, da zarar an matsa mai lemun tsami zai kame ya warke.

-Rage Sha’awa: Ana shan lemun tsami da lipton dan rage sha’awa. -Makyankyaro: Idan goge makyankyaro da lemun tsami akai-akai zai mutu.

-AMOSANI: Ana goga lemun tsami a kai bayan an aske gashin kai.

-Karni: Ana amfani da lemun tsami wajan kawar da karnin kifi. Amma a kula, idan mace ta yawaita amfani da lemun tsami to zai rage mata sha’awa. Haka mata masu ciki ka da su yawaita amfani da lemun tsami. Masu genbon ciki wato olsa, suma su kula wajan shan lemun tsami. Amma dukkan wadannan zai musu illa ne idan sun sha a ciki ba wai shafawa ba.






No comments:

INA MAFITA

Mu'jizar da ke cikin Zaitu

Amfanin Man zaitun Ciwon Ciki: Duk mutumin da yake ciwon ciki sai ya samu man zaitun kamar cikin cokali ya hada da garin habbatus saud...