ASSALAFY ISLAMIC MEDICINE ENTERPRISE
ASSALAFY ISLAMIC MEDICINE CENTER Muna Rukya, sannan kuma muna saida Magunguna na Musulunci da na Gargajiya, sannan kuma muna hada magunguna , musamman wadanda suka shafi na sihiri, Jinnu da sauransu. Muna hada mayukan gyaran jiki, magunguna da suke kara Ni'ima, girman Nono, Hip Up, Man Vaseline...etc kuna iya kiran Mu ko whatsapp: +2347016433333, +2347039620000 youtube: https://youtube.com/c/assalafyislamicmedicinecenter
Sunday, September 28, 2025
DABINO
Amfanin dabino a jikin Dan adam.
Dabino yana daya daga cikin 'ya'yan itatuwa masu matukar amfani ga jikin adam saboda irin sinadaren da ya dauke dashi. Dabino yana girme ne a bishiya kuma 'ya'yan na cure ne kuma ya fi son yanayi mai zafi. Bayan 'ya'yan dabinon sun nuna ana iya cinsu hakan nan kokuma a cire kwallon da ke ciki a sarrafa su ta wasu hanyoyin don more lagwada da amfanin da dabinon ke dauke dashi.
Ga dai wasu fa'idoji guda shida da dabino keyi a jikin dan adam.
1. Dabino nada tasiri wajen kara kuzari ga masu aure Binciken masana kimiyyan sinadaren abinci ya nuna cewa dabino yana da matukar muhimmanci wajen kara kuzari tsakanin ma'aurata. Domin samun wannan fa'idar, sai mutum ya debi dabino kamar cikin hannunsa ya jika su cikin nonon akuya su kwana, da safiya sai a marka dabinon tare da nonon kuma ana iya kara zuma da cardamom. Wannan hadin yana da mutukar amfani wajen inganta kwanciyar aure.
2. Maganin gudawa Dabino da ya nuna sosai yana dauke da sinadarin potassium wanda ke da mutukar muhimmanci wajen magance gudawa. Sinadarin fibre da ke cikin dabino kuma yana taimakawa wajen magance basir da sauran matsalolin da ke da alaka da fitar bayan gida da gyaran ciki.
3.Lafiyar zuciya Dabino yana da matukar amfani wajen karawa wa zuciyar dan adam lafiya. An fi samun fa'idan da ke cikin dabinon idan an tsoma shi cikin ruwa ya kwana sai a dauko a ci da safe. Hakan yana da matukar amfani ga masu fama da ciwon zuciya. Sinadarin Potassium da ke cikin dabinon yana kare buguwar zuciya da wasu cututuka masu kama da hakan.
4.Karin kuzari Dabino na dauke da suga wanda basu da ila ga jikin dan adam kamar glucose, fructose da sucrose. Saboda hakan duk lokacin da mutum ke jin kasala idan yaci dabino zai samu kuzari nan take.
5.Karfafa garkuwan jiki da magance allergy Wani abin mamaki game da dabino shine yadda take dauke da sinadarin sulphur wanda ba'a cika samunsa a 'ya'yan itatuwa ba amma kuma yana da matukar amfani da jikin dan adam cikinsu kuwa harda kara karfin garkuwar jiki da magance 6.Yana taimakawa masu son mayar da jikinsu Dabino na dauke da suga, sinadarin Protein da ke gina jiki da kuma vitamins. Kilogram daya da dabino na dauke da calories 3,000 wanda hakan sun isa jikin dan-adam biyan bukatun ta na kwana daya. Idan mutum ya rame kuma yana son mayar da kibansa, dabino na iya taimakawa wajen gina jiki sai mutum ya jibinci cin dabinon
Amfanin tumatir ga lafiya da Adam
AMFANIN RUWAN TUMATIR
Tumatir yana dauke da sinadirrai daban daban masu dimbin amfani ga lafiyar jikin dan adam.
Bincike ya tabbatarda cewa a kowane kofi daya na ruwan tumatir na daukeda kaso 75 na sinadirin vitamin C, da kaso 22% na vitamin A.
Ana samun sinadirin Vit E da vitamin K da Folate da niacin,da pantothenic acid da riboflavin da B6 da potassium da manganese da phosphorus da copper da iron da magnesuim,da sodium da makamantansu.
Sinadirin potassium dake a cikin ruwan tumatir yana taimakawa matuka musan dan rage taruwa ko yawaitar sodium a cikin jiki da kuma rage hauhawan jini (blood pressure)
Lycopene wani sinadirane dake akoi a cikin ruwan timatir - yana taimakawa wajen karfafa jiyojin jini har zuwa ga zuciya.Haka kuma suna kona sinadiran cholesterol dake katutu a cikin jini ya daskare hanyoyin jini har ya haifarda wata illa ga zuciya.
Ruwan tumatir yana kare jiki daga barazanar kamuwa da kansa (ciwon daji).Bincike ya tabbatarda cewa wannan sinadirin na lycopene yana daukeda wasu magunna dake magance ciwon daji (anti imflammatory da anti cancer cells).Haka kuma lycopene din yana rage girman ciwo ko kurji na ciwon daji (tumor) dake tsira ga hanta,huhu,mamma,da kuma prostate cancer.
Yana rage kiba da tumbi da nauyin jiki sanadin samuwar sinadirin leptin.
- A wani bincike da kasidar British journal of Nutrition in 2013 ta kaddamar ta gano cewa ruwan timatir na rage mafiyawan cutukan zuciya da kuma ciwon suga.
- Ruwam tumatir na narkarda abinci a cikin kankanin lokaci(fast digestion)
- Ruwan tumatir na kara samarda garkuwar jiki.(boosts immunity)
- Ana tarfa zuma a tareda cokali uku na ruwan tumatir sai a tagasa a sha maganin cutukan ciki da zafin jiki.
- Ana soya kwai da timatir da albasa dan samun ruwan maniyi ga jiki.
- Ruwan timatir na karin jini a jika.
- Sai dai da yake ruwan tumatir nada tsami(sour)dan haka mai olsa sai yasan yanda zai sha.
- Haka kuma mai ciwon Acid reflux disease sai ya nemi shawara kamin ya sha da bayanin da za ayi mashi.
Cutar Limoniya (Nimonea)
kamar haka:
HANYOYIN 10 MAGANCE INFECTION
- HANYOYIN 10 MAGANCE INFECTION
- ‘Yan Uwana Mata barkan mu da sake saduwa daku a cikin wannan fili namu mai matukar farin jini, wato Sirrin Gyaran jiki… Kamar yadda kuka sani shi wannan shiri a na yin shi ne don matan aure zalla domin basu shawarwari ta kowane bangare na rayuwarsu ta yadda za su samu su gyara zaman takewarsu da mazajen da mu’amalar su ta bangaren girki, tsafta, gyaran gida da gyaran jiki. Irin abubuwan daya kama mu mata mu dinga ci domin karin ni’imar mu da gamsuwar mazajen mu, da ma duk wani abu daya shafi rayuwar ya mace. Da fatan za ku dinga bibiyata a cikin wannan shiri.gurin da nayi kuskure sai nace Ina neman afuwar ubangiji da afuwar ku domin ajidan ci irin na dan Adamtaka, gurin kuma da nayi dai dai Sai nace Allah ya hada mu a ladan baki daya.
- Da farko Lallai ya kamata ku gane cewa infection yanada wuyan magani domin maganine da se andauki lokaci anayi kamin ya warke gaba daya,inda sansamune ku dauki lokaci kaman wata 6 ajere koma fiye shine zakiga kin maganceshi gabadaya amma in zaki fara ki bari to lallai zaki dade kina magani baki maganceshi gabadayaba. kuma lallai wacce take da miji sai sunyi magani su biyu amma intasah magani ita kadai kamar tayi a bandane don suna kara saduwa da mijin ata kara
- daukar ciwon_
- Mu na rokon da Allah ya baku lafiya ingantatta kuma yasa kaffarane.
- A gwada daya daga cikin wadannan:
- 1- A samu Saiwar Garafuni da Sassaken Magarya, sai a tafasa, idan ya dan huce sai mace ta dinga kama ruwa da shi. Kullum sau daya. Yana maganin budewa da kaikayi.
- 2- A samu Garafuni da Sassaken Sanya sai a tafasa, mace ta dinga shan rabin kofi da safe, rabi da yamma. Ya na fitar da dattin mara da maganin farin ruwa mai wari.
- 3- A samu Furen Tumfafiya, sai a shanya ya bushe, a daka a dinga zubawa a cikin Nono a na sha. Ya na magance matsalar ruwan infection.
- 4- A samu Lalle da Ganyen Magarya da Kanumfari, a hada waje daya a daka sannan a tafasa a zuba farin miski a ciki. Idan ya dan huce sai ta shiga ciki ta zauna tsawon kamar minti goma. Yin haka yana maganin kaikayi da kuraje da budewa da dadewar gaba.
- 5- A samu Kabewa a dafa ta, bayan an dafa sai a tsame daga ruwa a jajjagata ko a birga, a zuba Madara ko Nono sannan a sa Zuma a sha. Wannan yana mganin rashin sha’awa da bushewa da rashin gamsuwa.
- 6- A dafa Zogale, idan ya dahu sai a murje shi ko a dama, a tace, a yi lemon juice da shi. Yana maganin fitar farin ruwa mai wari da cushewar mara kuma ya na kara ni’ima.
- 7- A samu Dan-Tamburawa da Albabunaj a tafasa a zuba Man Hulba a ciki. Sai ta dan tsuguna tururin ya dinga shigarta. Idan ya dan huce kuma sai ta shiga ciki ta zauna. Zai magance mata kaikayi da kuraje kuma ya na sa matsewa.
- 8- A samu Farar Albasa da Kanumfari da Citta da Malmo da Barkono da Raihatul Hubbi, sai ta da ke su ta yi yaji ta dinga cin abinci da shi. Ya na saukar da ni’ima da magance duk matasalolin sanyi.
- 9- A samu Sabulun Zaitun da Sabulun Habba sai a daka su. A samu ganyen Magarya da Garin Bagaruwa a daka a tankade. Sai a zuba akan sabulan da aka daka sannan a kwaba da Ma’ul Khal, a zuba Man Tafarnuwa da Farin Almiski. Sai mace ta dinga kama ruwa da shi kullum sau daya. Da ruwan dumi amma ake tsarki da shi. Wannan Sabulu ya na maganin kuraje da kaikayi da fitar wari.
- 10- A samu Man Zaitun da Man Habba da Man Tafarnuwa da Man Kanumfari sai a hade su waje daya. Mace ta dinga shan cokali daya kullum kafin ta karya. Ya na wanke dattin mara kuma ya na samar da ni’ima.
- 11- A samu Ciyawar Kashe-Zaki da Farin Magani sai ta hada waje daya ta dinga jika rabin karamin cokali ta na sha. Sannan ta dinga shan Man Zaitun Cokali daya kullum kafin ta karya. Wannan ya na maganin dattin mara da wanke daudar mahaifa.
- 12- A bare tafarnuwa, idan za ki kwanta bacci sai ki dauki sala daya ki yi matsi dashi, ana son idan mace za ta yi wannan hadin to miji ya daga mata kafa wato kada ya kusance ta, Da safe sai ta tafasa garin hulba ta zauna a ciki zata yi hakan har tsawon kwana uku.
- 13- Ki hada hulba da bagaruwa guri daya, ki dafa idan ruwan ya sha iska sai ki zauna a ciki, kuma ki samu man habbatussauda ki yi matsi da shi. Ni’ima Ba Sassauci Da farko daki samu kadarki wadda ba ta fara kwai ba. Sai ki dare hanjinta ta cikin dunbutu tunda ba a bukatar a yi mata gunduwa-gunduwa. Sai ki gyara ridinki (kantu) ki shanya ya bushe sai ki daka shi. Kina iya tafasa kadar sannan sai ki duba ridin ta cikin dunbutun kadar. Sai ki samu abu ki daure dumbutun; sannan ki hada kayan miya kadan sai ki kara duba nonon rakumi a cikin kayan miyar ki hada ki dafa har sai sun dahu sai ki sauke. Sannan a ranar ki jika kanumfari ya jiku sosai. Ya dama ruwan shanki.
- Kunun Zakin Dabino: Za ki sami dabino mai kyau ki cire ki tsabtace shi, saiki jika har sai yayi taushi sosai sai ki markada a blander , kisaka zuma ko suga kadan da madarar ruwa, asa yayi sanyi sai ki sha.
- Jan Hankali Ga Mai Matsalar Bushewar Farji:
- Sirrin Bushewar Farji:
- ’Yar’uwa ga dama ta samu, idan ki na fama da bushewar farji, a koda yaushe to sai ki sami man zaitun da man habbatussauda, sai ki hada su wajen daya, ki dinga shafawa a cikin farjinki insha Allah Zaki ga biyan bukata, domin kowace cuta tana da magani, sai dai in baki nema ba, amma in kika nema Zaki samu.
INA MAFITA
Mu'jizar da ke cikin Zaitu
Amfanin Man zaitun Ciwon Ciki: Duk mutumin da yake ciwon ciki sai ya samu man zaitun kamar cikin cokali ya hada da garin habbatus saud...
-
MAGANIN SANYI MAZA DA MATA 1. ALAMOMIN CIWON SANYIN MARA NA MATA / SANYIN MATA WANDA AKE YAƊAWA TA JIMA'I* 📗📗📗📗📗📗📗📗📗...
-
KARIN HIPS (DUWAWU) Kafin kiyi amfani da maganin karin hips Abinda ya kamata kifara sani shine yaya yanayin jikinki yake? Ya dace ki...
-
MAGANIN KARFIN MAZA(MEN POWER) DA NAMIJIN GORO. A DAURE A JARRABA YANA YI FA!!! A yau zamuyi bayanin hanyar da za'a bi domin samun k...



