Monday, June 29, 2020

Bushewar gaban 'Ya Mace

Yadda ake magance masala bushewar gaba

Tambaya*****Assalamu alaikum malam Allah yasa kama da mafificin Alkairi Amin malam dan Allah a taimaka min kamar yadda aka saba koda magani ko shawarwari malam wallahi gabana ne wato azzakari na ne wajan tabon yake qaiqayi Lamar zanyi hauka idan na Sosa Saita tsantsage kamar anyanka da reza, sai kuma matata itakuma gabanta ne yake farin ruwa dan Allah malam ataimaka mana Allah yasakama da Alkairi ameen. Dan Allah aboye sunana daga wani dalibinka nagode.

AMSA ******* Wa alaikumus salam wa rahmatullah wa barakatuh. Lallai bisa dukkan alamu ka dauki wannan matsalar ne daga wajen Matarka sanadiyyar wannan infection din dake tare da ita. Shi kuma irin wannan infection din na mata yana da sabubba masu yawa ga wasu kadan daga ciki :

  • 1. Sanadiyyar rikicewar jinin haila.
  • 2. Sanadiyyar Qazantar Underwears da take amfani dasu.
  • 3. Sanadiyyar amfani da Public Toilets marassa tsafta.
  • 4. Sanadiyyar Istimna'i.
  • 5. Sanadiyyar Jinnul Ashik (Namijin dare).

Idan har wadancan dalilan ne (from 1 to 4) suka haddasa mata matsalar, to in sha Allahu maganin asibiti ma (Antibiotics) zasu yi tasiri sosai. Amma idan Ashiq ne sanadiyyar matsalar, To dole sai anyi mata rukyah an rabashi da jikinta sannan Infection din zai warke gaba daya. Idan ta warke kaima zaka warke in sha Allahu.

Amma ga wasu magunguna nan ku jarraba:

Ku nemi ganyen Raihan ku rika tafasawa (cokali 2).tare da garin hulba (cokali 1) da kai da ita kowa ya rika yin Sit-bath dashi (wato kuna shiga cikin ruwan maganin bayan an sirkashi). Sannan ku rika tafasa furen Albabunaj kuna sha tare ds zuma. shi kuma zai wanke muku mafitsararku, Zai gyara muku Qodarku da dukkan reproductive organs dinku. Sannan ku rika shafa Man lalle ko Man Zogale ajikin al'aurarku domin samu saukin wannan tsagewar. Allah ya sawwake. Allah ya baku lafiya.



No comments:

INA MAFITA

Maganin Maza

ASSALAFY ISLAMIC MEDICINE CENTER