Friday, June 5, 2020

MATSALOLIN RASHIN HAIHUWA (STERILITY DISEASES)

MATSALOLIN RASHIN HAIHUWA (STERILITY DISEASES)


Galibi in aka sami kusan shekara ba a haihu ba mace ake zargi da cutar rashin haihuwar ba namiji ba, bayan kuwa kowa na da matsalar, namiji ma na iya kamuwa da ita, koda zai auri mata dari ba za su haihu ba, kamar yadda mace in za ta auri mazan duniya ba haihuwar, in Allah ya so su da samun juna biyu sai ka ga ya ba su lafiyar cutar da suke fama da ita, kamar mace in ya kasance ba cutar ba ce ta ainihi wata matsala aka samu wace a dalilinta cikin ya qi shiga sai a yi qoqari a gano matsalar, da zarar an magance ta kuma za ka ga cikin ya shiga ba tare da matsala ba.
.
"Kararanci" na nufin rashin haihuwa ne yanke, sai a ce wa mutum bakarare ko juya, galibi irin wannan cutar ba ta jin magani ko qalilin, kamar toshewa ta gaba-daya da bututun qwan mace ke yi, ko macewar qwanyin namiji, yanzu dai akan sami wasu dabarbaru da akan shawo kan matsalar ko a magance ta in har an gano ta, babban abinda ya sa ake ta magani don neman haihuwa ba a dace ba galibi ana ta qoqarin magance cutar da ba ita take damun majinyacin ba, ko kuma mai lafiya yana magani, majinyaci kuma yana kallo, sai a dade ba amo ba labari.
.
ALAMOMIN KAMUWA DA CUTAR


Babbar alamar cutar ita ce a dade ba a sami haihuwar ba, matsala ta biyu kuma ita ce tantance wa yake dauke da matsalar, mijin ko matar? A bayyane dai babu wata katamaimiyar alama, sai dai ga mace wani sa'in akan sami rashin daidaituwar al'adarta, ko ma gaba daya al'adar ta bace, kamar namiji sai dai in an ga alamun matsalolin "hormones" kamar gashi ya riqa qin tsirowa ko shi da kansa ya ga wasu alamomi a gabansa wajen saduwa ko gabobin saduwar.
.


DALILAN KAMUWA DA CUTAR
Koda yake an raba cutar zuwa gida 3:-

  • 1) Wace take samun mace tun haihuwarta ko bayan ta yi aure.
  • 2) Wace ke samunta bayan haihuwar farko, ko bayan yin 'bari ko daukar ciki a wajen mahaifa.
  • 3) Wace take samun maza kuma kamar macewar qwanyi, ko harbawar ta yi qaranci ya zamanto qwanyin ba za su iya isa ga qwan macen ba.

Mafi yawancin dalilan cutar kan rabu ne bisa wadannan dalilan guda 3, kuma za mu maida hankali ne a kansu:-
.


A WURIN MAZA
1) Akwai matsalolin hormones, masamman wadanda ke da alaqa da qwaqwalwa dana wuya da pancreas.
2) Samun matsala tun daga wurin bubbugar maniyyin, ya zamanto an sami tawaya ko wata cutar, tun lokacin balagar mutum ko bayan lokacin, kuma an watsar ba a dauki matakin da ya dace ba.
3) Yanayin halitta dan bututun maniyyin ya toshe, ko kafin ya hadu da na fitsari bayan ya hadudin a sami danyatar bututun.
4) 'Ya'yan gwailon jariri ba su sauka a cikin jakarsu ba uwar kuma ba ta bincika ta tabbatar da samuwarsu ba, kamata ya yi duk uwa ta tabbatar 'ya'yan gwailon danta guda biyu sunanan.
5) Ko a rasa bututun maniyyin da zai dauko shi zuwa waje gaba daya.
.
6) Cutar sanyi dake samun namiji za ta iya haifar da matsala ta masamman.
7) Tsinkewar ruwan maniyyi a dalilin "Prostate" ko qarancin Fructose".
8) Illar da ake samu a jijiyar 'ya'yan gwailon mutum.
9) Samun matsaloli da garkuwar jiki inda ake haduwa da abubuwan dake kashe qwanyi.
10) Cancer dake kama 'ya'yan gwailo da sauran cututtuka.
11) Kwanowar ruwan maniyyi bayan an harba shi; A maimakon ya yiwo waje sai ya koma 'ya'yan gwailo.
12) Sai kuma ruwan maniyyin zuwa mahaifan mace nan ma za a iya gamuwa da wasu matsalolin da za su iya shafar maniyyin namiji kamar:-
.
a) Shan taba sigari da wiwi, cocaine da sauran kayan barasa.
b) Shaqar wasu abubuwa dake da guba, kamar kayan feshi, maganin sauro da sauran qwari, ko zama a inda akwai mugun zafi masamman na wuta.
c) Qarancin vitamin C a jiki.
d) Amfani da wasu magunguna na tsawon lokaci, kamar magungunan cura tsoka wurin masu wasan gina jiki ko daga nauyi.
e) Hauhawar jini dake bata hanyoyin jinin, zai iya shafar miqewar alqalamin namiji.
f) Muguwar qiba dake kawo matsala wurin saduwa da toshewar hanyoyin jini wace take da tasiri a qarfin alqalami.


.
A WURIN MATA
Akan sami matsaloli ma a wurin mata kodai bisa dalilin hormones ko rashin nunar gabobin saduwar mace a halicce, sauran za ka taras suna da alaqa da haihuwa, bari ko danyatar mahaifa ko kuma bututun qwanyin mace ko ma matsalolin da ake samu wurin nasa qwai wato "Ovulatory Dysfunctions":-

  • 1) Samun qananan jakunkuna a qwai din wato "Polycystic Ovarian Disease"
  • 2) Ya ma sami matsala gaba-daya:-

a) Matsalar da ake samu ta halitta yadda nan da nan qwan ke mutuwa saboda wani abu na halitta.
b) Haduwa da wasu matsaloli na magunguna kamar laza yayin aikin Cancer, qwayoyin cuta, ko shan taba.
c) Sai matsalolin garkuwar jiki yadda suke abka wa qwanyin mace.
d) Wasu matsalolin da ba a ma san kansu ba wato "Idiopathic".
e) Dauke qwanyin gaba daya saboda wasu daliloli.
.
f) Akwai wasu matsalolin na jiki kamar gazawa wurin sakin wasu hormones "Gonadotrophin Deficiency" saboda:-
i) Kumburi daga qwaqwalwa "Pituitary Tumors".
ii) Gamuwa da wata cuta da ta kawo matsala wato "Pituitary Lesion Destructive".
iii) Matsaloli wurin saduwa wato "Hypothalamic failure" wannan kan iya zama babbar matsalar dake yaduwa, ita take haifar da matsalolin nasa qwan mace.
.
Akwai wasu cututtukan dake da alaqa da toshewar bakin bututun da qwan mace kan bi ya gangaro, idan har ya wuce 3cm yakan toshe bututun ne ya hana qwai ya gangaro, ko a sami mannewar bututun wanda za ta hana qwan isa ga mahaifa a lokacin da ake buqata, haka in aka sami ciki a wajen mahaifa shi ma babbar matsala ne, ko in bututun asali bai da tsawo bai wuce 4cm ba.
.
Matsalolin mahaifa sukan haifar kamar cutar:-
a) Matsalolin da wasunsu sukan faru ne a dalilin bari da mace ke samu sai ya shafi haihuwanta masamman in an yi mata aiki, ko in mahaifar na qarin qaho wato "Rudimentary horn" wannan zai iya sakawa ta sami cikin a wajen mahaifa, wace take da sifar "T" kuma ta sami jinkirin haihuwa ko bari.
b) Mannewar mahaifa a dalilin yawan wankin mahaifar ko danyatar mahaifar, ko wani rauni a cikin mahaifar, wannan kam da yawa za ka ji mata na kukan cewa al'adarsu ta yi qaranci matuqa.
.
c) Sai kuma samun "Fibroids" a cikin mahaifa koda yake ana cewa bai haifar da cutar rashin haihuwa amma fa in ya yi tsanani yana illa masamman aikin da ake yi wajen tsaftace mahaifar, haka lalacewar mahaifar wato "Fibrosis" bayan mace ta yi fama da danyatar mahaifa.
d) Samun wani kumburi a cikin mahaifa wanda a dalilinsa za ka ji mace na ta kukar radadi a yayin al'ada.
.
WASU DALILAN KUMA
Akan sami wasu matsalolin a rasa gane dalilansu kuma, kamar dai:-
1) Sammun maiqo mai dama a cikin ruwan maniyyi wato "Fatty Acids".
2) Samun ruwan jiki (WBC) a tsukin mahaifa "Cervical Leucocytosis".
3) Wasu matsaloli na gado daga iyaye.
4) Qarancin vitamins ko taruwar iron.


Matsolin rayuwa kuma akwai rashin hutu a wurin namiji, yadda a qarshe ya kasa fitar da lafiyayyen qwanyi, natsuwarsa da kwanciyar hankali na taimakawa wurin maganin saurin kawowarsa, raunin alqalami da rashin kawowar, maganganun na da yawa a nemi likitochi.




No comments:

INA MAFITA

Maganin Maza

ASSALAFY ISLAMIC MEDICINE CENTER