Matsalolin Ciwon Sanyin-Mata /Sanyin Gaba da Rigakafi
SANYI kalma ce mai fadin ma'ana da Malam Bahaushe ke yin amfani da ita domin yin kokarin bayanan wasu matsalolin lafiya na daban-daban , misali , ciwon-sanyin jiki [rheumatism], ciwon sanyin mura [cold and flu] da ciwon sanyin-mara ko ciwon sanyin-mata ko ciwon sanyin maza-da-mata da ake dauka ta hanyar jima'i [STDs/STI da sauransu. Saidai Malam Bahaushe baya kiran ciwon sida/kanjamau da ciwon sanyin-mara duk da cewa kau anfi yada cutar ta jima'i.
Za muyi bayani akan ciwon sanyin-mata ne kadai. Matsalolin ciwon sanyin-mata, infections or wasu cututuka ne ko matsaloli dake addabar gaban mace, wato cututtuka masu sanya kaikayin farji, ko radadin ciwo, kumburin gaba ko warin gaba , zubar farin ruwa, kurajen farji, zafi wajen yin fitsari ko wajen yin jima'i da sauransu. Ciwon sanyin-wata matsala ce dake faruwa ga mata da dama a cikin wasu lokutta na rayuwarsu. Ana samun wannan cututtuka ko matsaloli sabili da wani sauyin yanayin jiki da mata ke samu wasu lokutta da kuma sabili da wasu kwayoyin halittar 'bacteria' da 'fungus' dake zaune cikin al'aurar mace, haka kuma , mata na iya samun wannan ciwon a lokacin juna-biyu da kuma shayarwa,Har ila yau, za'a iya samun ciwon ta hanyar jima'i da wasu dalilan ko hanyoyi na daban.
Nau'in ciwukan sanyin-mata suna da yawa, to amma bincike ya nuna cewa ciwon sanyin-mata nau'i uku ne (3) suka fi addabar mata da yawa. Za muyi bayani akansu kadai, a takaice insha Allahu, sune kamar haka: (sunayen su da yaren turanci)
1.kwayoyin halittu masu haddasawa.
2. Cuta mai shafar farji.
3. Cuta mai yaduwa lokacin jima,i

1. Kwayoyin hallittu masu haddasawa Akwai wasu kwayoyin halittun 'fungas' (masu suna 'candida') sune ke haddasa 'Yeat infection'. Su wadannan halittu wanda kwayar idon mutum baza ta iya ganin suba , saboda kankaantar su saida taimakon madubin likita ne za'a iya ganin su [microscope] . Halittun suna rayuwa a wasu wurare cikin jikin mutum kuma adadinsu baya da yawa . Ana samunsu cikin farji kuma, asali basu cika cutarwa ba.'Candida' suna san wuri mai gumi, lema da rashin iska domin girma da yaduwa. Idan suka samu wannan yanayi da suke so toh za suyi yawa su kuma haddasa ciwon sanyin 'Yeast infection'. Anfi yawan samun irin wannan ciwon sanyi ga mata da yawa , kusan kashi 75 cikin 100 na mata sun taba samun wannan ciwon a cikin wasu lokutta na rayuwarsu. Alamomin cutar sun hada da: zubar farin ruwa mai kauri daga farji, kuraje ko kaikayin farji da kuma labban farji suyi jawur ko cikin farji.

2. Cuta mai shafar farji cuta ce dake shafar farji sabili da girman wasu kwayoyin halittun 'bacteria' masu cutarwa dake cikin farji suna rayuwa. Alamonin cutar sun hada da: zubar ruwa mai 'karnin kifi daga farji, warin sa musamman lokacin jima'i, ko radadin zafi lokacin fitsari, amma babu kaiyayi cikin alamomin. Alamomin cutar kuma na iya 'buya.

No comments:
Post a Comment