Monday, June 29, 2020

Dadin Aure

Amarya ko Uwar vida, Menene jin dadin Aure???

Masu fama daukewar ni'ima da rashin sanin dadin aure ko rashin nishadi to amarya ko uwar gida ga yanda zaki magance wadannan matsaloli cikin sauki.

*aya* *zuma* *dabino* *garin sallaja*

sai ki markadesu ki tacesu sai ki rinka diba kadan-kadan kina hadawa da zuma da garin habba kadan kina sha safe da yamma.

*WADDA BATAYI AURE BA KADA TAYI* mijinki zai ji kin canza sosai.

SINADARIN MA 'AURATA

shi wannan wani sinadarine mai albarka wanda ake yi masa lakabi da sinadarin ma'aurata, kuma yana jimawa a jiki, sannan yana kara kuzari kuma yana karawa mace martaba ga mijinta. zaki samu:

  • *furen zogale*
  • *zanjabil* 
  • *habba* 
  • *garin raihan*

sai ki dakesu guri daya sudaku dakyau sai rinka diban karamin cokali kina hadawa da zuma kina safe da yamma shima wannan sai mai aure amma idan kin kusa yin aure zaki iya yin wannan hadin.

HADIN MATAN MASAR DA MATAN SUDAN:

ko shakka babu shi wannan hadin matan masar da matan sudan,da matan jordan suna yinshi yana kara ni'ima musamman yana gyara aure, kuma yana kara dadi wurin saduwa yana kuma sa nishadin masoya, sannan kuma zaki zama yar gaban goshi.

  • kankana mai kyau
  • zuma
  • raihan

sai ki yayyanka kankanar ki zuba a kofi, ki saka zuma da madarar ruwa da garin raihan sai ki rinka sha safe da yamma.

RASHIN SHA'AWA

akwai matanda basayin sha'awa ko basa jin dadin saduwa ko ni'imarsu ta dauke, to yanda za'a magance wannan matsala shine sai kisamu

  • zangarniyar zogale,da ya'yanta gadaya
  • karanfani
  • citta
  • masoro
  • kinba

sai ki dakesu guri daya su zama gari,sai ki rinka shan wannan hadi a shayi safe da yamma,ki gwada ki gani, yana kara dadin da mai gida zai gamsu sannan kuma zaki rinka cin dabino(ajuwa) mai kyau tare da kwakwa zaki sha mamaki.

NI'IMA◦ SINADARI MAI DADI

ga wani hadi na musamman dan karin ni'ima da nishadi da dadi.  *ya'yan zogale* ,*kankana* sai ki dakesu guri daya suyi laushi sai ki rinka sha da nono safe da yamma.

DON FARIN CIKIN MA'AURATA

shi wannan wani hadi ne da akeyinshi dan farin cikin ma'aurata, kuma yana sa asamu nishadi da kuma karin ni'ima da dadi, yanda akeyi shine za'a samu.

  • kankana mai kyau sosai( a yayyankata)
  • ya'yan zogale
  • kumasoriyya ta asali
  • ayaba mai kyau sosai

ya'yan zogale da kumasoriyya za a dakesu da kyau suyi laushi, sai ki rinka diban karamin cokali na garin maganin kina hadawa da wancen kankanar da ayaba da madara ta ruwa, sai ki yamutsasu ki rinka sha, sau biyu a rana safe da yamma.

sannan▻ kuma in zaki kwanta da daddare sai ki hada farin miski da zuma farar saka da man zaitun mai kyau ki rinka shafawa a gabanki,zai kashe kwayoyin cututtuka da gamsar da maigida da nishadi.

DON MAGANCE ZAFIN SADUWA:

wannan wani hadi ne da akeyi don magance zafin saduwa ko rashin sha'awa ko daukewar ni'ima.

◘-dabino

◘-garin ridi

◘-garin habba

◘-da garin raihan

sai a samu zuma lita daya a hadasu wuri daya a rinka sha cokali daya a ruwan shayi safe da yamma.




No comments:

INA MAFITA

Maganin Maza

ASSALAFY ISLAMIC MEDICINE CENTER