ALAMOMIN KAMUWA DA SIHRI KO SHIGAR ALJANI JIKIN DAN ADAM
Hakika ko wace cuta da Allah ya saukar ya saukar da maganinta kuma masana ilimin magani sukan iya gane alamomi ko wace cuta, sau dadama akan samu matsala wajen magani musamman Wanda yashafi sihri ko aljani, wasu lokuta akan yitayin magani batareda angane hakikanin rashin lafiyarba, don haka akwai bukatar atabbatar da rashin lafiya kamin afara magani wannan xai taimaka sosai domin kaucewa magani daban ciwo daban. Don haka alamominda xaa iya gane shigar aljani/jinn jikin mutun ko alamun kamuwa da sihri
gasu kamar haka:
- 1. Yawan runtse idanu ko Kafewar idanu kafewa mai tsanani.
- 2. Dora hannaye akan idanu tareda rufesu.
- 3. Zafin jiki mai tsanani wanda akayita magani amma bai dainaba.
- 4. Yawan ciwon kanda bayajin magani.
- 5. Rashin magana da fushi mai tsanani.
- 6. Kebancewa daga cikin mutane.
- 7. Rikicewa da canzawar al'ada ga mata.
- 8. Yawan kasala yayin karatun alqurani ko wani aikin ibada.
- 9. Yawan kunci da bacinrai mai tsanani batareda daliliba.
- 10. Mugayen mafarki.
- 11. Aljani yakan canza yanayin wanda yashiga jikinsa, wasu lokuta.
- 12. Yawan mantuwa.
- 13. Kiyayyar wanda kakeso kai tsaye batareda wani daliliba, ko sayayyar wanda bakaso kai tsaye.
- 14. Kuka batareda daliliba.
- 15. Yawan firgita ko razana lokacinda mutun yake bacci.
- 16. Rashin bacci batareda wani daliliba.
- 17. Rashin kunya da saba umarnin iyaye wanda baasan mutun da hakanba.
- 18. Bayyanar aljani ajikin mutun ko yasanya marar lafiya gudu ko sambatu.
Wannan kadan daga alamunda zaa iya gane wanda yakamu da aljani ko sihri, ko biyomu donjin matakan samun kariya da kuma yanda ake warware sihri ko karar aljani.
WAR WARE SIHRI/ IBDALUS_SIHR
1. Miye sihri:- sihri kalmace ta larabci wadda take nufin juyadda al'amari ba yadda aka saba ganinsaba, yasamo asaline tun zamani mai tsawo kamar yadda Alqur'ani da sunna suka tabbatar da kasantuwarsa, wadanda sukeyinsa sukan kirashi da adduah ko magani amma ko shakka babu haramunne kuma kafircine. Wadanda suke sihri sune bokaye da mugayen malamai tareda hadinkan wadansu kafuran aljannu. Babu sabani akan kasantuwarsa kafirci ko kadan.
2. Meyasa akeyin sihiri? Wadanda sukeyin sihri sukanyishine akan bukatu daban daban kamar haka:
Jahilci da jahiliyya. Kwadayin duniya, mulki, sarauta ko Neman matsayi. Neman lafiya, Neman soyayya, Kawarda soyayyar wani, Al'adun gargajiya da wasanninsu, Nuna bajinta. Dukkan wadannan dililaine da yakesa akeyin sihri, amma ko da wane dalili akayishi toya sabawa addini kuma Allah yakanyi hushi da masu aikatawa.
3. Kashe kashen sihri: sihri yakan kasanye ta dalinda yasa akayishi ko hanyarda akeyinsa kamar haka:
A.Sihrin kulla soyayya kamar mata da miji Wanda asali babu soyayyar,
B. Sihrin raba sayayyar wani akan wani musamman mata da miji, mai arziki da yaronsa,
C.Sihrin wasiwasi ko juyadda al amari yawab mantuwa tareda rikitar dashi.
D. Sihrin rashin lafiya, Wanda akeyi domin shigarda cuta a jikin wani ayita magani amma baa gane matsalarba.
E. Sihrin hauka Wanda akeyi domin ahaukatar da wani ko wata.
F. Sihrin mallaka, Wanda da dama mata sukeyi domin mallake mazajensu.
G. Sihrin takhyeel shine Sihrin juyadda al'amurra abinda a hankalce bazai yiyuba ko bazaa iyayinsaba sai ayi anfanida sihri don kawar da hankalin mutane kamar tafiya cikin iska, shiga cikin bakin wata dabba a fifa ta dubura, ko tashi sama kamar tsuntsu da sauransu.
WAYE MAI SIHRI
insha Allah zamuyi bayani akan siffofin mai sihri, boka ko malamin tsibbo, domin wasu lokuta akan fada hannun wadannan miyagun mutane da sunan neman magani wanda da karshe akan fada cikin matsala, siffofinda yakamata a iya gane bokaye mai tsibbo ko mai sihri gasu kamar haka.
1. Sukan sanarda marar lafiya sunansa dana mahaifiyarsa da abinda yazo dashi tinkamin yayi bayanin abinda yazo dashi.
2. Sukan nemi wani sahen jikinsa kamar gashinsa ko tufafinsa musamman wanda take daukeda zufansa domin hada magani.
3. Neman wata dabba tareda wata siffa ta musamman, misali bakar akuya, bakar kaza da sauransu.
4. Amfani da kalamanda marar lafiya baya fahimtar abinda yake fada.
5. Daukaka sauti wajen karatun Qur'ani ko wadansu zantuka irin na masafa.
6. Sukan kebance daga cikin mutane.
7. Umartar marar lafiya ya kebance daga cikin mutane.
8. Umartar marar lafiya ya daina wadansu ayukkan ibada, kamar alwala, sallah, ko wankan janaba.
9. Umartar marar lafiya ya binne wani abu da sunan magani.
10. Yakan bawa marar lafiya wadansu kalamai ya dinga furuci dasu.
11. Labartawa marar lafiya abinda ya boyewa kansa.
12. Yin abubuwan ban mamaki wadanda suka sabawa kaida ko hankali.
Ko biyomu domin jin alamominda ake gane wanda akayiwa sihri da yadda ake war ware sihri da yardar Allah.
No comments:
Post a Comment