CIWON SANYI NA MATA
dalilai da yawa suna saka mata kamuwa da ciwon sanyi saboda idan namiji yanada dashi zai iya sakawa mace ga kuma shiga kowanne toilet ko wajen tsugo a toilet sannan kuma koda mata hudune agida aka samu daya me wannan cutar tana iya sakawa sauran shiyasa mata masu hikima basa rabuwa da riga kafin cutar akwai abunda Zaki fara shine shan Maganin sanyi domin naciki ya mutu
Kuma idan Zaki hada da kanki ga yanda zakiyi zaki samun garin ganyen magarya da garin hulba da yayan habbatussauda da garin zogale da ganyen gasaya da kanunfari ki dafashi kitace ruwan wannan shima zakisha ruwan kullum yana kashe infection na ciki ko kuma kisamu Garin hulba da garin habbatussauda da garin tafarnuwa da garin zogale duk zaki hadasu waje daya ki hada da zuma kinashan cokali uku kullum 1 hulba kadai zata iya kawarda ciwon idan kika samu garinta me kyau kullum kina dafa cokali Biyu kinasha sau Biyu arana 2
Yan zogale suma sunada amfani awannan fannin zaki iya hadasu da yayan tafasa da Garin tafarnuwa kina hadawa da Zuma kinasha 3 sassaken gabaruwa kuwa da sassaken mangwaro da Garin hulba dafawa zakiyi idan kina zama acikin ruwan da dumi duminsa har tsawon mako Biyu (2weeks)
NAZARI A KAN CIWON SANYI
(Gonorrhea)
Ciwon sanyi ciwo ne mai mugunta sosai, in aka sake da shi ba'a hanzarta daukar mataki ba, ya na iya jawo miyagun illoli masu barna sosai. *Abubuwan da ke jawo shi* Wasu 'yan kananan kwayoyi cuta dangin jarsume (Germs) wadanda a ke kira (Gonococcus) su ne masu jawo wadannan muguwar cuta. *Alamomin farko* Abu na farko da fara nuna cewa mutun ya kamu da ciwon sanyi shi ne: 1- Zafin fitsari da yinsa da kyar, kuma a kai-a kai da fitarsa kadan kadan. Ga mata kuma ya na iya fitowa a gefen dumbarun Gaba (farji) ko daga sama wajen tsirowar gashi, wannan kurji na kitsinya yana iya fitowa a wasu wuraren gefen al'aura har ya warke shi kadai ba tare da sha magani ba, daga karshe ya zama hatsari.
GA MAZA
- Ciwon magudanar maniyyi zuwa 'ya 'yan maraina.
- ii- Ciwon 'ya'yan maraina da kumburinsu.
- iii- Ciwon burustata.
- iv- Ciwon mara.
- v- Ciwon kuiba-kuiba.
- vi- Toshiyar mafitsara. In wadannan alamomi suka cigaba, ba tare da an dauki mataki ba, ciwon zai iya gawurta, ya fara nuna wasu alamomi, wadan da su ka hada da.
- i- ciwon gabobi.
- ii- Ciwon ido da kaikayi tare da bushewar idanu. iii- Kwaro-kwaro (kaikayin matse-matsi) iv- Ciwon mara.
- v- Ciwon jiki.
- vi- Ciwon baya da rikewar kugu.
GA MATA KUMA*
1–Zubar farin ruwa, kuma ruwan zai iya zuwa kamar haka:
- i- Majina.
- ii- Madara.
- iii- Kindirmo.
- iv- Tumbudi.
- v- Guntsarin nono.
- vi- Kamar awara.
- vii- Kamar an tauna kwakwa.
2- Ciwon Muhbalin mahaifa, mai jawo yawan ciwon mara.
3- Ciwon baroro mahaifa, mai jawo kuiba-kuiba.
4-Kwaro-kwaro (kaikayin gaba)
5- Wari ko doyin farji, kuma a na iya jinsa ta numfashi.
*********
Zamu kawo ci gabansa nan gaba.
No comments:
Post a Comment