Sunday, September 28, 2025

DABINO

ASSALAFY ISLAMIC MEDICINE CENTER

Amfanin dabino a jikin Dan adam.



Dabino yana daya daga cikin 'ya'yan itatuwa masu matukar amfani ga jikin adam saboda irin sinadaren da ya dauke dashi. Dabino yana girme ne a bishiya kuma 'ya'yan na cure ne kuma ya fi son yanayi mai zafi. Bayan 'ya'yan dabinon sun nuna ana iya cinsu hakan nan kokuma a cire kwallon da ke ciki a sarrafa su ta wasu hanyoyin don more lagwada da amfanin da dabinon ke dauke dashi.

Ga dai wasu fa'idoji guda shida da dabino keyi a jikin dan adam.

1. Dabino nada tasiri wajen kara kuzari ga masu aure Binciken masana kimiyyan sinadaren abinci ya nuna cewa dabino yana da matukar muhimmanci wajen kara kuzari tsakanin ma'aurata. Domin samun wannan fa'idar, sai mutum ya debi dabino kamar cikin hannunsa ya jika su cikin nonon akuya su kwana, da safiya sai a marka dabinon tare da nonon kuma ana iya kara zuma da cardamom. Wannan hadin yana da mutukar amfani wajen inganta kwanciyar aure.

2. Maganin gudawa Dabino da ya nuna sosai yana dauke da sinadarin potassium wanda ke da mutukar muhimmanci wajen magance gudawa. Sinadarin fibre da ke cikin dabino kuma yana taimakawa wajen magance basir da sauran matsalolin da ke da alaka da fitar bayan gida da gyaran ciki.

3.Lafiyar zuciya Dabino yana da matukar amfani wajen karawa wa zuciyar dan adam lafiya. An fi samun fa'idan da ke cikin dabinon idan an tsoma shi cikin ruwa ya kwana sai a dauko a ci da safe. Hakan yana da matukar amfani ga masu fama da ciwon zuciya. Sinadarin Potassium da ke cikin dabinon yana kare buguwar zuciya da wasu cututuka masu kama da hakan.

4.Karin kuzari Dabino na dauke da suga wanda basu da ila ga jikin dan adam kamar glucose, fructose da sucrose. Saboda hakan duk lokacin da mutum ke jin kasala idan yaci dabino zai samu kuzari nan take.

5.Karfafa garkuwan jiki da magance allergy Wani abin mamaki game da dabino shine yadda take dauke da sinadarin sulphur wanda ba'a cika samunsa a 'ya'yan itatuwa ba amma kuma yana da matukar amfani da jikin dan adam cikinsu kuwa harda kara karfin garkuwar jiki da magance 6.Yana taimakawa masu son mayar da jikinsu Dabino na dauke da suga, sinadarin Protein da ke gina jiki da kuma vitamins. Kilogram daya da dabino na dauke da calories 3,000 wanda hakan sun isa jikin dan-adam biyan bukatun ta na kwana daya. Idan mutum ya rame kuma yana son mayar da kibansa, dabino na iya taimakawa wajen gina jiki sai mutum ya jibinci cin dabinon

No comments:

INA MAFITA

Mu'jizar da ke cikin Zaitu

Amfanin Man zaitun Ciwon Ciki: Duk mutumin da yake ciwon ciki sai ya samu man zaitun kamar cikin cokali ya hada da garin habbatus saud...