Friday, May 15, 2020

Yadda Ake Hada Man Karas Mai Kara Tsahon Gashi

Yadda Ake Hada Man Karas Mai Kara Tsahon Gashi

 

Ga abubuwan da ake bukata

1.    Karas

2.    Man zaitun ko man kwakwa

3.    Fiya (Avocado)

Yadda ake hadawa

1.    Da farko za a goga karas din da dan dama sannan a bare fiya guda daya a cire kwallon ciki.

2.    A dora kasko a wuta, amma ba mai zafi ba sosai.

3.    A zuba man kwakwa ko man zaitun din a cikin kwaskon, shima da dam dama

4.    Sai a zuba karas da fiyan a cikin man a barshi ya soyu a cikin man

5.    Ana yi ana juyawa a hankali

6.    Ya kan dauki lokaci saboda wutar ba mai zafi ake bukata ba.

7.    Idan ya soyu, sai a tace shi a bari ya huce.

8.    A juye shi a cikin kwalba mai murfi.

 

Hanyoyin amfani da shi

1.    Za a iya shafa shi kwana daya kafin ranar da za a wanke gashi. Idan aka shafa sai a rufe da leda a kwana da shi. Washegari sai a wanke gashin.

2.    Za a iya amfani da shi a matsayin man kitso

3.    Za a iya shafa shi a jiki da daddare a kwana da shi, da safe a wanke.

 


No comments:

INA MAFITA

Amfanin Kanamfari Guda 11

Amfanin Kanamfari Guda 11 YADDA ZA'A YI AMFANI DA KANUMFARI WAJEN NEMAN LAFIYA 1.CIWON KAI (A), Yana maganin ciwon kai. A shafa ...