AMFANIN SHAN KANWA GUDA GOMA
Kanwa ta kasance daya daga cikin ma'adinnan da ake samu a cikin wasu gulabe a kasashen Africa wacce ta kasance ita ba bishiya ba,ba wani ganye ba,amma kuma wata hikima ta ubangiji tana da wani alfano na daban.
A Turance ana kiranta da suna potash,yarbawa suna kiranta da kaun,su kuma Igbo suna cewa da ita akanwu.Tana daukeda minerals irin su leonite,kainite,glaserite,longbeinite,potassium sulphate.
Shafin ciwo da magani yayi nazari akan kanwa da amfaninta da kuma illolin da take iya haifarwa.
Ga bayanin a takaice
1.kanwa na kontarda kornafi ko tashin zuciya.Idan dattin ciki yaiyi yawa a cikin mutum yakan iya haifar da tashin zuciya.Idan hakan ya faru to sai a nemi kanwa a jika a sha.inshaAllahu za a sami sauki.
2.Kabewar ciki : Idan ka ci abinci amma sai cikin naka ya kumbure to sai ka nemi kanwa da ruwa masu kyau ka jika ka sha sau biyu a cikin sa'oi uku.
3.Ciwon ciki : A wasu lokutan haka kawai zaka ji cikin naka na murdawa ko yana ciwo ka rasa sanin dalili.Anan za ka iya neman kanwa ka jika ka sha.
4.Saurin narkarda abinci: Wasu sukan dauki lokaci mai tsawo suna fama a bayan da suka ci abinci wanda baya saurin narkewa sai a dauki lokaci mai tsawo ciki a takure.Matsala irin wannan sai a nemi kanwa a sha.
5.kanwa na rage yawan bugun jini
6.kanwa na rage tsamin abinci.Idan abinci yaiyi tsami kamar miyar tumatir ko wani ganye haka to sai a jefa kanwa kadan zata daidaita tsamin ya zamo daidai da yanda ake bukata.
8.Idan yaro karami wanda baya iya magana,ko jinjiri (baby) na ta faman kuka aka rasa gane abinda ke damunsa to a nemi kanwar jarirrai a gasa a wuta sai a jefa a cikin ruwa a karamin cup idan ta jika (medium solution) sai a karanta fatiha kafa goma a tofa a bashi ya sha.InshaAllahu za a dace.
10.Taurin bayan gari da yawan sakin iska sanadin wata matsala.Sai a nemi kanwa a jika da ruwan dumi a zanka sha a hankali.
To miye illolinta ?
Yawan shan kanwa na ragewa namiji yawan maniyi.Wannan binciken da wata likita mai suna Mr Ochuko Erukainure ta tabbatar kenan.A dan haka bata shawarci maza da suyi amfani da kanwa ba.
A wani bincike da wasu masana harkar magani da hadin huiwar biochemistry department dake a Bells University a Ota ya nuna cewa shan kanwa na illata matse matsin namiji ta yanda zai iya hana haihuwa.
Sun kara da cewa a sanadin yawan sodium dake tare da kanwa yawan shanta na iya janyo rauni ko wani lahani ga koda da kuma hanta.
Idan dai aka kiyaye da yanda ya dace a sha kanwa kada a yawaita shanta.to ba wani illa da zata haifar.
Sun kara da cewa a sanadin yawan sodium dake tare da kanwa yawan shanta na iya janyo rauni ko wani lahani ga koda da kuma hanta.
Idan dai aka kiyaye da yanda ya dace a sha kanwa kada a yawaita shanta.to ba wani illa da zata haifar.
No comments:
Post a Comment