AMFANIN GANYEN AYOYO GUDA GOMA SHA BIYAR
Ganyen Ayoyo muhimmin ganyene da ake amfani da shi a sassa daban daban a cikin duniya.
- A arewacin Nigeria ana miyar ganyen ayoyo tare da tuwon masara.
- A kasashen Yarbawa suna kiran ganyen ayoyo da Ewedu,suna shan miyar da tuwon gari waton (amala).
- A kasar India,suna kiran ganyen ayoyo da 'Naltag sag' suna sarrafa ganyen su yi abinci,su yi miya,kuma su yi amfani da busashen ganyen dan maganin wasu cutuka a yankunansu.
A kasar Egypt,da wasu yankuna na kasashen Larabawa suna kiran ganyen ayoyo da suna Malakhiyah.kusan a duk kasar Egypt ana amfani da ganyen ayoyo (Egyptian national dish) saboda amfaninsa ga lafiyar jiki kamar yanda binciken shafin ciwo da magani ya tabbatar.
To ko miye amfanin ganyen Ayoyo ?
Ganyen ayoyo na daukeda sinadirran betacarotene,iron,calcium,vitamin C,vitamin A,vitamin E,Riboflavin,folate,fiber,niacin.
Wadannan sinadirran suna da matukar muhimmanci sosai wajen kare jiki da yaki da cutuka.
Sinadirran Vit.E da C da kuma A da ake samu a cikin ganyen ayoyo suna yakar kwayoyin cuta daga ciki harda kwayar ciwon daji (cancer cells).
- Ganyen ayoyo na daukeda sinadirran collagen masu gyaran fatar jiki.
- Ganyen ayoyo na daukeda fibre dake taimakawa dan rage kiba (weight loss).
- Ganyen ayoyo na wanke ciki da maganin bahaya mai tauri.
- Ganyen oyoyo na karfafa sinadirran jiki dake aikan yaki da kwayoyin cuta a jiki.(boosts immunity).
- Ganyen ayoyo na karfafa lafiyar ido a sanadin sinadirran vit A da carotene.
- Ganyen ayoyo na samarda karfin hakora da karfin kassan jiki.
- Ganyen ayoyo na rage hauhawan jini.
- Ganyen ayoyo na kona kitsen dake taruwa a cikin jini har yakai ga shafuwar lafiyar zuciya.
- Ganyen ayoyo na magance basir idan aka hada da cumin extract.
- Ganyen ayoyo na kara lafyar mahaifa ga mata.
- Ganyen ayoyo na kara lafiyar jiki da jini.
- Ganyen ayoyo na magance ciwon sanyi (std)
No comments:
Post a Comment