Sunday, July 19, 2020

Na'a na'a

Amfanin Na'a na'a a jikin Dan adam.

Tana magance matsalar bacin ciki da rashin fitar bahaya mai sa tsugunno a bayi. A yi shayin na’a-na’a ko a zuba manta cikin shayi marar madara sai a sha.

Tana saukake narkewar abinci.

Ta kan taimaka wajen narkar da abinci yadda sassan jiki za su yi amfani da shi.

Tana maganin mura da tari da kuma mura mai damun makoshi. A yi amfani da man na’a-na’a ko ganyen, a tafasa ganyen a yi shayi marar madara, haka kuma, za a iya amfani da man na’a-na’a cikin ruwan zafi, a yi turiri, a lullube da mayafi. Wannan shi ma yana maganin mura ana bude baki yadda tiririn zai shiga cikin makoshi, domin shigar tasa ce za ta sa a samu saukin murarar.

In kuma akwai majinar kirji duk zai taimaka wajen fitar da ita, ya washe kirjin tare da makogwaro.

Maganin ciwon kai. A shafa manta wajen da kai ke ciwo. Maganin ciwon jiki. A shafa manta ga jijiyoyin jiki dake ciwo ko wajen dake damunka da ciwo, za a samu sauki in sha Allahu.

Maganin ciwon hakori. A yi amfani da man na’a-na’a da auduga, a diga man ga auduga , sa’annan a lika ga hakori mai ciwon.

Maganin kaikayi. Za a iya shafa manta a wajen da yake kaikayin. Korar sauro. A shafa man na’a-na’a a ga jiki hannuwa da kafafu, sauro zai gujesu. Kashe tsutsar ciki. Taimakawa hanta wajen aiki. Rage yawan damuwa.

Tana hana damuwa, a tafasa ganyen na’a-na’a a yi shayi, ko manta a zuba a cikin kofin shayi, safe da yamma.

Tana taimakawa kwakwalwa wajen rike karatu da kaifin fahimta. A yi shayi da ganyen na’a-na’a a rinka sha da zuma.

Tana sanya girki yayi kamshin filebo. A yi amfani da ganyen wajen girki. Hakan zai taimaka wajen son cin abincin musamman ga wanda baya son cin abinci.




No comments:

INA MAFITA

Mu'jizar da ke cikin Zaitu

Amfanin Man zaitun Ciwon Ciki: Duk mutumin da yake ciwon ciki sai ya samu man zaitun kamar cikin cokali ya hada da garin habbatus saud...