Amfanin Kanamfari Guda 11
YADDA ZA'A YI AMFANI DA KANUMFARI WAJEN NEMAN LAFIYA
1.CIWON KAI
(A), Yana maganin ciwon kai. A shafa
man kanimfari a goshi, Yana taimakawa
wajen ciwon kai wanda ke faruwa sanadiyar mura.
(B), Idan kuma ciwon kan bana Mura bane, za'a iya samun Kanumfari guda biyar a
saka a cikin ruwa kofi guda, a saka a wuta su tafasa sosai sai a saka Suger
kamar Rabin cokali a ciki idan
ya dan huce sai a sha ayi haka sau 2 a yini In shaa Allahu kan zai daina ciwo
koda kuwa baya jin Magani ne.
2. CIWON HAKORI
Yana maganin ciwon hakori. Zaka
iya amfani da man-kanimfari (clove oil)
ga hakori mai-ciwo ko kuma kanimfarin
(dakakke) , a jikashi kadan da ruwa a
lika wajen hakori mai-ciwo. Idan mai
( clove oil) kake amfani dashi sai asamu auduga a zuba man kadan a lika wajen
hakori mai-ciwo (ka danne da hakora).
3.WARIN BAKI
Za’a iya amfani dashi a matsayin abun wanke baki. Yana maganin warin baki (a
tafashi a yawaita wanke baki dashi sau 3 a rana).
4.MAGANIN AMAI
(A), Domin Tsayawar amai ga Mata masu ciki, a daka kanunfari biyu a sa babban
cokali daya na zuma a sha yana maganin Amai ga macce mai ciki.
(B),Don magance amai baga mai juna biyu ba kuwa, a saka kanumfari 4 a cikin
ruwa kofi daya a tafasa idan ya tafasa a saka sugar cokali daya a sha.
5.TYPHOID
A samu ruwa littr biyu sai a saka kanumfari kamar guda 5 a cikin ruwan a tafasa
ruwan kada a sauke sai ruwan sun koma sauran littr daya sai a sauke idan suka
huce sai a riqa sha Wannan yana Maganin typhoid.
6. Ciwon Kunne;
A hada Man kanun fari da Man Ridi diga a kunne mai ciwo duk lokacin da za'a
kwanta wannan yana maganin ciwon kunne.
7.MAGANIN MURA
Ga masu su mura A tafasashi da citta/jinja (ginger) a sha shayi.
8. MAGANCE MAKERO/KYANDA
Ana goga Man kanumfari a wurin da matsalar tace wannan yana maganin Makero.
9. GIRMAN MAZAKUTA
Asamu nikakken kanumfari ko adakasa sai ajikasa da mansa ahada da man zaitun,
sai ajika "gaba" dashi,idan za'a kwanta,da rana kuwa duk bayan anyi
wanka sai ashafa, wannan yana sa girman Azzakari.
10. KARFIN MAZAKUTA
A samu Man kanumfari duk za'a yi saduwar aure awa daya kafin a fara a shafe
gaba da shi.
11. KURAJEN HARSHE
Don Magance Kurajen Harshe, daka Kanumfari a saka a harshen a barshi zawon wani
lokaci, ko kuma idan za'a kwanta a saka in shaa Allahu kafin safe zasuyi dama.
No comments:
Post a Comment