Amfanin 19 da Na'a-na'a ke yi ga Lafiyar Dan-Adam
Shekaru aru-aru da suka shuda al'ummu daban-daban ke amfani da Na'a Na'a, domin inganta lafiya. Misali a yaren Girka ana kiran na'a-na'a da 'Mentha' wanda ke nufin magani. Wannan shi zai nuna wa mai karatu cewa, an dade ana amfani da ita wajen kawar da matsalolin jikin dan-Adam.
Tarihi ya tabbatar da cewa, Rumawa Sun Kasance suna zuba ta cikin Ruwan wankasu ba don komai ba sai don sanin fa'idarta wajen samar da lafiyayyiyar fata, sannan su na yin amfani da ita wajen gusar da warin baki musamman lokacin da suka ci abinci mai wari dangin albasa, tafarnuwa da sauran su. Baya ga haka sun kasance suna yawaita sanya ta cikin abinci da abin shansu, musamman ma cikin girke-girkensu.
Tun a shekarun da suka gabata, jama'a su ka gano tasirinta wajen Maganin Mura, da warkar da Cutukan da kan shafi fatar Jikin bil-adama.
Ba tare da mun tsawaita ba, za mu tafi kai tsaye ga wannan maudhu'i, mai taken amfanin Na'a-na'a ga lafiyar dan-adam.
1. Taimaka Wa Mata Masu Juna Biyu.
Wasu matan masu ciki kan fuskanci matsaloli irin su amai, tashin zuciya ko kuma yawan zubar da yawu. Duk mai fama da daya daga cikin wadannan matsaloli za ta iya amfani da ganyen na'a-na'a don samun sauki.
Abin da za su yi abu ne mai sauki kwarai da gaske, kawai su samu ganyenta su wanke shi da kyau su rinka taunawa, ga mai yawan zubar da yawu, ta sanya a bakinta ta kyale shi zai kawar ma ta da yawan zubar da wannan yawun. Hakanan, mai junan dake fama da amai za ta iya dafa na'a-na'a kamar shayi ta sha.
2. Maganin Kurajen Fuska.
Wannan wata matsala ce da ta fi addabar matasa maza da mata. Albishir ga ma su fama da wanan matsala, ko kuma wadanda ke gudun samuwar kurajen fuska don kuwa za su iya magance hakan ta hanyar yin amfani da na'a-na'a.
Yawaita amfani da Na'a Na'a kan hana fesowar kurajen fuska wato riga-kafi kenan, idan kuma kurajen sun feso a fuska sai mai fama da hakan ya yi amfani da manta. Insha Allahu ta hanyar shafa manta zai samu sauki, musamman ga masu fama da maikon fuska.
3. Maganin Mura.
Ga dukkan wanda ke fama da mura, matukar ya yi amfani da man na'a-na'a zai samu sauki cikin yardar Allah. Abin da zai sai ya samu manta, ya Sha Cokali 2 da safe da rana sannan da dare wato, sau 3 kenan a yini, ko kuma ya samu busasshen ganyenta ya yi hayaki da safe da yamma. Ga mai son ya yi amfani da gabyen kuma, zai iya zuba ta a shayi, ya sha safe da yamma. Sai dai zai hada da tafarnuwa, citta da lemon tsami. Hakanan za'a iya hada na'a-na'a da zuma a sha don maganin mura.
4. Ciwon Kai.
Idan ciwon kai ya addabe ki, sai ki samu danyen ganyen Na'a Na'a ki shafa, in Allah ya so, zata magance matsalar.
5. Maganin Warin Baki.
Idan mai karatu ya tuna a sama mun bayyana cewa, kabilar romawa na amfani da ita wajen tsaftace bakinsu, musamman idan sun ci nau'in abinci mai wari. Har ya zuwa wannnan lokaci ta na nan da wannan tasiri. Ga duk mai bukatar bakinsa ya kasance cikin kamshi kuma ya samu daddadan numfashi sai ya yawaita shan ta saboda ta na sanya baki ya dauwama cikin kamshi a kowane lokaci.
Wata hanyar kuma, ita ce, za'a iya cin ganyenta kamar sau 3 ko 4 a mako, hakan zai dauwamar da baki cikin kamshi, kuma wani abin sha'awa shine, yawaita hakan na magance ciwon hakori ya sanya dadashi ya yi lafiya, ku ma koda ya na zubar jini zai daina cikin hukuncin Mai-duka.
6. Gyaran Jiki Da Muhalli.
Idan mutum na son jikinsa ya kasance cikin kamshi, to sai ya samu busasshen ganyen na'a-na'a ya rika yin hayaki da shi, saboda yawaita hayaki da busashshen ganyenta na sanya kamshin jiki da kuma muhalli, wato wajen da aka yi turaren ko hayakin shi ma zai kasance cikin kamshi.
7. Hasken hakori.
Baya ga tsaftace baki da gusar da warinsa da take yi, hakanan amfani da ita kan sanya hakora su yi haske. Domin samun wannan fa'ida sai a samu busasshen ganyenta a rinka goge hakora da shi, za'a ga abin mamaki da yardar Ubangiji.
8. Samar Da Kuzarin Jiki.
Wannan tsiro mai albarka kan samar da kuzarin jiki da nishadi. Domin samun amfanuwa daga wannan aiki nata, sai a hada na’a-na’a da zuma a ke sha, hakan zai samar ma da kuzarin jiki sannan ya samar da nishadi. Idan kuma kasala ce ta addabi mutum sai ya samu man na'a-na'a ya ke shaka a hankali ko kuma a samu manta a zuba cikin ruwa a shiga cikin tsawon mintuna 15, hakan na magance kasala ko gajiyar da ake fama da ita.
9. Ciwon Ciki Lokacin Al'ada.
Wasu matan kan yi fama da ciwon ciki yayin da suke al'ada, to idan kina daya daga cikin ma su fama da wannan matsala, da zarar kwanakin al'adarki sun cika sai ki tanadi na'a-na'a, duk lokacin da ki ka fara jin alamun ciwon sai ki dafa na'a-na'a kamar shayi kina sha. In sha Allahu za ki samu waraka.
10. Maganin Kumburi Da Cushewar Ciki.
Idan aka samu cushewar ciki ko kuma cikin ya yi irin kumburin nan da aka kasa yin bayan gida sai a samu ganyen na'a-na'a a dafa shi kamar shayi ana sha bayan kammala cin abinci, za'a samu sauki idan Allah Ya yarda.
11. Karin Kaifin Basira.
Ina daliban ilmin addini da na zamani, wannan hadin naku ne. Duk dalibin dake son Kwakwalwarsa ta bude, sai dimanci shan wannan hadi da za mu ambata. Ana son a sami zuma mai kyau marar hadi, da man na'a-na'a da kuma ruwan khal. Bayan ya sami wadanan abubuwa sai ya hada su waje guda ya ke sha. Da yardar Allah, za'a ga abin al'ajabi.
12. Shan na'a-na'a na da kara lafiyar hanta wajen taimaka ma ta yin aikinta yadda ya kamata.
13. Ta na taimaka wa wajen narkar da abinci dalilin haka ya sa take magance matsalar kumburi da cushewar ciki.
14. Ta na inganta aikin zuciyar dan-adam, wanda hakan kan bayu wajen karfafa zuciyar ta zamanto cikin koshin lafiya koda yaushe.
15. Maganin toshewar hanci zai iya rabuwa da shi, ta hanyar yin sirace da ita.
16. Yawan shan na'a-na'a na kashe tsutsar ciki.
17. Shafa man na'a-na'a a hannaye da kafafuwa na korar sauro.
18. Yawaita shan shayin na'a-na'a na magance shiga damuwa, ya na hana shiga damuwar rigakafi kenan, sannan ya na rage ta, idan har mutum ya tsinci kansa cikinta.
19. Shafa manta a wajen dake kaikayi na magance shi.
No comments:
Post a Comment