GYARAN NONO A SAUWAKE
GYARAN NONO
Mace tana fara fitar da nono daidai lokacin fara jinin al'ada yayin da Allah ya banbanta halittar jinsi daban daban ta yanda jinsin al'ummar africa bakaken fata ya banbanta dana wasu kasashen don haka abu na farko daya kamata jama'a su fara sani akwai banbanci tsakanin nonon baturiya dana bakar fata dan haka maganin gyaransu da namu ya banbanta
dan haka idan gyara nono kikeso girmansu ko tsayuwarsu tareda kyawunsu ba tareda yayi miki illah ba dole sai dai kiyi amfani da na gargajiya.
akwai banbanci tsakanin tsayar da nono da girmansa to amma saidai abu daya baya samuwa dole sai an hada da wani: ma'ana bazai yu nono ya tsaya kadai ba har sai girmansa ya karu haka zalika bazaiyu ace nono ya girma ace bai tsayaba kuma wadanda sukafi matsala a gyara nono sune wadanda ya kwanta shiyasa duk maganinda zai kara girman nono kuma ya tsayar dashi zai zama na musamman sannan za'a dauki lokaci ana shansa sabanin wanda kawai cikowa take bukata.
nonon mace yanada suffa kala kala nayi kokarin binciko bayanai akai tare da bin diddigin magunguna daya dace masu suffar nonon suyi kai harma wanda zaiyi da kowanne
1 na farko Akwai nono mai (mango Shape) wato Shine wanda bakinsa (nipples) yake Kallon sama irin wannan nonon baya zubewa da wuri irin wannan batashan wahalar gyara dan haka
zaki iya wannan yanda zakiyi ki samu ayaba (plantain) ki yanyankata ta bushe sannan ki daka garin to saiki samu aya ki wanketa kisaka gyada kisaka amarkada miki
saiki tace ruwan kina diban wannan garin plantain din kina zuba madara peak kinasha kamar sau biyu arana kafin sati daya zakiga canji sosai nononki zasu tashi su ciko.
sai kuma me bi masa wato (Pointed breast) shine zakuga yana kallon gaba (straight) gasKiya irin wannan nonon yana saurin faduwa domin riga kafin faduwarsa arinka kunun alkama: wato idan aka nika alkamar sai ayi kununta asaka nono da zuma anasha, idan kuma zubewa yayi
zaki hada farar shinkafa da alkama da garin habatussauda da aya da gyada ki nikasu suyi laushi ki tankade sai ki ajiye wannan garin kina hadashi da nono kinasha kullum wannan shine hadinda zaisa nono ya ciko ya kara girma kuma ko budurwa zata iyayi...
Akwai nono mai Kallon gefe (left and right) zakuga aKwai nisa sosai a tsaKanin nonuwa biyun zai iya kallon hagu ko dama wadannan sune sukafi matsala domin sa'ar mace wannan nono su zama kanana amma da zaran sun dan fara tashi to tabbas ta rasa nono domin gyaransu su dawo dole sai kinyi amfanida maganin nonon na musamman wato gari da akesha na kwana 30 ko 25 wannan kowanne irin nono mace take dashi zai temaka mata
Domin anyi amfanida ingantattun magunguna kuma na gargajiya, gadalin nono da nonon kurciya da 'ya'yan baure kumbura fage zakiyi garinsu idan suka bushe a inuwa sai ki samu hulba mai kyau ki hada, sai kuma kisamu aya da alkama da ridi da gyada da farar shinkafa da waken suya
dukkansu ki gyarasu kamar gyada da ridi da waken suya saiki soya su sai kiyi garinsu adakasu ko nikawa saiki samu ruwan zafi kamar rabin kofi ki zuba garin cokali daya ki gauraya ki zuba zuma ko zugar da nono ko madara ta ruwa peak kinasha kullum kafin wani lokaci zasu tashi koda kanana ne
kuna iya kiran mu don neman karin bayani akan wannan numba:
+2347016433333, +2347039620000
https://assalafyislamicmedicinecenter.blogspot.com/
https://youtube.com/c/assalafyislamicmedicinecenter








No comments:
Post a Comment