Sunday, September 28, 2025

Amfanin tumatir ga lafiya da Adam

AMFANIN RUWAN TUMATIR


Tumatir yana dauke da sinadirrai daban daban masu dimbin amfani ga lafiyar jikin dan adam.

Bincike ya tabbatarda cewa a kowane kofi daya na ruwan tumatir na daukeda kaso 75 na sinadirin vitamin C, da kaso 22% na vitamin A.


Ana samun sinadirin Vit E da vitamin K da Folate da niacin,da pantothenic acid da riboflavin da B6 da potassium da manganese da phosphorus da copper da iron da magnesuim,da sodium da makamantansu.
Sinadirin potassium dake a cikin ruwan tumatir yana taimakawa matuka musan dan rage taruwa ko yawaitar sodium a cikin jiki da kuma rage hauhawan jini (blood pressure)

Lycopene wani sinadirane dake akoi a cikin ruwan timatir - yana taimakawa wajen karfafa jiyojin jini har zuwa ga zuciya.Haka kuma suna kona sinadiran cholesterol dake katutu a cikin jini ya daskare hanyoyin jini har ya haifarda wata illa ga zuciya.

Ruwan tumatir yana kare jiki daga barazanar kamuwa da kansa (ciwon daji).Bincike ya tabbatarda cewa wannan sinadirin na lycopene yana daukeda wasu magunna dake magance ciwon daji (anti imflammatory da anti cancer cells).Haka kuma lycopene din yana rage girman ciwo ko kurji na ciwon daji (tumor) dake tsira ga hanta,huhu,mamma,da kuma prostate cancer.

Yana rage kiba da tumbi da nauyin jiki sanadin samuwar sinadirin leptin.

  • A wani bincike da kasidar British journal of Nutrition in 2013 ta kaddamar ta gano cewa ruwan timatir na rage mafiyawan cutukan zuciya da kuma ciwon suga.
  • Ruwam tumatir na narkarda abinci a cikin kankanin lokaci(fast digestion)
  • Ruwan tumatir na kara samarda garkuwar jiki.(boosts immunity)
  • Ana tarfa zuma a tareda cokali uku na ruwan tumatir sai a tagasa a sha maganin cutukan ciki da zafin jiki.
  • Ana soya kwai da timatir da albasa dan samun ruwan maniyi ga jiki.
  • Ruwan timatir na karin jini a jika.
  • Sai dai da yake ruwan tumatir nada tsami(sour)dan haka mai olsa sai yasan yanda zai sha.
  • Haka kuma mai ciwon Acid reflux disease sai ya nemi shawara kamin ya sha da bayanin da za ayi mashi.


No comments:

INA MAFITA

Mu'jizar da ke cikin Zaitu

Amfanin Man zaitun Ciwon Ciki: Duk mutumin da yake ciwon ciki sai ya samu man zaitun kamar cikin cokali ya hada da garin habbatus saud...