RASHIN ZUWAN
JININ AL’ADA (HAILA) AKAN LOKACI
Barkanmu da warhaka. Yau zamu yi bayani akan matsalar da dama
daga cikin Mata suke fama da shi, wato: rashin zuwan jinin haila akan lokaci. Mata
da yawa su kan fama da wannan matsala, wata sai tayi wata daya bata ga jinin
Hailan ta ba, wata kuma sai tayi wata uku sannan zata gani, wasu lokutan sai ya
rika mata wasa.
KADAN DAGA CIKIN DALILAN DA YAKE HAIFAR DA HAKA
*Dalilin da yake janyo da irin wannan matsala shi, duk macen
da take FAMILY PLANING zata iya fuskantar daukewa al’ada ko kuma hailan ya rika
mata wasa, yak an sa jinni yazo ma wasu Matan a wata sau 3
*Yanayin zafin rana ko irirn abincin da ake ci ko ake sha
yakan haifar da zuban jinni da yawa ko kuma rashin sa
*Mata masu fama da matsalar Jinnul Ashiq, sukan fuskanci da
rashin zuwan jinin al’ada ko kuma yawan zuban sa har tsawon wata 1 ko sama da
haka. Dalili kuwa shine irin wannan Jinnu idan baya son Matan ta dauki ciki
balantana ta haihu sai ya haifar mata da irin wannan matsala….
Jinnul Ashi1 sukan shiga jikin Mace ta hanyar sihiri (Asiri),
wasu lokutan kuma sukan shiga ta karan kansu a lokacin da suka ga Mace bata
suturta jikinta da tufafin da ya dace……
SHAWARA
Macen da take fama da wannan matsala na rashin zuwan al’ada,
na farko ta fara tuntubar likita, a gwada ta a tabbatar da abinda ya haifar da
shi. Kada taje chemist, kada ta fara shan magungunan gargajiya har sai ta fara tuntubar likita. Idan suka tabbatar mata
da matsalar, ta gane wani iri ne, anan kodai ta karbi magani daga Asibiti ko
kuma ta dawo gida tayi na gargajiya, tunda yanzu ta san matsalar ta, ko kuma
tayi na Musulunci.
MAGANI
Maganin Musulunci guda daya wadda tak zamu bayar don ki gwada idan
kina fama da irin wannan matsala shine kamar haka:
1.
KUSTUL HINDI (قسط الهند)
2.
SHAJARATU MARYA (شجرة مريم)
YADDA ZA AYI AMFANI DA SHI
Za a jika Shajaratu Maryam din a ruwa sai a debo garin Kustul
Hindi cokali 3 a hada ciki, sai a barshi yayi 24hrs kafin a fara sha cokali 3
bayan kowace aya 3.
Insha Allahu za a dace.
Note: hanzari ba gudu ba, ita mai fama da matsalar jinnu,
tabbas sai anyi mata Ruqya sannan Malamin ya dora ta akan maganin da ya dace.
Sai a karo nag aba zamu kawo muku bayani akan wace jininta
yake zarcewa, baya tsayawa inshaAllahu.
No comments:
Post a Comment