بسم الله الرحمن الرحيم
Da Sunan Allah Mai rahama Mai jinkai
Littafi Na Farko
Farawar wahayi
Sheikh al-Imam, Hafiz Uban Abdullahi, Muhammad dan
Ismail dan Ibrahim dan al-Mugirah mutumin Bukhara, Allah Yayi masa
rahama Amin ya ce:
BABI NA FARKO: - Bayanin yadda wahayi ya fara zuwa ga
Manzo Allah (S.A.W). Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: ‚Lallai, Munyi wahayi
zuwa gare ka, kamar yadda Muka yi wahayi zuwa ga Nuhu, da kuma Annabawan da
suka zo a bayansa (4: 163).
1.Imam Al-Bukhari (RA)
ya ce: ‚Al-Humaidi Abdullahi dan Zubair ya ba mu labari, ya ce, ‚Safiyanu ya ba
mu labari ya ce, Yahaya dan Sa’idu mutumin Madina ya
ba mu labari ya ce, Muhammad dan Ibrahim at-Taimiyyu, ya ba ni labari yana
cewa: Na ji Umar dan Khattab (RA) Allah Ya yarda da shi, akan munbari yana
cewa, ‚Na ji Manzon Allah (S.A.W.) yana cewa: ‚Sakamakon ayyuka
sun dogara ne akan niyyoyi kuma kowane mutum zai samu sakayya ne dangane da
abinda yayi niyya. Du wanda hijirarsa ta kasance don kwadayin
duniya, ko don ya auri wata mata, to, sakamakon hijirarsa ya dogara ga abin nan
da ya yi hijira dominsa.”
2. Imam Al-Bukhari (RA) ya ce: ‚Abdullahi dan Yusuf
ya ba mu labari, ya ce, Malik ya ba mu labari daga Hisham dan Urwata daga
Ubansa, daga A’ishatu Uwar mumunai (RA) Allah Ya yarda da ita cewa: Harith dan
Hisham yardar Allah ta tabbata gare shi, ya tambayi Manzon Allah (S.A.W.) ya
ce, Ya Manzon Allah, yaya wahayi yake zuwa maka‛? Manzon Allah (S.A.W.) ya ce,
‚Wani lokaci ya kan zo gare ni kamar gwarje (watau kararrawa). Wannan shi ne
hali wanda ya fi tsanani a gare ni. Ya ratsa jikina (kafin Jibirilu ya tafi) na
haddace abin da ya fada. Wani lokaci Mala’ika yana siffantuwa a gare ni da
siffar mutum namiji, ya yi mini magana, in haddace abin da yake fada. Aishatu
(Allah Ya yarda da ita) ta ce, ‚Hakika na gan shi lokacin da wahayi ke sauka
gare shi a ranar da ake tsananin sanyi, gumi na ketowa daga gefen kunnensa
(goshi).
3. Imam Al-Bukhari (RA) ya ce: ‚Yahaya dan Bukair ya
ba mu labari ya ce, ‚Laithu ya ba mu labari daga Ukail daga dan Shihab daga
Urwata dan Zubair daga Aishatu uwar muminai (RA) Yardar Allah ta tabbata gare
ta, ta ce, ‚Farkon abin da aka fara yi wa Manzon Allah na wahayi, shi ne
mafarki na kwarai a cikin barci. Sai ya kasance ba ya ganin wani mafarki face
sai misalin abin ya bayyana gareshi kamar wayewar gari. Bayan haka sai aka sa
masa son ya kebantu (kadaita) daga mutane. Ya rika kadaituwa a kogon Hira yana
ta tunanin ibada, yakan yi kwanaki masu adadi kafin ya koma ga iyalinsa, kuma
yana tafiya da guzurin abin da zai ci, sa’annan ya koma wajen Khadija don samo
wani guzurin ya koma. Yana kan haka har gaskiya ta bayyana gare shi, yana cikin
Kogon Hira Mala’ika ya zo masa, ya ce masa ‚Yi karatu‛, ya ce ‚Ai ni ba mai
karatu ba ne‛ Ya ce, sai ya kama ni ya matsani, har ya kai iyakar wahala gareni
bayan haka ya sake ni. Sai ya ce, ‚Yi karatu‛ sai na ce Ni ba mai karatu ba ne
sai ya sake matsani na biyu. ‚Sai ya ce, ‚Yi karatu. Sai na ce, Ni ba mai
karatu bane‛. Sai ya sake matsani na uku ya sake ni, sai ya ce: Ka yi karatu da
sunan Ubangijinka, wanda ya yi halitta. Ya halicci mutum daga gudan jini. Ka yi
karatu, kuma Ubangijinka lallai shi ne mafi girma‛. Sai Annabi tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi ya koma da wannan (aya), zuciyarsa tana
makyarkyata, ya shiga wajen Khadija ‘yar Khuwailid (Allah Ya yarda da ita), ya
ce, ‚Ku lullube ni! ‚Ku lullube ni!!‛ Suka lullube shi, har tsoro ya fita daga
gare shi. Ya ce wa Khadija, bayan ya ba ta labarin abin da ya faru. Hakika na
ji tsoro a kaina‛ sai Khadija ta ce, Ba haka ba ne, wallahi Allah bai bakanta
maka rai har abada don kai kana sadar da zumunci kana daukar wahalar mutane,
kana ba wanda ba shi da shi, kana ci da bako, kana taimako wajen kau da musibu
a kan gaskiya. Sai Khadija ta tafi da shi zuwa ga Waraka dan Nawfal dan Asad dan
Abdul’uzza dan Baffan Khadija. Shi kuma Mutum ne wanda yake Addinin Nasara, tun
Zamanin Jahiliyya. Ya kasance yana rubuta littafin Linjila, a cikin harshen
Ibraniyawa gwargwadon abin da Allah Ya bashi ikon rubutawa. Ya zama tsoho
tukuf, har ya makance. Sai Khadija ta ce masa, Ya kai dan Baffa! Ka saurari dan
dan’uwanka. Sai Waraka ya ce da shi, Ya dan’uwana, me ka gani? Sai Manzon Allah
(S.A.W) ya ba shi labarin abin da ya gani, sai Waraka ya ce, ‚Wannan shi ne
Manzon alheri, wanda Allah ya aiko shi zuwa ga Musa. Sai ya ce, Kaicona! Da ma
a ce ina da sauran karfi ko da zanyi tsawon rai lokacin da mutanenka za su fitar
(kore) ka, sai Annabi (S.A.W) ya ce, Su masu fitar da ni ne? Ya ce, I, babu
wani mutum da zai zo da misalin abin nan da ka zo da shi, face an yi kiyayya da
shi. In har wannan lokaci ya riske ni, zan taimake ka, taimako mai karfi. Ba a
dade ba, sai Waraka ya mutu. Bayan haka sai wahayi ya yanke.
dan Shihab ya
ce: Abu Salmah dan Abdurrahman ya ba ni labari cewa: Jabir an Abdullahi mutumin
Madina (RA) ya ce, Annabi yana ba da labari game da yankewar wahayi, ya ce, a
cikin labarinsa, ‚Ina cikin tafiya, sai na ji sauti daga sama, sai na daukaka
ganina sai na ga Mala’ikan nan da ya zo gare ni a Kogon Hira yana zaune a kan
kujera tsakanin sama da kasa, kuma aka firgitar da ni, sai na koma na ce, Ku
lullube ni, sai Allah Ya saukar da aya (74: 1-5). Ya kai wanda ya lulluba da
mayafi tashi ka yi gargadi. kazanta, ka kaurace mata. Bayan haka sai wahayi ya
yi ta sauka, bi da bi. Abdullahi dan Yusuf da Abu Salih da Hiral dan Raddad
dukka sun karbo wannan daga Zuhuri, Yunus da Ma’amar suka ce: ‚Kafadunsa
(Annabi) na rawa, lokacin da yake ba da labara.
4. Imam Al-Bukhari (RA) ya ce: Musa dan Isma’il ya ba
mu labari, ya ce, Ya ji daga Abu Awanata, shi ma ya ji daga Musa dan Abi
Aishatu daga Sa’id dan Jubair, daga dan Abbas (RA) cewa: Allah Ya ce, wa Annabi
a cikin Alkur’ani, Kada ka motsar da harshenka don ka yi gaggawar haddacewa. (dan
Abbas) ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya kasance yana kokarin ya haddace wahayi da
tsanani har yana motsa labansa. dan Abbas (RA) ya ce, Ni zan motsa nawa gare ku
kamar yadda Manzon Allah (S.A.W) ya ke motsa nasa (labba), Sa’id dan Jubair
kuma ya ce, Ni zan motsa na wa kamar yadda na ga dan Abbas yana motsa nasa. Sai
ya motsa labbansa. Yace ana nan haka sai Allah Madaukaki Ya saukar da cewa, Kada
ka motsar da harshenka game da shi domin kayi gaugawar rike shi (Alkdur’ani).
Lallai ne wajibine a gare Mu, Mu tara shi. Mu (tsare maka) karatunsa
(75:16-17). (Watau: tun da Mune Muka saukar da shi, Mu za mu hore maka shi,
kada ka motsa harshenka don ka yi gaggawar haddace shi.) dan Abbas ya ce: Tara
shi cikin kirjinka aikin Mu ne, kuma karanta shi aikin Mu ne. Allah Ya ce: To,
idan Muka karanta shi, sai ka bi karatunsa (75:18). dan Abbas ya ce: ma’anarsa,
Ka saurara, kuma ka yi shiru. Allah (SWT) Ya ce: Sa’annan lallai ne, wajibi ne,
agare Mu, bayaninsa (75:19).‛ dan Abbas ya ce: Bayaninsa, aikin Mu ne, kuma
abayan saukar wannan aya, Manzon Allah (S.A.W) ya kasance idan Jibrilu (AS) ya
zo masa, yana saurarawa. Idan Jibrilu ya tafi, sai Manzon Allah (S.A.W) ya
karanta kamar yadda (Jibrilu) ya karanta masa.
5. Imam Al-Bukhari (RA) ya ce: ‚Abdanu ya ba mu
labari, yana cewa, ya ji daga Abdullahi ya ce: Yunus ya ba su labari ya karbo
daga Zuhri, Hawwala Sanad Bishinu dan Muhammad ya ba mu labari ya ce, Abdullahi
ya ba mu labari ya ji daga Yunus, da Ma’amar. Su kuma daga Zuhuri kamar yadda
suka fada. Ubaidullahi dan Abdullahi ya ba ni labari daga dan Abbas (RA) yana
cewa, Manzon Allah (S.A.W) ya fi kowa kyauta (alheri), ya fi kuma yawaita
kyauta, a cikin watan Azumin, yayin da Jibrilu (AS) yake zuwa masa. Jibrilu
(AS) yana zuwa gare shi a kowane dare na watan Ramadan, yana karanta masa
Al-kur’ani tare, hakika Manzon Allah (S.A.W) ya fi kowa alheri, don alherinsa
ya fi iska mai gudana (kawo giragizan ruwan sama).
6. Imam Al-Bukhari (RA) ya ce, ‚Abul Yamani al-Hakam
dan Nafi’i ya ba mu labari, ya ce, Shu’aibu
ya ba mu labari ya ji daga Zuhuri. Shi kuma daga Ubaidullahi dan Abdullahi dan
Utba dan Mas’ud cewa: Lallai Abdullah dan Abbas (RA) ya ba shi labara cewa: Abu
Safiyanu dan Harb (RA) ya ba shi labari, cewa: Lallai Hirakla (Sarkin Rumawa)
ya aika masa a lokacin yana daga cikin ayarin kuraishawa wadanda sun kasance
suna fatauci a kasar Sham (Syria), cikin dan lokacin da Annabi (S.A.W) ya kulla
alkawari na sulhun barin yaki ko fada tsakaninsa da Abu Safiyanu da kafiran Makka.
Sai suka je masa (Hirakla) a kudus lokacin da suke acan. Ya kira su zuwa
fadarsa, yana tare da manyan ‘yan majalisarsa daga manyan Romawa. Sa’annan ya
kirawo su, kuma ya kira Tafintansa (mai fassara) ya ce, A cikinku wane ne ya fi
kusancin zumunta da mutumin nan da ke cewa shi Annabi ne? Sai Abu Safiyanu ya
ce, Ni ne mafi kusancin zumunta da shi. Sai Hirakala ya ce, To, ku matso da shi
kusa da ni, kuma ku matso (kusanto) da abokan tafiyarsa, ku sanya su baya gare
shi, Sa’annan yace, wa Tafintan (mai fassara): Kace musu (abokan tafiyarsa), ni
mai tambayar wannan (Abu Safiyanu) labarin wannan mutum (Annabi) ne, idan ya fada
mini karya, to, ku karyata shi. (Abu Safiyanu) ya ce, Wallahi ba don ina jin kunya
ba kuma kada sun bayyana karya agare ni ba, da na yi masa karya. Farkon abin da
(Hirakala ya tambaye ni game da labarin Annabi) shi ne, Yaya dangantakarsa take
gareku? Sai na ce: shi dan dangi ne. Hirakala ya ce, ‚ko a cikin kabilarku wani
ya taba fadin wannan magana, cewa shi Annabi ne a gabaninsa? Sai na ce masa, A’a
Ya ce A cikin Ubanninsa (Iyayensa) akwai wanda ya taba zama Sarki? (Abu
Safiyanu) na ce, A’a, Sai Hirakla ya ce, Manyan mutane ne su ke binsa ko kuwa
talakawa? Sai na ce: Talakawa ne mabiyansa. Hirakla ya ce, karuwa suke ko
raguwa? Na ce karuwa suke yi. Ya ce, Ko akwai daya daga cikinsu wanda yake fita
don kyamar Addinin, bayan ya shiga? (Abu Safiyanu). Na ce, A’a. Hirakala ya ce,
Ko ya taba yin yaudara? Na ce, A’a! Sai dai yanzu muna cikin wani alkawari na
wani lokaci da shi, ba mu san abin da zai aikata ba. (Abu Safiyanu ya ce), Ban
sami wata kalma ta suka da zan shigar da ita ba, sai wannan. Hirakala ya ce, Yaya
yakinku yake da shi? Sai na ce, Yaki
tsakaninmu jan masaki ne, yana rinjayar mu, muna rinjayarsa. Hirakala ya ce, To,
me yake umurtanku da shi? Na ce, Yana cewa, Ku bauta wa Allah Shi kadai, kada
ku hada kowa tare da Shi wajen bauta. Ku bar abin da iyayenku suka fada. Yana
umurtar mu da yin Salla da gaskiya da kamewar kai daga zunubi da sadar da
zumunta. Sai Hirakla ya ce, wa Tafintansa, Ka ce masa, Na tambaye ka
dangantakarsa, ka ce dan dangi ne, to, haka nan manzanni suke. Kullum ana aiko
su ne daga cikin ‘yan kangi (watau a cikin zuriyarsu). Hirakla ya ce, Na
tambaye ka, shin daya daga cikinku ya taba fadar wannan maganar, ka ce a’a. To,
da an sami wani wanda ya fadi, wannan maganar a gabaninsa da sai in ce, wani
mutum ne da ke koyi da abinda aka fada a gabaninsa. Hirakla ya ce, Na tambaye
ka ko akwai wani daga cikin iyayensa da ya taba yin sarauta ka ce mini a’a. To,
da ka ce mini akwai wanda ya taba yin sarauta a cikin iyayensa, da sai in ce
wannan mutum yana neman sarautar mahaifinsa (ubansa) ne. Hirakla ya ce. Na
tambaye ka kun taa tuhumarsa da karya, ka ce a’a. To, lallai ni, na sani tun da
dai bai taba yi wa mutane karya ba to, ba zai dangana karya ga Allah ba. Hirakla
ya ce, Na tambaye ka; manyan mutane ke binsa ko talakawa, ka ce, talakawa ne
mabiyansa. Haka ne, su ne mabiyan manzanni (Annabawa). Hirakla ya ce: Na
tambaye ka, suna karuwa, ko suna raguwa? Kace suna karuwa, to, haka al’amarin
imani ya ke, idan ya shiga, sai ya cika. Hirakla ya ce: Na tambaye ka, mabiyinsa
yana fita daga Addinin don kyama bayan ya shiga? Ka ce, a’a. To, haka imani
yake lokacin da ya kama zukata. ‚Hirakla yace: ‚Na tambayeka ko yana yaudara?
Kace ‚A’a, to haka manzanni suke, ba su yaudara. Na tambaye ka, da me yake umurtarku?
Ka ce, yana umurtanku, ku bauta wa Allah shi kadai kada ku hada wani da shi,
yana hana ku bauta wa gumakka. Yana umurtarku da ku yi Sallah da fadin gaskiya
da kamewar kai. To, in abin da kake fada gaskiya ne, sai ya mallaki wurin kafafuwan
nan nawa. Hirakla ya ce: Na san zai fito, amma ban yi zaton daga cikinku ba ne.
Da na san zan sadu da shi, da na yi shirin tarbarsa (haduwa da shi). Kuma da na
kasance gunsa, lallai da na zama mai wanke duddugensa (dugadugansa). Sa’annan
ya yi kira cewa, a kawo wasikar da Manzon Allah (S.A.W) ya aiko manzonsa da ake
kira Dihiyatu da ita, zuwa ga Shugaban Busura yace, ya aika ta zuwa ga Hirakla!
Da mai fassara ya karanta wasikar, ta ce: -
Da Sunan Allah Mai rahama Mai jinkai. Daga Muhammad
bawan Allah, Manzon Allah, zuwa ga Hirakla Shugaban Rumawa. Aminci ya tabbata
ga wanda ya bi shiriya. Bayan haka, ina kiran ka da kiran Musulunci. Ka mika
wuya ka tsira, Allah Ya ba ka ladanka kashi biyu. In kaki, zunubin Irisiyyin
(manoma) yana kanka. Sai ya karanta masa ayar kur’ani cewa, ‚Ya ma’abuta
Littafi, ku tafo (zo) zuwa ga wata kalma daidai tsakaninmu da ku. Kada mu bauta
wa kowa face Allah (Shi kadai). Kada mu hada wani da Shi, sashinmu kada ya riki
wani sashi abin bautawa. Idan suka kawar da kai, to, ku ce: ku shaida lallai
mu, masu mika wuya ne ga Allah (3:64).
Sai Abu Safiyanu ya ce, ‚Lokacin da mai fassara ya
fadi abin da ya fada, na karatun wasikar Annabi, sai maganganu suka yawaita gareshi
(Hirakla) aka daukaka murya sama sai aka fitar da mu. Sai na ce wa abokan
tafiya ta, lokacin da aka fidda mu, ‚Hakika, al’amarin nan na dan Abi-Kafshata
(alkunya ce ga mahaifin Annabi) ya kasaita, tun da Hirakala sarkin Turawa ke
tsoronsa. (Abu Safiyanu ya ce), Tun daga nan, ban gushe ba ina mai sakankance
cewa, wannan al’amari zai rinjaya, har Allah Ya sanya son Musulunci a gare ni.
Dan Nazuri Hakimin kudus da Hirakla sun kasance
manyan Fada-Fada na Nasara, a Sham (Syria). dan Nazuri yana ba da labari, cewa:
Lokacin da Hirakla ya taho kudus, ya wayi gari yana mai bacin rai. Wani sashi
daga cikin manyan malamansa (makusantarsa). Suka ce, lallai kamannunka
(halayenka) sun canza. dan Nazuri ya ce, Hirakla ya kasance mai fasaha ne. Yana
duba a taurari, ya fadamusu abin da zai faru a lokacin da suka tambaye shi
cewa, Ni na gani a cikin dare a lokacin da na duba taurari, na ga wasu mutane masu
kaciya mulkinsu zai bayyana. To, wannan kuwa ya bayyana. Wanene ke yin kaciya
cikin wannan al’umma? Sai suka ce masa‚ Babu masu yin kaciya sai Yahudawa, kada
ka damu da su." Suka ce masa, Rubuta zuwa ga Sarkin Madyana ka umurce shi
dakashewar Yahudawan da ke zaune a kasar. Muna cikin wannan al’amari, sai aka
zo ma Hirakla da wani mutum wanda Sarkin Gassan ya aiko masa da shi, yana ba da
labarin bayyanar Annabi (S.A.W). Lokacin da aka ba Hirakla wannan labari, sai
Hirakla ya ce, Ku tafi ku duba ko wannan mutum yana da kaciya ko ba shi da shi.
Da aka duba, sai aka ce yana da kaciya. Ya tambaye shi, al’adar Larabawa. Sai
ya ce, Su, ma suna yin kaciya. Sai Hirakla ya ce. To, wannan mulkin wannan
al’umma ne, ya bayyana. Sai Hirakla ya rubuta wasika zuwa ga wani abokinsa
Sarkin Rumiya wanda shi ma yana da Ilmi irin nasa, sa’annan sai Hirakla din ya
tafi Himsa. Bai bar Himsa ba har sai da amsar wasikar da ya yi ta zo masa, yana
mai amincewa da ra’ayinsa (Hirakala) akan bayyanar Annabi (S.A.W), kuma lallai
Annabi ne, sai Hirakala ya yi izni ga Shugabannin Rumawa da su shiga cikin wani
dakin taro nasa da ke Himsa, da suka shiga sai ya ba da umurnin a rufe kofofi,
sai aka kukkulle. Ya hau daga sama ya fuskance su ya ce, Ya jama’ar Rumawa!
Shin kuna son rabo da shiriya kuma mulkinku ya tabbata. To, ku yi mubaya’a ga
wannan Annabi. Sai suka yi bore irin boren jakunan dawa (daji), suka nufi kofofi,
suka iske su a kukkulle (rufe). Lokacin da Hirakla ya ga kyamarsu ta kai
matukar kyama ga irin maganar da ya yi, sai ya debe tsammanin imani agare su,
sai ya ce Ku dawo da su. Ya ce: Ni na fada muku waccan Magana ce don in jarraba
karfin imaninku a kan Addininku. Saboda haka na ga karfin imaninku. Sai suka yi
sujada a gare shi suka kuma yarda da shi. Wannan shi ne karshen al’amarin
Hirakala. Salihu kan Kaisan ne ya karbo wannan magana, shi da Yunus da Ma’amar,
daga Zuhuri.
LITTAFIN IMANI
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai.
BABI
NA FARKO: - Kuma bisa fadar Annabi (S.A.W) cewa: An gina Musulunci akan
abubuwa biyar. Shi magana ne kuma da aiki yana karuwa yana kuma raguwa. Allah Madaukaki
Ya ce, Don Ya kara wa wadanda suka yi imani imaninsu, Kuma Muka kara musu wata
shiriya (18.13). Kuma Allah Na cewa, Yana kara wa wadanda suka shiryu, da wata
shiriya. Kuma lallai wadanda sukashiriya, Yana kara musu wata shiriyar, kuma Ya
sanya musu tsoronSa, kuma Ya kara wa wadanda suka yi imani, da wani imani. (19:76)
Kuma da maganar Allah Madaukaki Ku ji tsoronsu, sai suka kara imani’’ (9:124).
Kuma da maganar Allah Madaukaki Bai kara musu komai ba, fae imani da mika
wuya’’ (3:173). Soyayya don Allah da fushi don Allah, duk suna cikin imani.
Hakika Umar dan Abdul-Aziz, ya rubuta takarda zuwa ga Adiyyi dan Adiyyi, yana
cewa, ‚Lallai imani yana da farillai, yana kuma da dokoki yana kuma da iyakoki,
kuma yana da sunnoni. Duk wanda ya cika su. To, lallai imaninsa ya cika. Wanda
bai cika su ba, to, imaninsa bai cika ba. Idan na rayu, zan bayyana muku su har
ku yi aiki da su. Idan na mutu, to, ba ni yin kwadayi ga abokantakarku. Kuma
Annabi Ibrahim (AS) ya ce, Amma don zuciyata ta natsu’’ (2:260). Mu’adhu (R.A) ya
ce, Zauna tare da mu ko na dan lokaci, don ko ma sadaukar da wannan lokacin
zuwa ga imani. dan Mas’ud (R.A) ya ce: Sakankancewa imani ne dukkansa. dan Umar
(RA) ya ce: Bawa ba ya kaiwa ga gaskiyar tsoron Allah, sai ya bar kokwanto
cikin kirjinsa (zuciya). Mujahid ya ce, dangane da fassara wannan aya, An hukunta
gare ku‛ ma’ana: Mun yi wasiyya gare ka Ya Muhammad da shi wannan hukunci,
Addini daya. dan Abbas (RA) yafassarar maganar Allah wadda Yake cewa, Shario’i
da tsarin Musulunci cewa: Ana nufin: Tafarkin Musulunci da Sunna.
BABI
NA BIYU: - Addu’arku ita ce imaninku. (A ganin Shehun malami Imam Nawawi,
kuskure ne rubuta Babi a nan).
7. Imam Al-Bukhari (RA) ya ce: Ubaidullahi dan Musa
ya ba mu labari, yana cewa Hamzalata dan Abi Safiyanu ya ba su labari, ya karbo
daga Ikrama dan Khalid daga dan Umar (RA), yardar Allah ta tabbata gare su, ya
ce: Manzon Allah (S.A.W). Ya ce: An gina Musulunci kan abubuwa guda biyar (1)
Tabbatar da cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma da tabbatarwa
cewa Annabi Muhammad (S.A.W) Manzon Allah ne. (2) Da tsayar da Sallah (3) Da
kuma bayar da Zakka (4) Da Hajji (5) Da yin Azumin wata Ramadan. (Kasancewar
wan nan hadisi cikin wan nan babi na karantar da sallar da azuminku da zakkarku
da hajjinku na daga cikin imaninku da bayan imani da Allah da ManzonSa).
BABI NA UKU: - Game da al’amuran da suka shafi imani.
Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: Fuskantar Gabas ko Yamma (Lokacin Sallah) ba
shi ne biyayya ba, biyayya shi ne ban gaskiya ga Allah da ranar al-kyama. Da
ban gaskiya da Mala’iku da ban gaskiya da Littafi (al-kur’ani) da ban gaskiya
ga Annabawa da bayar da dukiya bisa son mai bayarwa: Ga ‘yan’uwa na kusa, da marayu
da talakawa da matafiyi (wanda guzurinsa ya yanke) da mabarata da ‘yantar da
bayi. Da ya tsayar da Sallah bayar da Zakka. Da masu cika al-kawari in sun
kauka, da masu hakuri acikin halin wahala ko tsanani kuma da lokacin tsananin
yaki. Wadannan, su ne suka gasganta, kuma su ne masu tsoron Allah’’ (2:177). Kuma
(dan Abbas (RA) ya ce: Allah Ya ce: ‚Ha kika muminai sun samibabban rabo’’ (23:1).
8. Imam Al-Bukhari (RA) ya ce: Abdullahi dan Muhammad
ya bamu labari, cewa: Abu Amir al-Akadi ya ba mu labari daga Sulaiman dan
Bilal, daga Abdullahi dan Dinar daga Uban Saleh daga Abu Hurairah (RA) yardar
Allah ta tabbata a gare shi. Ya karbo daga Annabi (S.A.W) ya ce, Imani ya kasu
kashi sittin da wani abu (bakwai), kunya kashi (yanki) ne daga cikin imani.
BABI NA HUDU: - Musulmi shine wanda Musulmai suka kubuta
daga cutarwar harshensa da hannuwansa.
9. Imam Al-Bukhari (RA) ya ce: Adam ban Abi Iyyas ya
ba mu labari, ya ce, ‚Shu’uba ya ba mu labari ya karbo daga Abdullahi dan Abi
Safar da Isma’ila daga Sha’abi ya karbo daga Abdullahi dan Umar (RA), yardar
Allah ta tabbata a gare su daga Annabi (S.A.W) ya ce, Musulmi shi ne wanda
Musulmai suka kubuta daga cutarwar harshensa da hannuwansa. Mai kaura shi ne
wanda ya kaurace wa abin da Allah Ya yi hani gare shi. Abu Ma’awiyya ya ce, Dawud
ya ba mu labari daga Amir, shi Amir ya ce, ya ji Abdullahi yana cewa, ya karbo
daga Annabi (S.A.W) sai Abdul A’ala ya ce, ya karbo daga Dawud daga Amir daga
Abdullahi daga Annabi (S.A.W).
BABI NA BIYAR: - Wane Musulunci ne ya fi (Musuluncin
wane ne yafi)?
10. An karbo daga Sa’idu dan Yahaya dan Sa’id
Bakuraishe ya ce, Ubana ya ba mu labari ya ce, Abu Burda dan Abdullahi dan Abu
Burda, ya ba mu labari, daga Abu Burda, daga Abi Musa (RA) yardar Allah ta
tabbata a gare shi ya ce, ‚Sun ce ya Manzon Allah! Wane Musulunci ne ya fi?
Annabi (S.A.W) ya ce: Wanda Musulmai suka kubuta daga (sharrin) harshensa da
hannuwansa.
BABI NA SHIDA: - Ciyar da wadansu daga abinci yana
cikin Musulunci.
11. An karbo daga Amru dan Khalid ya ce: Laith ya ba
su labari daga Yazidu daga Abil Khair daga Abdullahi dan Amri, yardar Allah ta
tabbata a gare su, Wani mutum ya tambayi Annabi (S.A.W), Wane (aikin) Musulunci
ne, ya fi alheri? Annabi (S.A.W) ya ce: Ka ciyar da abinci, ka yi sallama ga
wanda ka sani da wanda ba ka sani ba.
BABI NA BAKWAI: - Ka so wa dan’uwanka abin da kake so
wa kanka, yana daga cikin imani.
12. An karbo daga Musaddad, ya ce, Yahaya ya ba mu
labari daga Shu’uba daga katadata daga Anas (RA) yardar Allah ta tabbata gare
shi daga Annabi (S.A.W) daga Hussaini Mu’allami ya ce: katadata ya ba mu labari
daga Anas, ya karbo daga Annabi (S.A.W), ya ce dayanku ba ya yin imani, sai ya
so wa dan’uwansa abin da yake so wa kansa. (Imanin dayanku bai cika, har sai ya
so wadan’uwansa abinda yake so wa kansa).
BABI NA TAKWAS: - Son Annabi (S.A.W) yana daga cikin
imani.
13. An karbo daga Abu Yamani, ya ce, Shu’aibu ya ba
mu labari daga Uban Zinad daga A’araj. Ya ce, ya karbo daga Abi Hurairah (RA)
yardar Allah ta tabbata a gare shi, lallai Manzon Allah (S.A.W) ya ce, Na
rantse da Wanda raina yake hannunSa, dayanku ba ya zama mumini sai kaunarsa
gare ni ta fi kaunar da yake da ita ga mahaifinsa da dansa. (Imanin dayanku bai
cika, har sai na kasance ni, yafi so fiye da iyayensa da ‘yayansa).
14. An karbo daga Yakubu dan Ibrahim ya ce, dan
Ulayya ya ba mu labari daga Abdul-Aziz dan Suhaib daga Anas (RA) ya karbo daga
Annabi (S.A.W) Hawwala Sanad ya ce, Adam ya ba mu labari ya ce, Shu’uba ya ba
mu labari daga katadata daga Anas daga Annabi (S.A.W), ya ce dayanku ba ya zama
mumini sai kaunarsa gare ni ta kasance ta fi kaunarsa ga mahaifinsa da dansa da
mutane baki daya (Imanin dayanku bai cika har sai ya so ni fiye da mahaifinsa,
da ‘yayansa da dukkan mutane).
BABI NA TARA: - dandadon (zakin) imani.
15. An karbo daga Muhammad dan Muthanna ya ce, Abdul
Wahabu Thakafi ya ba mu labari daga Ayyub daga Abi kilaba daga Anas (RA) daga
Annabi (S.A.W) ya ce: Abubuwa uku wanda suka kasance gare shi, ya sami dandanin
imani (1) Yakasance Allah da ManzonSa su, suka fi zama abin so (kauna) a gare
shi fiye da komai (2) Shi so mutum, kuma yana son shi ne domin Allah. (3) Ya yi
kyamar komawa ga kafirci kamar yadda yake kyamar (kin) a jefa shi wuta.
BABI NA GOMA: - Son mutanen Madinah (Ansar) yana daga
alamar imani.
16. An karbo daga Uban Walid ya ce, Shu’uba ya ba mu
labari daga Abdullahi dan Abdullahi dan Jabar ya ce, Na ji Anas (RA) daga
Annabi (S.A.W) ya ce, Alamar imani, son Mutanen Madina. Alamar munafunci!
kinsu.
BABI NA GOMA SHA DAYA: - kyamar munanan ayyuka.
17. An karbo daga Abu Yamani ya ce, Shu’aibu ya ba mu
labari daga Zuhuri, daga Abu Idris A’izullah dan Abdullahi, cewa: Ubadata dan
Swamiti (RA) yardar Allah ta tabbata gare shi, yana cikin wadanda suka halarci
yakin Badar, Kuma yana daga cikin wadanda suka ba da rayuwarsu ga Annabi
(S.A.W), a akaba (Kuma shi Nakib ne, watau: mutumin da ke cikin jagorancin
kungiyar mutane a daren alkawari Akaba). A wannan lokaci akwai wasu jama’a daga
sahabban Manzon Allah (S.A.W) suna kewaye da shi, sai ya ce: Ku dauki alkawari
gare ni, ba za ku hada bautar Allah da wani ba, ba za ku yi sata ba, ba za ku
yi zina ba, ba za ku kashe ‘ya ‘yanku ba, ba za ku zo da wata karya ba wadda
zaku zama masu kaga ta tsakanin hannuwanku da kafafuwanku (zargin mara laifi),
ba za ku saba ba ga wani abu na alheri. Wanda ya cika daga cikinku sakamakonsa
na ga Allah. Wanda ya aikata wani abu da aka hana shi, aka yi masa azaba a
kansa a nan duniya ya kasance gafartawa gare shi. Wanda ya aikata wani abu da
aka hana, sa’an nan Allah Ya rufi asirinsa, to, al’amarinsa yana ga Allah. In
ya so Ya gafarta masa, in Ya so Ya yi masa azaba. Muka dauki alkawari a kan haka.
BABI NA GOMA SHA BIYU: - Gudun fitina yana cikin
addini.
18. An karbo daga Abdullahi dan Maslamata daga Malik,
daga Abdurrahman dan Abdullahi dan Abdurrahman dan Abi Sa’asa’ata, ya karbo
daga Ubansa, daga Abi Sa’idin al-Khudri shi, yana cewa, Manzon Allah (S.A.W) ya
ce: Lokaci ya yi kusa (ya zama) fiyayyar dukiyar Musulmi ta kasance tumaki,
yana bin su a cikin kwarin duwatsu da wuraren ruwa, ya tsira da Addininsa daga
fitina.
BABI NA GOMA SHA UKU: - Ana kama mutum da abinda
zuciyarsa ta kudura. Da fadar Annabi (S.A.W), ‚Na fi ku sanin Allah, Lallai
sani, aikin zuciya ne, domin fadar Allah Madaukaki ‚Sai dai ana kama ku ga
abinda zukatanku suka yi tsiwirwiri (kudurce) (2:225).
19. An karbo daga Muhammad dan Salami ya ce, Abdatu
ya ba mu labari daga Hisham, ya karbo daga Babansa, daga Aishatu, (RA) Allah ya
yarda da ita, ta ce, Manzon Allah (S.A.W) ya kasance idan ya sanya su aiki,
yakan sanya su abinda suke iyawa. Suka ce: Mu ba kamarka muke ba, ya Manzon
Allah! Lallai Allah Ya gafarta maka abinda ya wuce da wanda zai zo daga
laifuka. Sai
Annabi (SAW) ya yi fushi har aka san ya yi fushi ga
fuskarsa. Sa’annan ya ce, Nine mafificinku ga biyayya wa Allah kuma nine
mafificin saninku ga Allah, (watau: Ni ne na fi ku tsoron Allah, kuma na san
Allah fiye da ku).
BABI NA GOMA SHA HUDU: - Yana daga cikin imani,
(mutum) ya yi kyamar (kin) ya koma cikin kafirci, kamar yadda ya ke kyamar
(kin) a jefa shi cikin wuta.
20. An karbo daga Sulaiman dan Harb, ya ce Shu’uba ya
ba mu labari dsaga katadatah daga Anas (RA), yardar Allah ta tabbata gare shi,
daga Annabi (S.A.W) ya ce: Abubuwa uku wanda suka kasance gare shi, ya sami
dandanin imani. Wanda Allah da ManzonSa suka kasance su ne abin kauna, a gare shi
fiye da komai (A) Wanda ya kaunaci bawa (wani mutum) bai kaunace shi ba, sai
don Allah (B) Wanda ya yi kyamar (kin) komawa cikin kafirci, bayan Allah Ya
kubutar da shi, kamar yadda yake kyamar (kin) a jefa
shi cikin wuta.
BABI NA GOMA SHA BIYAR: - Fifikon masu imani zai
kasance gwargwadon kyawon ayyukansu ne. (Mumini yakan fi wani mumini ta
aikinsa).
21. An karbo daga Isma’il ya ce, ‚Malik ya ba ni
labari daga Amru dan Yahaya al-Marizini, daga Ubansa, ya karbo daga Abi Sa’id al-Khudri
(RA), yardar Allah ta tabbata a gare sh. Daga Annabi (S.A.W) ya ce: Mutanen
Aljanna zasu shiga Aljanna kuma mutanen wuta zasu shiga wuta. Sa’annan Allah
Madaukaki Yana cewa, Ku fitar da wanda ya kasance a cikin zuciyarsa akwai
gwargwadon kwayar komayya na imani. Sai a fitar da su, amma wannan lokaci har
sun yi bakin kirin (wuluk). Sa’annan a sanya su a cikin koramar rayuwa ko kuma
rayuwar, bisa ga kokwanton mai ruwaya, shi ne Malik (watau: mai ruwaya na
shakka, wanne ne ba wanne ne ba.) Sai su tofu (tsira) kamar yadda ciyawa
(yabanya) ke tofuwa a gefen jigawa. To, ba ka gani ba lallai ita (Jigawa) tana fidda
fatsifatsi, wanda ya yi yaushi ya koma yabanya (mai toho.) Sai Wuhaibu ya ce, Amru
ya ba mu labari ga fassarar rayuwa, ya ce, rayuwar nan, ma’anan kwayar komayya
ce, na wani aikin kwarai.
22. An karbo daga Muhammad dan Ubaidillah ya ce,
Ibrahim dan Sa’ad ya ba mu labari daga Salihu daga dan Shihab, ya karbo daga
Abu Umama dan Sahal, cewa shi ya ji daga Abu Sa’id al-Khudri (RA) yana cewa:
Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Wata rana ina barci, sai na ga mutane (acikin
mafarki) ana gitta (nuna mini) su gare ni, suna sanye da wasu riguna (taguwa)
akwai wadda tasa
(taguwar) ta kai kusa da nononsa (kirjinsa). Kuma
akwai wanda tasa taguwar kasa da haka take (ba ta kai kirji ba), sai aka gitta (nuna)
Umar dan Khattab (RA) gare ni yana sanye da tasa taguwar yana janta har kasa.
Sahabbai suka ce, ‚Yaya ka dauki (fassara) wannan mafarkin ya Manzon Allah? Sai
ya ce, Na dauke (fassara) shi Addini ne.
BABI NA GOMA SHA SHIDA: - Kunya na daga cikin imani.
23. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce, Malik dan
Anas ya ba mu labari daga dan Shihab daga Salim dan Abdullahi ya karbo daga
Ubansa. Manzon Allah (S.A. W) ya wuce wani mutum daga cikin mutanen Madina.Yana
yi wa dan’uwansa wa’azi game da kunya. Sai Annabi (S.A.W) ya ce: Barshi, lallai
kunya yana daga cikin imani. (watau: ka kyale shi, idan bai yarda da na ka
wa’azin ba to lallai kunya na daga cikin imani).
BABI NA GOMA SHA BAKWAI: - Tsayar da ginshikan
Musulunci, shi ne zama lafiyar al’umma. Allah Madaukaki Ya ce: In suka koma
(tuba) ga Allah, suka tsayar da Sallah, suka ba da zakkar dukiyarsu, to ku fita
hanyarsu (ku ba su ‘yancinsu) (9:5).
24. An karbo daga Abdullahi dan Muhammad al-Musnadi
ya ce, Abu Rauhil al-Harami dan Umara ya ce, Shu’uba ya ba mu labari daga Wakil
dan Muhammad ya ce, ya ji Ubansa yana ba da labari daga dan Umar (RA), Lallai
Manzon Allah (S.A.W) ya ce: An umurce ni da na yaki mutane har su tabbatar da
babu abin bauta wa da gaskiya sai Allah, kuma lallai Muhammad, Manzon Allah
ne. Sa’annan su tsayar da Sallah, su ba da Zakka. To,
in suka aikata haka, jininsu ya tsaru gare ni, da dukiyarsu sai da wani hakkin Musulunci,
sakamakonsu yana ga Allah.
BABI NA GOMA SHA TAKWAS: - Yin aiki shi ne imani.
Allah Madaukaki Ya ce: Waccan Aljanna ita ce wadda aka gadar muku da ita, domin
abinda kuka kasance kuna aikatawa‛ (43:72) Mafi yawan masana sun ce a wajen
fassarar wannan aya, Ina rantsuwa da Ubangijinka, lallai zan tambaye su baki daya
daga abin da suka kasance suna aikatawa’’ (15:92). Watau: game da kalamar: Babu
abin bauta wa da gaskiya sai Allah. Kuma haka suka fassara maganar Allah
Madaukaki cewa, Don irin wannan, masu aiki, suyi ta yin aiki’’ (37:61.).
25. An karbo daga Ahmad dan Yunusa da Musa dan Isma’ila
sun ce, Ibrahim dan Sa’ad ya ba su labari, ya ce, dan Shihabi ya ba su labari daga
Said, dan Musayyib daga Abu Hurairah (RA) cewa: An tambayi Manzon Allah
(S.A.W), Wane aiki ne mafifici (a Musulunci)? Annabi (SAW) ya ce, Imani da
Allah, mutumin yace da kuma me? Annabi (SAW) ya ce, Hajji na kwarai, (Hajji
wanda Allah Ya karba).
BABI NA GOMA SHA TARA: - Mutum ya yi furuci da imani,
ba shi zai sa a kira shi mumini ba. In Musuluncin mutm bai kasance a kan
gaskiya ba. To, mika wuyansa ya kasance a kan tsoron kisa ne. Bisa fadar Allah
(SWT) cewa: kauyawa sun ce, Mun yi imani. Ka fada musu, Ba ku yi imani ba, sai
dai ku ce mun mika wuya’’ (49:14) Idan Musuluncin mutum ya kasance a kan
gaskiya yana daidai da maganar Allah (Wanda ambatonSa Ya daukaka) cewa: Lallai
addini a wurin Allah, shi ne Musulunci’’ (3:19).
26. An karbo daga Abu Yamani, ya ce, Shu’aibu ya ba
mu labari daga Zuhuri, ya ce Amiru dan Sa’ad dan Abi Wakkas ya ba shi labari
daga Sa’ad (RA) yardar Allah ta tabbata gare shi, cewa: Manzon Allah (S.A.W) ya
taba ba wadansu jama’a kyauta a lokacin nan Sa’ad (RA) yana zaune. Sai Annabi
(SAW) ya bar daya daga cikinsu bai ba shi kyautar ba, Sa’ad ya ce, Shi ya fi ba
ni sha’awa daga cikinsu (Mutanen). Sai na ce, Ya Manzon Allah! Me kake gani ga
wane (da ba ka ba shi kyauta ba?), Wallahi ni ina zatonsa Mumini ne Annabi
(SAW) yace: Ko dai Musulmi. Sai na yi shiru na dan lokaci. Sa’annan abin da na
sani game da mutumin nan ya rinjaye ni na maimaita maganata na ce: Me kake gani
ga wane? Wallahi, ni ina zatonsa Mumini ne. Sai (SAW) yace: Ko dai Musulmi. Sa’annan
abin da na sani game da shi ya rinjaye ni, na maimaita maganata. Annabi ya sake
fa]in maganarsa, sa’annan ya ce, Ya Sa’ad! Wallahi ni ina ba mutum (kyauta)
alhali waninsa shi ne abin kauna a gare ni (kuma shi ne mafi alheri a gare
shi), domin tsoron kada Allah Ya kifa shi a cikin wuta (wanda aka baiwa ya
kyauta, don rashin hakuri). Yunus da Salih da Ma’amar dan’uwan Zuhuri, su suka
karbo wannan magana daga Zuhuri.
BABI NA ASHIRIN: - Yawan sallama yana daga cikin
Musulunci. Ammar (RA) ya ce: Abubuwa gudu uku, wanda ya tara su, to, lallai ya
tara imani tare da shi. Ka yi wa kanka adalci. Yawaita sallama ga halittu
(wanda ka sani da wanda baka sani ba). Da ciyarwa ba tare da talauta kai ba
(babu kwauro).
27. An kabo daga kutaibah, ya ce, Laithu ya ba mu
labri daga Yazid dan Abi Habibi daga Abul Khair daga Abdullahi dan Amrin, (RA)
cewa: Wani mutum ya tambayi Annabi (S.A.W) ‚ Wane (aikin) Musulunci ne ya fi
alheri? Annabi ya ce, Ka ciyar da abinci, kayi sallama ga wanda ka sani da
wanda ba ka sani ba.’’
BABI NA ASHIRIN DA DAYA: - Butulcewar abokan zama,
kuma wani kafirci (butulci) yana gaba da wani. An karbo daga Abu Sa’id
al-Khudri daga Annabi (S.A.W).
28. An karbo daga Abdullahi an Maslama, daga Malik,
daga Zaid dan Aslama, daga Ada’i dan Yassar daga dan Abbas (RA) ya ce, Manzon
Allah (S.A.W) ya ce, An nuna mini wuta a cikin mafarki. Sai ga shi mafi yawan
mutanen da ke cikinta mata ne, suna butulcewa. Sai aka ce Shin suna butulce wa
Allah ne? Ya ce: suna butulce wa abokan zama (mazajensu). Kuma suna butulce wa kyautatawa.
Da za ka kyautaata wa dayarsu tsawon zamani, sa’annan ta ga wani abu a gare ka
(na kasawa) Sai ta ce Dadai, ba ta tabaganin wani alheri a gare ka ba.
BABI NA ASHIRIN DA BIYU: - Sabo, aikin jahilci ne. Ba
a kafirta mai yinsa, sai in ya hada Allah da wani. Bisa fadar Annabi (S.A.W),
‚Kai mutum ne, har yanzu akwai halayen jahilci tare da kai (aikin jahiliyya).
Da fadar Allah Madaukaki Lallai Allah ba Ya gafarta wa wanda ya hada Shi da
wani wajen bauta, sai dai Yana gafarta abin da bai kai haka ba ga wanda Ya so’’
(4:48).
29. An karbo daga Sulaiman dan Harb, ya ce, Shu’uba
ya ba mu labari daga Wasil al-Ahdabi daga Ma’aru, ya ce, Na hadu da Aba Dharrin
(RA) a wani gari da ake kira Rabzah (a kasar Iraki) shi da yaronsa suna sanye
da tufafi masu kyau (iri daya), Sai na tambaye shi akan wannan, sai ya ce, Miyagun
maganganu sun gudana tsakani na da wani mutum, sai na yi wa uwarsa gori. Sai Annabi
(S.A.W) ya ce mini, ‚Kai mutum ne har yanzu akwai halayen jahilci tare da kai
(aikin jahiliyya). Allah Ya sanya ‘yan’uwanku abin mallaka a gare ku (bayi)
kuma suna karkashin ikonku. Wanda duk dan’uwansa ya kasance karkarshin ikonsa,
ya ciyar da shi daga abincinsa. Ya tufatar da shi irin tufafinsa. Kuma kada ku
sanya su aiki wanda ya fi karfinsu. Idan har kuka sanya su irin haka, to,
lallai ku taimaka musu.
BABI NA ASHIRIN DA UKU: - Fada a tsakanin Mumimi da
Mumini bai sanya a kafirta su, saboda fadar Allah Madaukaki cewa: In kungiya
biyu ta Muminai suka yaki juna, ku (sulhunta) gyara tsakaninsu’’ (49:9). Allah
Madaukaki Ya ambace su Muminai.
30. An karbo daga Abdurrahman dan Mubarak ya ce,
Hammad dan Zaid ya ba mu labari ya ce, Ayyuba da Yunus sun ba mu labara daga
Hassan daga Ahnafu dan kais ya ce, Na tafi don in taimaki wannan mutum, sai Abu
Bakarata (RA) ya gamu da ni, ya ce, Ina za ka? Na ce, Zan taimaki wannan mutum
(Aliyu dan Abi dalib), Abu Bakarata (RA) ya ce, Koma! Lallai ni, na ji Manzon
Allah (S.A.W) yana cewa, Idan Musulmai biyu suka hadu da takubbansu (suna fada).
To, wanda ya yi kisa da wanda aka kashe sunacikin wuta. Sai na ce, Ya Manzon
Allah! Wannan shi ya yi kisa, to mene ne laifin wanda aka kashe? Sai Annabi
(S.A.W) ya ce, Ai shi ma ya kasance mai kwadayi ne akan ya kashe dan’uwansa.’’
BABI NA ASHIRIN DA HUDU: - Wani zalunci yana gaba da
wani (wani bai kai wani ba).
31. An karbo daga Abu Walid ya ce, Shu’uba ya ba mu
labari, Hawwala as-Sanad, (wato Isna’di ya canza). Yace kuma Bishir ya bani
labarin Hadisin da ya karbo daga Muhammad, daga Shu’uba, daga Sulaiman, daga
Ibrahim daga Alkama daga Abdullahi (RA) ya ce, Lokacin da wannan aya ta sauka,
da cewa: Kuma wadanda suka yi imani ba su hada (gauraya) imaninsu da zalunci ba
(ba su
yi shirka ba). (6:83) Sahabban Manzon Allah (SAW)
suka ce, Wane ne a cikinmu bai taba zalunci ba? Sai Allah Ya saukar da wannan
aya, Lallai hada bautar Allah da wani zalunci ne mai girma (31:13).
BABI NA ASHIRIN DA BIYAR: - Alamar Munafiki.
32. An karbo daga Sulaiman Uban Rabi’a ya ce, Isma’ila
dan Ja’afar ya ba mu labari, ya karbo daga Nafi’u dan Malik dan Abi Amir Uban
Suhaila daga Ubansa daga Abu Huraira (RA) daga Annabi
(S.A.W) ya ce: Alamar munafiki uku ce: Idan ya yi Magana ya yi karya, Idan ya
yi alkawari sai ya saba, Idan aka ba shi amana sai ya yi ha’inci (yaudara).
33. An karbo daga kabisat dan Ukbata ya ce, Safiyanu
dan A’amash ya ba mu labari, daga Abdullahi dan Murra daga Masruk, daga Abdullahi
dan Amri (RA) Annabi (S.A.W) ya ce: Wanda abubuwa hudu suka kasance gare shi,
ya kasance tsantsan munafiki, Wanda dabi’a daya daga cikinsu ta kasance gare
shi, dabi’ar munafinci ta tabbata gare shi, sai ya bar ta. Na farko: In aka ba
shi amana, ya yi yaudara. In ya yi magana ya yi karya. In aka yi alkawari da
shi, ya saba. In ya yi husuma (fada) ya yi tsaurin kai (afajirc). To, Shu’uba
ya karbo irin wannan daga A’amash. (alamar munafinci na hudu shine: idan mutum
ya yi fada da wani kosulhunta su, sai ya rika fadar bakar magana ga abokin fadarsa
don ka da su shirya).
BABI NA ASHIRIN DA SHIDA: - Sallar dare don neman
Lailatul kadari, yana daga cikin imani.
34. An karbo daga Abu Yamanin ya ce, Shu’aibu ya ba
mu labari ya ce, Abu Zinadi ya ba mu labari daga al-A’araj, daga Abu Huraira
(RA) ya ce, Annabi (S.A.W) ya ce: Wanda ya tsaya (da sallar dare) a cikin dare
mai daraja, yana mai imani tare da neman sakamakon Allah, an gafarta masa abin
da ya gabata na laifinsa.
BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI: - Yaki don daukaka kalmar
Allah (Jihadi) yana daga cikin Imani.
35. An karbo daga Haramiyyu dan Habsu, ya ce
Abdulwahid ya ba mu labari, ya karbo daga Umarah Ya ce Abu Zur’a dan Amru dan
Jarir ya ba mu labari ya ce, ya ji Abu Huraira (RA) daga Manzon Allah (S.A.W)
ya ce: Allah Ya karba wa duk wanda ya fita zuwa ga yakin daukaka kalmar Allah,
kuma bai fita ba face don ba da gaskiya gare Ni (Allah), da kuma gaskanta manzanni
Na, to, wannan ya karbi kiran Allah, ko dai Allah Ya dawo da shi tare da abin
da ya samu na lada, ko ganimar yaki, ko kuma in shigar da shi Aljanna Ta.
(Annabi ya ce): Ba domin kada in tsananta (matsa) wa al’ummata ba, da ban zauna
a bayan wani Sariyya ba, (yakin da shi (SAW) bai halarta ba), Sai in ta zuwa
jihadi, ina gurin in yi mutuwar shahada saboda Allah. Sannan a raya ni, Sannan
in sake zuwa jihadi (yaki) in yi mutuwar shahada, Sannan a sake raya ni, kuma
in sake mutuwar shahada sabo da Allah.
BABI NA ASHIRIN DA TAKWAS: - Sallar Asham (Tarawihi)
a cikin watan Azumin Ramadan yana daga cikin imani.
36. An karbo daga Isma’il ya ce, Maliki ya ba ni
labari daga dan Shihab, daga Humaidi dan Abdurrahman, daga Abu Hurairah (RA)
lallai Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Wanda ya tsaya a cikin daren watan Azumi (ya
yi Sallar Asham) yana mai ba da gaskiya. Yana mai neman sakamako, an gafarta masa abin da ya gabata
na laifukkansa.
BABI NA ISHIRI DA TARA: - Azumin watan Ramadan don
neman sakamako yana daga cikin imani.
37. An karbo daga dan Salam ya ce, Muhammad dan
Fudail ya ba mu labari, labari daga Abu Salmata, daga Abu Huraira ya ce, Manzon
Allah (S.A.W) ya ce: Wanda ya yi azumin watan Ramadan yana mai imani, kuma yana
neman sakamako, an gafarta masa abin da ya gabata na laifukansa.
BABI NA TALATIN: - Addini sauki gare shi. Bisa fadar
Annabi (S.A.W): Addinin da Allah Ya fi so, shi ne mai sauki mai rangwami.
38. An karbo daga Abdussalami dan Mudahhar ya ce,
Umar dan Aliyu ya ba mu labari, daga Ma’anin dan Muhammadu al-Ghifari, daga
Sa’idu dan Abi Sa’id al-Makbari, daga Abu Huraira (RA) daga Annabi (S.A.W) ya
ce: Lallai Addini sauki ne. Duk wanda ya tsananta (wuce iyaka) acikin Addini
sai ya rinjaye shi. To, ku rika daidaita (al’amura), ku tsakaita, ku fadi kalma
mai dadi. Ku nemi taimakon Allah safiya da maraice kuma da wani abu na lokacin
(yanki) dare.
BABI NA TALATIN DA DAYA: - Sallah tana daga cikin
imani. Bisa fadar Allah Madaukaki, Allah bai kasance Yana tozartar da imaninku
ba’’ (2:143) mai karbo labarin ya ce, Watau: Sallarku ta jihar daki (kudus).
39. An karbo daga Amru dan Khalid ya ce, Zuhair ya ba
mu labari, daga Abu Is’hak daga Bara’u (RA) cewa: Manzon Allah (S.A.W) ya
kasance farkon isowarsa Madina ya sauka a gidan kakanninsa. Mai karbo hadisi ya
yi kokwanto ya ce, Ko dangin uwarsa mutanen Madina kuma (SAW) ya rika yin
Sallah yana mai fuskantar Arewa (Jerusalem) watanni goma sha shida. Ko watanni
goma sha bakwai. Ya kasance yana son daki (ka’aba) ya zama wurin fuskantarsa ga
sallah. Kuma lallai shi ya yi Sallah, farkon Sallar da ya yi (ta wajen Ka’aba),
ita ce Sallar La’asar ya yi ta tare da wadansu mutane. Sai wani mutum ya fita
bayan kare Sallah, ya tafi zuwa wani Masallaci ya iske mutanen wannan Masallaci
suna ciki ruku’u (suna fuskantar Baitil Makdisi). Sai ya ce, Na rantse da
Allah, na yi Sallah tare da Annabi yana mai fuskantar Makka (Ka’aba). Sai
(mutanen) suka juya wajen dakin (Ka’aba) a kamar yadda suke. Kuma Yahudawa sun
kasance abin ya ba su sha’awa a lokacin da Annabi yake fuskantar {udus (Baitil
Makdisi), haka ma Nasara (Kiristoci). Lokacin da Annabi (SAW) ya juya ya
fuskanci Makka (Ka’aba), sai suka musanta (kyamaci) haka. Sai Zuhair ya ce, Abu
Is’hak ya ba mu labari daga Bara’u a cikin wannan hadisin, Lallai mutane da yawa
sun mutu gabanin a juya alkibla, kuma an kasha wasu, ba mu san abin da za mu ce
game da su ba." Sai Allah Ya saukar da wannan aya cewa: Allah bai kasance
Yana tozarta imaninku ba.
BABI NA TALATIN DA BIYU: - Kyawun Musuluncin mutum
tsayar da Sallah. Imam Al-Bukhari (RA) ya tsallake mutum daya anan sai ya ce: Malik
(RA) ya ce, Zaidu dan Aslam ya ba ni labari, cewa Ada’a dan Yasar ya ba shi
labari, lallai Aba Sa’id al-Khudri (RA) ya ba shi labari, cewa: Ya ji Manzon
Allah (S.A.W) yana cewa: In bawa ya musulunta kuma musuluncin sa ya yi kyau,
Allah Yana kankare masa dukkan laifi da ya kasance ya aikata. Kuma ya kasance
bayan haka, akwai sakamako zuwa ribanyawa (ninkawa), kyakkyawan aiki daya, ana
saka masa da irinsa goma, har yakai dari bakwai zuwa ribin haka. Mummunan aiki
daya kuwa, da shi ake saka masa, sai fa in Allah Ya gafarta masa wannan
mummunan aikin.
40. An karbo daga Is’haka dan Mansur ya ce,
Abdurrazak ya ba mu labari ya ce, Ma’amar ya ba mu labari daga Hamman. Daga Abu
Huraira (RA) ya ce, Manzon Allah (S.A.W) ya ce, In Musuluncin dayanku ya yi
kyau, duk kyawawan aikin da ya aikita ana rubuta masa lada goma misalinsa, har
zuwa dari bakwai da ninki, duk mummunan aikin da ya aikata, ana rubuta masa
irinsa daya.
BABI NA TALATIN DA UKU: - Aikin Addinin da Allah Yafi
so, shi ne wanda babu fashi.
41. An karbo daga Muhammad dan Muthanna ya ce, Yahaya
ya ba mu labari daga Hisham ya ce, Ubana ya ba ni labari daga A’ishatu (RA)
cewa: Manzon Allah (S.A.W) ya shiga gare ta, a lokacin wata mata na tare da
ita, sai Annabi ya ce, Wace ce wannan? Sai ta ce, Wance ce wadda kake maganar
Sallar ta (sabo da yawan Sallar ta), sai Annabi ya ce, Yi shiru! Ina horonku (umurtanku)
da aikata abin da kuke iyawa. Na rantse da Allah, Allah ba Zai kosa ba, sai
idan kun kosa da kanku. Kuma Addinin da Allah Ya fi so, shi ne wanda mai yinsa
ba ya fashi.
BABI NA TALATIN DA HUDU: - karuwar imani da
raguwarsa. Allah Madaukaki Ya ce: Don Mu kara musu wata shiriya’’ (18:13). Don
waDanda suka yi imani su kara imani‛ (74:31). Allah Ya ce: (a wata ayar,) Yau
Na kammala muku Addininku (5:3) In Musulmi ya bar wani abu daga kammalarsa, to
ya kasance ragagge (tauyayye).
42. An karbo daga Muslim dan Ibrahim ya ce, Hishamu
ya ba mu labari ya ce, katadata ya ba mu labari daga Anas (RA) daga Annabi
(S.A.W) ya ce: Wanda ya fadi ‘Lailaha illallahu (Babu abin bautawa da gaskiya
sai Allah) zai fita daga wuta, in akwai gwargwadon nauyin kwayar sha’ir (hatsin
mai kama da shinkafa) na alheri a cikin zuciyarsa. Wanda ya fadi ‘La’ilaha
illallahu’ zai fita daga wuta, idan akwai gwargwadon nauyin kwayar alkama na
alheri a cikin zuciyarsa. Kuma wanda ya fadi La’ilaha illallahu zai fita daga
wuta, in akwai gwargwadon nauyin kwayar zarra na alheri a cikin zuciyarsa. Sai
Abu Abdullahi (Bukhari) ya ce, Abanu ya ce, katada ya ba mu labari daga Anas
daga Annabi (S.A.W) ya ce: imani maimakon alheri. Ma’anar cewa: duk wanda ya
kasance akwai imani cikin zuciyarsa gwargwadon zarra, ba cewa: alheri ba.
43. An karbo daga Hassan dan Sabbah, ya ji daga
Ja’afar dan Aunu ya ce, Abu Umaisi ya ba mu labari daga kaisu dan Muslim, daga
darik dan Shihab, daga Umar dan Khattab (RA) cewa: Wani mutum daga cikin
Yahudawa ya ce masa, ‚Ya Sarkin Muminai! Akwai wata aya a cikin Littafinku kuna
karanta ta. Da agare mu ne ta sauka mu taron (dandazon) Yahudawa, da mun riki
wannan yini ranar Idi. Sai Umar (RA) ya ce masa, Wace aya ce? Sai wannan mutum ya ce: Yau Na kammala muku
addini kuma Na cika muku ni’imaTa gare ku, kuma Na yarda Musulunci shi ne
Addini a gare ku. (5:3) sai Umar (RA) ya ce, Lallai mun san wannan rana, da wurin
da ta sauka ga Annabi (S.A.W), a lokacin yana tsaye a Arfa, ranar Juma’a.
BABI NA TALATIN DA BIYAR: - Tsarkake dukiya (fidda
Zakka) na daga cikin imani. Da maganar Allah Madaukaki cewa: Ba a umurce su da
komai ba face don su bauta wa Allah, suna masu tsarkake Addini a gare Shi. Suna
masu mika wuya gare Shi. Suna masu tsayar da Sallah, suna fitar da Zakka,
wannan, shi ne Addini madaidaici (98-5).
44. An karob daga Isma’ila ya ce, Malik dan Anas (RA)
ya bani labari daga Baffansa Abi Suhailin dan Malik, daga Ubansa ya ji Dalha
dan Ubaidillah (RA) yana cewa, Wani mutum daga cikin mutanen Najad mai bitaccen
kai (mai kura, wanda bai tsefe gashin ba). Ana jin babbar muryarsa kamar kukan
kudan zuma kuma ba a fahimtar abin da yake cewa, ya zo ga Annabi (S.A.W), har
ya kusance shi, sai ga shi yana tambaya ne game da Musulunci. Sai Annabi
(S.A.W) ya ce Salloli biyar a dare da rana. Sai mutumin ya ce, Shin akwai wani
abu a kaina bayan wadannan? Annabi ya cigaba da cewa: Azumin Ramadan. Sai
mutumin ya ce, Shin akwai wani abu a kaina bayan wannan? Annabi ya ce: Sai in
ka so ka yi nafila. Sa’annan Annabi ya fada masa bayar da Zakka. Ya ce, Shin
akwai wani abu a kaina ban da shi? Annabi ya ce: A’a sai in kaso ka yi nafila!
Sa’annan mutumin ya juya ya tafi yana mai cewa, Wallahi! Ba zan kara ba, ba
kuma zan rage ba. Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Ya sami babban rabo in ya yi
gaskiya.
BABI NA TALATIN DA SHIDA: - Rakiyar gawa zuwa kabari,
yana daga cikin imani.
45. An karbo daga Ahmad dan Abdullahi dan Ali
al-Manjufi, ya ce Rauhu ya ba mu labari daga Aufu, daga Hassan da Muhammad,
daga Abu Huraira (RA) cewa: Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Wanda ya yi wa gawar
Musulmi rakiya yana mai ban gaskiya, yana mai neman sakamako. Kuma ya kasance
da ita har aka yi mata Sallah, kuma aka rufe ta. To, lallai ya dawo da yanki biyu
na lada. Kowane yanki, ya kai misalin dutsen Uhudu (dutsen kusa da Madina). Wanda
ya yi mata Sallah sa’annan ya dawo kafin a rufe ta. To, ya dawo da yankin lada
daya. Uthmanu mai kiran Sallah, yana tare da mai bayar da wannan labari ya ce, Aufu
ya ba mu labari, daga Muhammad, daga Abu Huraira (RA) daga Annabi (S.A.W),
kamar haka.
BABI NA TALATIN DA BAKWAI: - Munafunci na bata aikin
kwarai. Tsoron Mumini domin kada aikinsa ya baci alhali bai sani ba. Da maganar
Ibrahim at-Taimiyyu, Ba na gwada magana ta da aiki na face ina tsoron kada in
zama makaryaci. dan Abi Mulaikata ya ce, Na riske mutane talatin daga cikin
Sahabban Annabi (S.A.W), kowanensu yana tsoron munafinci a kansa. Babu daya
daga cikinsu da ya taba cewa: Imaninsa ya kai karfin imanin Mala’ika Jibrilu da
Mika’ilu. Amma Hasan al-Basari ya ce, Mumini na gaskiya ne kadai ke tsoron
munafinci, kuma munafiki ne kawai ke ganin ya kubuta daga gare shi. Sa’annan da
abin da ake tsoro na dogewa akan munafinci da sabo ba tare da tuba ba, domin Allah
Madaukaki Ya ce, Kuma ba su doge ba akan abin da suka aikata, alhali kuma sun
sani (3:135).
46. An karbo daga Muhammad dan Ar’arata ya ce, Shu’uba
ya ba mu labari, daga Zubaid ya ce, na tambayi Uban Wa’il dangane da hukuncin
Murji’a (kungiyar da ta dakatar da Sayyidina Aliyu daga saurar Sahabbai). Sai
ya ce, Abdullahi (RA) ya ba ni labari cewa: Manzon Allah (S.A.W) ya ce, Zagin
Musulmi fasikanci ne, yakarsa kuma, kafirci ne. Utaibatu dan Sa’idu ya ba mu
labari daga Ism’ila dan Ja’afar, daga Humaidi, daga Anas ya ce, Ubadata dan
Samiti ya ba ni labari, cewa: Manzon Allah (S.A.W) ya fita yana mai son ba da
labari a gamed Lailatul kadar (dare mai daraja). Sai wadansu mutane biyu
(Musulmai) suka rika daga muryarsu suna zagin junansu (cikin husuma). Sai
Annabi (S.A.W) ya ce: Lallai na fito ne don in ba ku labarin game da Lailatul kadari
(dare mai daraja), amma da wane da wane sun zagi junansu, wannan ya sanya an dauke
(an mantar da ni) shi (daren). Muna tsammanin ya zama alheri gare ku, ku neme
shi a cikin kwana bakwai na karshen wata ko tara ko biyar.
BABI NA TALATIN DA TAKWAS: - Tambayar (Mala’ika)
Jibrilu ga Manzon Allah (S.A.W) game da sanin sa’ar al-kiyama, ya kebanta ga
Allah. Da jawabi akan imani da Musulunci da Ihsani, suna a cikin addini. Da
bayanin Annabi (S.A.W) ga Jibrilu. Sa’annan Annabi (S.A.W) ya ce: Wannan
Jibrilu ne ya zo don ya sanar da ku Addinnku‛ Annabi ya sa, imani da ihsani da
sanin sa’a (watau
ranar tashin al-kiyama), dukansu Addini ne, Kuma da
abinda Annabi (S.A.W) ya bayyana ga tawagar Abdu kais (wata kabila a Bahrain)
duk suna acikin imani. Kuma da fadar Allah Madaukaki Wanda ya nemi wani abu
wanda ba Musulunci ba ne, ya zama Addini gare shi, ba za a karbar masa ba
(3:85).
47. An karbo daga Musaddad ya ce, Isma’ila dan
Ibrahim ya ba mu labari daga Abu Hayyan at-Taimiyyu, daga Abu Zur’a daga Abi
Hurairah (RA) ya ce, Annabi (S.A.W) ya kasance ya fito wata rana ga mutane, sai
Jibrilu ya zo masa ya ce ‚Mene ne imani? Sai Annabi (S.A.W) ya ce, ‚Imani shi
ne ka yi imani da Allah da ManzaninSa, kuma ka yi imani da tashin al-kiyama.
Sai Jibrilu ya ce‚ Mene ne Musulunci? Sai Annabi (S.A.W) ya ce, Musulunci, shi ne
ka bauta wa Allah kada ka hada Shi da waninSa. Ka tsayar da Sallah, ka bayar da
Zakka wanda aka wajabta gare ka. Ka yi Azumin watan Ramadan. Sai Jibrilu ya ce,
Mene ne kyautatawa (ihsan)? Annabi ya ce, Ka bauta wa Allah kamar kana ganin
Sa, in ka kasance ba ka ganinSa, lallai Shi Yana ganinka. Jibrilu ya ce, Yaushe
ne tashin al-kiyama (sa’a)? Annabi (S.A.W) ya ce, ‚Wanda aka wa tambayar game
da sa’a bai fi mai tambayar sani ba, zan ba ka labarin alamominta: (1) In baiwa
ta haifi uwargijiyarta (Shugabanta). (2) Makiyayan rakuma da tumakai suna yin
gasa wajen gina dogayen gidaje. (3) Cikin abubuwa biyar, babu wanda ya sansu
sai Allah. Sa’annan Annabi (S.A.W) ya karanta wannan aya, Lallai sanin ranar
tashin al-kiyama, ga Allah yake (31:44), Sa’annan Jibrilu ya tafi. Sai Annabi
(S.A.W) ya ce: Ku kirawo shi Ba su ga kowa ba. Sai Annabi (S.A.W) ya ce: Wannan
Jibrilu ne ya zo don ya sanar da mutane Addininsu. Sai Uban Abdullahi (Bukhari)
ya ce, Annabi (S.A.W) ya sanya wadannan abubuwa dukansu suna daga cikin imani.
BABI NA TALATIN DA TARA: - karfin imanin wanda ya mika
wuya.
48. An karbo daga Ibrahim dan Hamzata ya ce, Ibrahim
dan Sa’ad ya ba mu labari daga Salih, daga dan Shihab daga Ubaidullahi an
Abdullahi, cewa: Abdullahi dan Abbas, yardar Allah ta tabbata gare shi, ya ba
shi labari ya ce, Abu Safiyanu ya ba ni labari, cewa: Hirakla Sarkin Rumawa, ya
ce masa Na tambaye ka, shin suna karuwa ne ko suna raguwa? Ka ce ‚Suna karuwa
ne. To, haka imani yake, sai ya cika. Na tambaye ka Shin wani yana fita don
fushi daga cikin Addininsa bayan ya shiga, ka ce, A’a, to haka imani yake
lokacin da ya cudanya da jinin zuciya. Wani ba ya iya fusatar da mai shi.
BABI NA ARBA’IN: - Wanda ya kubutar da Addininsa, ya
tsira.
49. An karbo daga Abu Nu’aim ya ce, Zakariya’u ya ba
mu labari daga Amir ya ce, ya ji Nu’umanu dan Bashir (RA) yana cewa: Na ji Manzon
Allah (S.A.W) yana cewa, Halal bayyane take, kuma Haram ma a bayyane yake.
Tsakaninsu akwai rikitarwa (kama da juna) wanda mafi yawan mutane ba su sansu
ba. Wanda ya tsira (nesanci) abubuwa masu kama da juna (masu cikici) to hakika
ya tsira da Addininsa da mutuncinsa. Amma duk wanda ya fada cikin rikitarwar
(abubuwa masu kama da juna), haka yake kamar mai kiwo a gefen hurumi (iyaka) ya
yi kusa ya fada cikinsa. Ku saurara! Lallai kowane Sarki yana da hurumi. Ku
saurara! Lallai hurumin Allah a cikin kasarSa, shi ne abin da Ya haramta. Ku
saurarra! Lallai akwai wata tsoka a cikin jiki in ta yi kyau, jiki ya yi kyau dukkansa,
in har ta baci, jiki ya baci dukkansa. Ku saurara! (Wannan tsoka) ita ce
zuciya.
BABI NA ARBA’IN DA BIYU: - Bayar da daya daga cikin
biyar na ganimar yaki, (ko ajiyar jahiliyya ga wanda ya hako shi daga kasa),
yana daga cikin imani.
50. An karbo daga Aliyu dan Ja’ad, ya ce, Shu’uba ya
ba mu labari daga Abi Jamrata ya ce, Na kasance ina zaune tare da dan Abbas
(RA) kuma ya kasnace yana zaunar da ni kan gadonsa, sai dan Abbas (RA) ya ce, Ka
zauna tare da ni har in sanya maka rabo daga dukiyata! Na zauna tare da shi
wata biyu, sa’annan ya ce, Lallai tawagar Abdul kais lokacin da suka je wurin
Annabi (S.A.W) ya ce, Wasu mutane ne ko kuma Wace tawaga ce? Sai suka ce,
Mutanen Rabi’a ce. Annabi (SAW) ya ce, Maraba da mutane ko Maraba da tawaga, ba
masu bakin cika ba kuma ba masu da-na-sani ba (nadama), Sai suka ce, Ya Manzon
Allah! Mu ba mu da ikon cira ta zuwa gare ka face a cikin watan Muharram (watan
cika ciki). Tsakaninmu da kai, akwai wannan kabila ta kafiran Mudar (mutanen
Makka). To ka umurce mu da al’amari mai rarrabewa. Mu ba na bayanmu labari kuma
mu shiga Aljanna da wannan (al’amarin), Sai suka tambaye shi daga abubuwan sha.
Annabi (S.A.W) ya umurce su da aikata abubuwa hudu. Ya hana su aikata
abubuwa hudu. (1) Ya umurce su da yin imani ga Allah
Shi kadai, ya ce, ‚Ko kun san mene ne yin imani ga Allah Shi kadai? Sai suka
ce, Allah da ManzonSa ne suka fi sani. Annabi (S.A.W) ya ce: Sakankancewar
(imani) babu abin bauta wa da gaskiya sai Allah. Kuma lallai Muhammadu Manzon
Allah ne (S.A.W), da tsayar da Sallah da tsarkake dukiya (fitar da Zakka) da
Azumin watan Ramadan, da Kuma su bayar daya daga cikin biyar na ganima, (ko
dukiyar ajiyar jahiliyya da aka samu daga kasa). (2) Ya hane su aikata abubuwa
hudu: Ya hana su shan tsimin tukunya (mai sa maye) da tsimin masaki (mai sa
maye) da kuma tsimin da aka sa ciki akushi da kuma tsimin cikin gora (mai sa
maye). Ko ya ce dan karamin akushi, sa’annan (SAW) ya ce musu: Ku tsare wadannan
kuba na bayanku labarinsu.
Kalmar
‘muzaffa’ wani abu ne kamar kwalta ko dankon zuma wadda ake rufe koren giya
dasu don su sanya mai shansu maye. Haka ‘mukayyar’ amma nakiru; abinda aka
rarake cikinsa daga itace don zuba giya, Allah Yasa mu dace.
BABI NA ARBA’IN DA UKU: - Ayyuka na tabbata
gwargwadon niyya kuma tare da tsarkakewarsu (neman sakamako a wurin Allah).
Kuma kowane mutum (na da sakamako) game da irin
niyyarsa. Kuma imani da alwala da Sallah da Zakka da Hajji da Azumi da sauran
hukunce-hukunce duk sun shiga cikin wannan. Da maganar Allah Madaukaki, ‚Ka ce
musu, kowa ya yi aiki a kan niyarsa (17:84) Imam Bukhari ya ce: Ya yi aiki bisa
nufinsa. Ciyarwar mutum ga iyalinsa da yake neman lada a kai, wannan sadaka ce.
Annabi (S.A.W) ya ce: Sai jihadi da kuma kyawon niyya. Sauran hadisin shine
fadar Annabi (SAW) cewa: Babu kaura daga garin Makka zuwa Madina bayan cin
Makka da yaki. Amma abin da ya saura shine jihadi da aiki bisa kyawon niyya.
51. An karbo daga Abdullahi dan Maslamata ya ce, Maliku
ya ba mu labari daga Yahaya dan Sa’id, daga Muhammadu dan Ibrahim, daga Alkamata
dan Wakkas, daga Umar (RA) cewa: Lallai Annabi (S.A.W) ya ce: Ayyuka suna
tabbata gwargwadon niyya, kuma kowane mutum yana da sakamako irin niyyarsa.
Wanda kaurarsa ta kasance saboda Allah da ManzonSa (SAW), to, sakamakon kaurarsa
tana ga Allah da ManzonSa (SAW), Wanda kaurarsa ta kasance don duniya ce zai
same ta, ko wata mata wadda zai aureta. To kaurarsa ta kasance a kan abin da ya
yi kaura dominsa.
52. An karbo daga Hajjaju dan Minhal, ya ce, Shu’uba
ya ba mu labari, ya ce Adiyyi dan Sabiti ya ba ni labari ya ce, Naji Abdullahi
dan Yazidu daga Abi Mas’ud, daga Annabi (S.A.W) ya ce, ‚In namiji ya ciyar da
iyalinsa yana mai neman lada. To, wannan sadaka ce a gare shi.
53. An karbo daga Hakam dan Nafi’i ya ce, Shu’aibu ya
ba mu labari daga Zuhuri ya ce, Amiru dan Sa’ad ya ba ni labari daga Sa’ad dan
Abi Wakkas, lallai shi (RA) ya ba shi labari cewa: Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Lallai
kai ba ka ciyar da wani abin ciyarwa ba, matukar kana mai neman yardar Allah
akan ciyarwar, face an ba ka sakamako akai, har abin da kake sanyawa ga bakin
matarka.
BABI NA ARBA’IN DA HUDU: - Babu fifiko tsakanin
Musulmi da Musulmi game da hakkin shari’a. Kuma da fadar Annabi (S.A.W) cewa, Addini
nasiha ne (gyara) don Allah da ManzonSa kuma da shugabannin Musulmai da kuma
dukkan Musulmi. Kuma da fadar Allah Madaukaki: Idan suka yi nasiha don Allah da
ManzonSa (9:91).
54. An karbo daga Musaddad ya ce, Yahaya ya ba mu
labari daga Ism’il ya ce, kaisu dan Abu Hazim ya bani labari daga Jarir dan
Abdullahi ya ce, Na dauki alkawari (mubaya’a) daga Manzon Allah (S.A.W) bisa ga
tsayar da Sallah da tsarkake dukiya (bayar da Zakka) da kuma yin nasiha ga
kowane Musulmi.
55. An karbo daga Uban Nu’uman ya ce, Abu Awanata ya
bamu labari daga Ziyad dan Ilakata ya ce, Na ji Jarir dan Abdullahi (RA) yana
cewa: A ranar da Mughira dan Shu’uba ya rasu (mutu), ya mike tsaye ya gode wa
Allah, ya yi maSa yabon da ya dace da Shi, sa’annan ya ce, Na umurce ku da ku
ji tsoron Allah Shi kadai, ba Shi da abokin tarayya, Da kwantar hankali da
natsuwa, har a kawo muku wani sabon Sarki. Lallai zai zo muku yanzu, Sa’annan
ya ce, Kune mi rangwame (gafara) ga Sarkinku, domin (Allah) Ya kasance mai son
rangwantawa (yafewa) ne.‛ Sa’annan ya ci gaba da cewa, ‚Bayan haka lallai ni,
naje wurin Annabi (S.A.W) na fada masa cewa: Zan dauki alkawari gare ka bisa ga
Musulunci. Sai ya gitta (sanya) sharadi gare ni cewa: Tare da yin nasiha ga
kowane Musulmi, daga nan na dauki alkawari a kan wannan. Ina rantsuwa da Mai
wannan Masallaci (Allah), lallai ni mai nasiha ne a gare ku. Sa’annan ya nemi
gafarar Ubangiji, ya sauka daga kan munbari.
Kuskuren da muka yi, Muna fata Allah
Ya gafarta muna, wanda kuma Muka dace, Muna fata Allah Ya sanya Muna shi cikin
kyawawan aiyukan mu.
Muna kira ga Makarantar
wannan dan karamin aiki, idan sun hararo kusken rubutu, su gaggauta tuntuban mu
ko kuma su gyara mana, sannan kuma su nema mana afwa.
وما توفيقي إلا بالله
No comments:
Post a Comment