Monday, April 26, 2021

Hanyoyi guda goma don magance infection (Sanyi na Mata da Maza)

HANYOYIN 10 MAGANCE INFECTION

 

‘Yan Uwana Mata barkan mu da sake saduwa daku a cikin wannan fili namu mai matukar farin jini, wato Sirrin Gyaran jiki… Kamar yadda kuka sani shi wannan shiri a na yin shi ne don matan aure zalla domin basu shawarwari ta kowane bangare na rayuwarsu ta yadda za su samu su gyara zaman takewarsu da mazajen da mu’amalar su ta bangaren girki, tsafta, gyaran gida da gyaran jiki. Irin abubuwan daya kama mu mata mu dinga ci domin karin ni’imar mu da gamsuwar mazajen mu, da ma duk wani abu daya shafi rayuwar ya mace. Da fatan za ku dinga bibiyata a cikin wannan shiri.gurin da nayi kuskure sai nace Ina neman afuwar ubangiji da afuwar ku domin ajidan ci irin na dan Adamtaka, gurin kuma da nayi dai dai Sai nace Allah ya hada mu a ladan baki daya.


Da farko Lallai ya kamata ku gane cewa infection yanada wuyan magani domin maganine da se andauki lokaci anayi kamin ya warke gaba daya,inda sansamune ku dauki lokaci kaman wata 6 ajere koma fiye shine zakiga kin maganceshi gabadaya amma in zaki fara ki bari to lallai zaki dade kina magani baki maganceshi gabadayaba. kuma lallai wacce take da miji sai sunyi magani su biyu amma intasah magani ita kadai kamar tayi a bandane don suna kara saduwa da mijin ata kara
daukar ciwon_

 

Mu na rokon da Allah ya baku lafiya ingantatta kuma yasa kaffarane.

A gwada daya daga cikin wadannan:

 

1- A samu Saiwar Garafuni da Sassaken Magarya, sai a tafasa, idan ya dan huce sai mace ta dinga kama ruwa da shi. Kullum sau daya. Yana maganin budewa da kaikayi.

 

2- A samu Garafuni da Sassaken Sanya sai a tafasa, mace ta dinga shan rabin kofi da safe, rabi da yamma. Ya na fitar da dattin mara da maganin farin ruwa mai wari.

 

3- A samu Furen Tumfafiya, sai a shanya ya bushe, a daka a dinga zubawa a cikin Nono a na sha. Ya na magance matsalar ruwan infection.

 

4- A samu Lalle da Ganyen Magarya da Kanumfari, a hada waje daya a daka sannan a tafasa a zuba farin miski a ciki. Idan ya dan huce sai ta shiga ciki ta zauna tsawon kamar minti goma. Yin haka yana maganin kaikayi da kuraje da budewa da dadewar gaba.

 

5- A samu Kabewa a dafa ta, bayan an dafa sai a tsame daga ruwa a jajjagata ko a birga, a zuba Madara ko Nono sannan a sa Zuma a sha. Wannan yana mganin rashin sha’awa da bushewa da rashin gamsuwa.

 

6- A dafa Zogale, idan ya dahu sai a murje shi ko a dama, a tace, a yi lemon juice da shi. Yana maganin fitar farin ruwa mai wari da cushewar mara kuma ya na kara ni’ima.

 

7- A samu Dan-Tamburawa da Albabunaj a tafasa a zuba Man Hulba a ciki. Sai ta dan tsuguna tururin ya dinga shigarta. Idan ya dan huce kuma sai ta shiga ciki ta zauna. Zai magance mata kaikayi da kuraje kuma ya na sa matsewa.

 

8- A samu Farar Albasa da Kanumfari da Citta da Malmo da Barkono da Raihatul Hubbi, sai ta da ke su ta yi yaji ta dinga cin abinci da shi. Ya na saukar da ni’ima da magance duk matasalolin sanyi.

 

9- A samu Sabulun Zaitun da Sabulun Habba sai a daka su. A samu ganyen Magarya da Garin Bagaruwa a daka a tankade. Sai a zuba akan sabulan da aka daka sannan a kwaba da Ma’ul Khal, a zuba Man Tafarnuwa da Farin Almiski. Sai mace ta dinga kama ruwa da shi kullum sau daya. Da ruwan dumi amma ake tsarki da shi. Wannan Sabulu ya na maganin kuraje da kaikayi da fitar wari.

 

10- A samu Man Zaitun da Man Habba da Man Tafarnuwa da Man Kanumfari sai a hade su waje daya. Mace ta dinga shan cokali daya kullum kafin ta karya. Ya na wanke dattin mara kuma ya na samar da ni’ima.

 

11- A samu Ciyawar Kashe-Zaki da Farin Magani sai ta hada waje daya ta dinga jika rabin karamin cokali ta na sha. Sannan ta dinga shan Man Zaitun Cokali daya kullum kafin ta karya. Wannan ya na maganin dattin mara da wanke daudar mahaifa.

 

12- A bare tafarnuwa, idan za ki kwanta bacci sai ki dauki sala daya ki yi matsi dashi, ana son idan mace za ta yi wannan hadin to miji ya daga mata kafa wato kada ya kusance ta, Da safe sai ta tafasa garin hulba ta zauna a ciki zata yi hakan har tsawon kwana uku.

 

13- Ki hada hulba da bagaruwa guri daya, ki dafa idan ruwan ya sha iska sai ki zauna a ciki, kuma ki samu man habbatussauda ki yi matsi da shi. Ni’ima Ba Sassauci Da farko daki samu kadarki wadda ba ta fara kwai ba. Sai ki dare hanjinta ta cikin dunbutu tunda ba a bukatar a yi mata gunduwa-gunduwa. Sai ki gyara ridinki (kantu) ki shanya ya bushe sai ki daka shi. Kina iya tafasa kadar sannan sai ki duba ridin ta cikin dunbutun kadar. Sai ki samu abu ki daure dumbutun; sannan ki hada kayan miya kadan sai ki kara duba nonon rakumi a cikin kayan miyar ki hada ki dafa har sai sun dahu sai ki sauke. Sannan a ranar ki jika kanumfari ya jiku sosai. Ya dama ruwan shanki.

 

Kunun Zakin Dabino: Za ki sami dabino mai kyau ki cire ki tsabtace shi, saiki jika har sai yayi taushi sosai sai ki markada a blander , kisaka zuma ko suga kadan da madarar ruwa, asa yayi sanyi sai ki sha.

 

Jan Hankali Ga Mai Matsalar Bushewar Farji:

 

Sirrin Bushewar Farji:

’Yar’uwa ga dama ta samu, idan ki na fama da bushewar farji, a koda yaushe to sai ki sami man zaitun da man habbatussauda, sai ki hada su wajen daya, ki dinga shafawa a cikin farjinki insha Allah Zaki ga biyan bukata, domin kowace cuta tana da magani, sai dai in baki nema ba, amma in kika nema Zaki samu.

 

Allah Ya sa mu dace

No comments:

INA MAFITA

Maganin Maza

ASSALAFY ISLAMIC MEDICINE CENTER