YOYON GABAN MACE (VAGINAL DISCHARGE)
Abin da ya kamata mu sani shi ne yoyon da gaban mace yake yi yana da wani amfani na tsaftace gabanta da tabbatar da lafiyarta a kowani lokaci, yadda halittun gabanta suke iya qoqarinsu wurin kawar da matattun qwayoyin jiki da sauran qwayoyin cuta dake kwance a gabanta ko bakin mahaifa, wannan aikin da suke yi ba ko shakka garkuwa suke ba mace daga qwayoyin cuta, yoyon da take yi halitta ne ga mace dama, sai dai akan dan sami bambanci tsakanin wannan da wancan gwargwadon yawan ruwan da zai fita ko yanayin qarninsa, kamar canjawa daga kalar miyau zuwa kalar majina. .
Masana sun nuna cewa yawan yoyon da gaban mace yake yi kan iya qaruwa gwargwadon lokacin da za ta nasa qwai, ko in tana shayarwa ko kuma in sha'awar saduwa ta kama ta, yakan dan fara tashi in ya kasance tana da juna biyu ko in ta yi biris da tsaftace gaban, akwai launuka da ruwayen kan canja, sai dai ba wani babban abin damuwa ne sosai ba sai in ta ga launin ya bambanta sosai, ko yana tashi yadda zai dami wani, masamman in akwai qaiqayi, ko radadi, wannan kam alama ce ta samuwar infection ko wata matsalar da ba a gama gano kanta ba. .
LAUNUKAN RUWAYEN
Akwai launuka daban-daban wadanda a dalilinsu ne ma ake iya rarrabe nau'o'in ruwayen da ma matsalar da mace ke fama da ita, misali
1) Fari: Akan sami dan ruwa, fari, kadan, dake fito wa mace dab da fara al'ada ko tana qarewa, wannan ba a tunanin cewa matsala ne, sai dai in an sami qaiqayi, ko in ruwayen sun daskare sun yi wani guda-guda, a irin wannan yanayi akan yi tunanin cewa infection ne yake qoqarin kama mace.
2) Tsinkakken ruwa maras kala, wannan ba matsala bane yakan fito a kowani lokaci, galibi in mace ta dan motsa jiki sai ya fito mata da dan dama. .
3) Tsinkakke mai yauqi, ko in ya yi kauri kamar majina, sau da yawa wannan yana nuni ne da cewa lokacin nasa qwai ya yi, shi ma ba wata matsala ba ne.
4) In ya yi ruwan zuma ko jini-jini, masamman a tsakankanin lokacin al'ada, ko da zarar ta kammala, wasu in sun gama kwanakin al'adan ne sai wannan ruwayen ya fara fitowa, to in dai ya yi hanta-hanta kuma kin san kin sadu da namiji gaskiya gwara ki yi magana da likita, don wani sa'in alamun ciki ne, ko kuma alamu ne dake nuna cewa cikin na neman ya fita. .
Dole a dauki matakin kai tsaye, don wadannan ruwayen dake dauke da wannan kalar a wasu lokutan suna nuna cewa ne za a iya samun cancer ta bakin mahaifa, yin scanning na da matuqar amfani. 5) Rawaya-rawaya ko tsanwa-tsanwa masamman idan ya riqa fitowa da kauri ko guda-guda, sannan ya riqa yin wani irin wari, wannan kam tabbas akwai matsala, alama ce dake nuna cewa akwai infection ko wata cuta da ake daukarta ta hanyar saduwa wato "Trichomoniasis". .
DALILAN KAMUWA DA CUTAR
Dole dai akan dan sami ruwaye dan kadan a gaban mace gami da bakin mahaifa, wanda su suke fitarwa don gaban nata ya zauna da tsafta, tsinkakken ruwa ne fari bai da qarni, in aka ga ruwan ya qaru, ko ya yi kauri, ko ya canja kala ko kuma yana tashi, lallai a fara lalubo dalili, wadannan alamomin duk suna tafe ne gami da bayanin canjawar komai, kamar kalar ta koma shudiya ko rawaya, ko ta yi guda-guda, ko ta fara yoyo sosai, ko kuma a fara jin ruwayen na tashi, a taqaice dai haka kurum mace ba za ta riqa jin qaiqayi ko radadin fitsari ba, ko wurin saduwa ta ji kamar ana yanka ta.
ALAMOMIN KAMUWA DA CUTAR
1) Danyatar gaban mace na qwayoyin cuta wato "Gardnerella vaginitis" ba ta cika matsa wa mata ba, akwai dai ruwaye fari da surkin ruwan toka, yana da qarni.
2) Na "Trichomoniasis" ruwan qwai ne ko kore yana da wari, akan ji zafi yayin jima'i ko fitsari, ga qaiqayi.
3) "Gonorrhea" shi akan ji zafi wurin fitsari, kuma akan yawaita fitsarin, ruwa kan fito rawaya, gaban mace kuma kan danyata ga qaiqayi. .
4) "Chlamydia trachomatis" ita ma kamar "Gonorrhea" take, sai dai ba ta cika matsawa ba, amma akwai yoyo da yuwuwar samun zafin fitsari ko wurin ya dauki radadi yayin saduwa.
5) Sai kuma "Candidiasis" wannan farin ruwa ne mai kauri, bai cika wari ba amma za a iya samun radadi, qurarraji, ko zafi lokacin da za a yi fitsari, matsalolin na da yawa in za a fadi dalilin kowanne, maganar za ta iya yin tsawo, a yi qoqarin ganin likita kawai don riga kafi. Allah ya karemu daga muggan cuttutukan masu adabarmu.
No comments:
Post a Comment