GYARAN FUSKA DA FATA,CIKINS SAUKI.
A yau zamuyi bayani game da gyarna fata, musamman masu fama da yawan kananan kuaraje da yawan gumin fuska da maiko na fuska.
Ga duk mai son rabuwa da wandan nan matsalolo ga hanya ingantacciya,wacce bata da wata illa,kuma ba tare da kashe wasu kudade ba,domin wasu masu son gyaran fuska da fata suna amfani da mayukan da suke dade fata wadan kuma suna da illoli sosai ga lafiyar fata.
Ga wasu hanyoyi Guda 3 wadda kowacce idan akai amfani da ita za'a samu Nasara.
HANYA TA FAFKO.
ZA'A NEMI.
1. Lemon tsami
2. Zuma
Da farko za'a matse lemon tsamin a cikin wani abu kamar roba,sai a zuba Zumar a ciki a cakuda sosai sai a shafe fuska da shi na tsawon minti 15 kafain wanka,sannan a wanke da ruwan dumi a shafa man Zaitun a fuskar.
HANYA TA BIYU.
ZA'A NEMI.
1. Danyen kwai
2. Zuma
Da farko zaa fasa kwan amma iya farin ruwan kwan banda kwandowar,sai a kawo Zuma a zuba a cakuda sosai a shafe fuska na tsawon minti 15 kafain wanka sai a wanke da ruwan dumi.
HANYA TA UKU.
ZA'A NEMI.
1. Tumatur(Tomato)
2. Lemon tsami
3. Zuma.
Da farko zaa matse lemon tsamin a runa, sannan a matse Tumatur shima a ciki sai a kawo Zuma azuba a ciki a huya sosai sannan a shafe fuska da shi na na tsawon minti 10 kafun wanka sanan a wanke da ruwan duni.
Dukkan kowacce hanya da zaka gwada zakayi na tsawon sati daya ko biyu gwargwadon yadda kake son fatar taka tayi kyau.
No comments:
Post a Comment