Tuesday, June 30, 2020

MATSALAR CIWON MARA

MATSALAR CIWON MARA NA MATA ME KAWO MATSALA A MAHAIFA.

Ciwon mara lokacin jinin al'ada wata larura ce da ke takurawa mata kwarai da gaske, saboda sau tari za ka ga matan dake fama da wannan matsala na fargabar zuwan lokacin da su ke jinin al'ada. Ba don komai su ke wannan zulumi ba, sai don tsananin azabar da su ke sha duk lokacin da su ka samu kansu a wannan hali saboda tsananin ciwon marar da suke fama da shi, sakamakon zuwan jinin.

Ciwon mara yayin al'ada wani irin ciwo ne da ke tsananta wajen wasu matan, ya na galabaitar dasu, za ka ga wasu har amai ya ke sa su, yayin da wasu numfashinsu ke dauke wa ya kai su ga suma.

Masana a wannan fanni dangane da wannan matsala ta ciwon mara yayin jinin al'ada, sun raba mata zuwa gida biyu. Kashi na farko shine, 'yan mata dake fama da ciwon mara lokacin al'ada tun kafin su yi aure. Sai wadanda ke fama da matsalar ko da bayan sun yi aure.

Dangane da kashi na farko, binciken masanan ya nuna cewa, wadansu 'yan matan su kan yi gam-da-katar wajen rabuwa da wannan matsala da zarar sun yi aure. 

Amma wasu su kan ci gaba da fama da matsalar ciwon marar ko da bayan sun yi aure, wadannan sune rukuni na biyu, kuma akansu ne za mu yi bayani


Duba da irin tsananin da mata ke fuskanta sakamakon wannan matsala ta ciwom mara lokacin alada yasa aka gudanar da bincike ga kuma sakamakon binciken da mu ka yi nan. 

Sai dai kafin kawo wa mai karatu sakamakon wannan bincike zai yi kyau mu yi tsokaci kan jinin al'ada.

Mu na kyautata zaton mai karatu ya san cewa, jinin al'ada tsarkin mahaifa ne, abin nufi idan mace ta yi al'ada wannan ya na nuna cewa, ba komai a mahaifarta, ma'ana ba ta dauke da juna biyu ke nan. Wannan hikima ya sanya Addinin Musulunci ya lizamta wa matan dake jini yin iddar saki ta hanyar tsarki uku, wanda hakan ke tabbatar da cewa, wannan mace ba ta dauke da juna biyu. Kuma hakan sai ya tabbatar da kare nasaba, yadda ba za a dauki dan wanda ya yi saki, a kai wa wanda zai aura ba. Wannan ni'ima ce da za mu ci gaba da godewa ALLAH (S.W.T) a kan ta. 

To sai masanan su ka ce, ciwon mara a lokacin jinin haila na faruwa ne, sakamakon yadda mahaifa ke takura da kuma motsawa domin fitar da wani abu daga cikinta wanda ba shi da amfani, to hakan ne ke haifar da ciwon mara ga mata.

Kamar yadda mu ka fada a sama mata sun sha banban dangane da ciwon mara lokacin al'ada, hakanan yanayin ciwon ya sha banaban, bugu da kari dadewa da kuma lokacin da ciwon ke farawa ko ya dauke, ya banbanta daga waccan mace zuwa waccan.

Yadda 'yan uwa mata za su bi, don maganin wanan matsala ta ciwon mara lokacin jinin al'ada. Mun yi kokarin kawo hanyoyi da yawa, sai ki dauki wacce ki ke ganin ta fi mi ki sauki ki jarraba, don kuwa tuni aka jarraba kowacce daga cikin hanyoyin kuma aka samu waraka da fatan Allah Ya sa mu dace, amin.



No comments:

INA MAFITA

Maganin Maza

ASSALAFY ISLAMIC MEDICINE CENTER