Sunday, July 19, 2020

Amfanin zogale

ASSALAFY ISLAMIC MEDICINE CENTER


Amfanin zogale ga lafiyar dan adam:

1- Ana dafa ganyen zogale da zuma a sha kamar shayi domin maganin Olsa (ulcer).

2- Ana shafa danyen ganyen zogale

akan goshi domin maganin ciwon kai.

3- Ga wanda ya yanke ko ya sare ko wani karfe ya ji masa ciwo, zai shafa danyen ganyen zogale inshaAllah jinin zai tsaya.


4- Ga mai fama da kuraje a jiki, ya hada garin zogale da man zaitun ya shafa.


5- Ana sanya garin zogale akan wani rauni ko gembo domin saurin warkewa.


6- Sanya garin zogale a cikin abinci yana maganin hawan-jini da kuma karama mutum kuzari.


7- Ana dafa ganyen zogale tare da sa kanwa 'yar

kadan domin maganin ciwon shawara.

8- Ga mai fama da ciwon ido zai diga ruwan danyen zogale, haka ma mai fama da ciwon kunne.


9- Macen da ke shayarwa ta dafa furen zogale da zuma dan karin nono.


10- Wanda ke fama da yawan fitsari wato cutar Diyabetis ya rinka shan furen zogale da citta kamar shayi.


11-Idan aka tafasa furen zogale da albasa aka sha kamar shayi yana maganin sanyi.


12-Haka ma cin danyen zogale yana maganin tsutsar ciki ga yara.


13-Ana daka ganyen zogale da 'ya'yan baure a

sha da nono ko kunu yana maganinciwon hanta.

14- Ga mai fama da sanyin kashi ko wani kumburi

zai soya 'ya'yan zogale a daka su sannan a hada da man kwakwa (man-ja) sai a shafa.

15-A daka zangarniyar zogale da 'ya'yan da ke ciki tare da karanfani, citta, masoro da kuma

kimba domin karin karfin da namiji da sa masa kuzari, haka kuma yana karawa mata nishadi.

16- A daka saiwar zogale da 'ya'yan kankana a

sha da nono yana maganin tsakuwar ciki (Apendis).

17-Haka kuma idan mutum yana fama da ciwon

Aids zogale kan rage radadinshi ta hanyar shan ruwan dafaffen zogale.

18-Haka kuma mai fama da Typhoid da malaria da kuma ciwon basir ko shawara, zai iya yawaita shan ruwan dafaffen zogalen domin samun sauki.



No comments:

INA MAFITA

Mu'jizar da ke cikin Zaitu

Amfanin Man zaitun Ciwon Ciki: Duk mutumin da yake ciwon ciki sai ya samu man zaitun kamar cikin cokali ya hada da garin habbatus saud...