Saturday, May 30, 2020

INFECTION NA MAZA DA MATA

​MAGANIN CIWON SANYI NA MATA

Hakika ciwon sanyi na mata yana daga cikin cututtuka masu wuyar magani, kuma mata da yawa suna shan fama dashi.

Ga wata fa’idah nan daga ZAUREN FIQHU ku jarraba, In sha Allahu za’a samu waraka.

ANEMI:

1. Garin Tafarnuwa. 

2. Saiwar Raihan (Doddoya – Rai dore) 

3. Garin Kanumfari da citta. 

4. Saiwar Zogale.

Wadannan abubuwan gaba daya ahadasu adakesu waje guda, sannan arika diban cokali guda ana dafawa ana sha kullum safe da yamma.

Sannan adebi wani ahada da barkono ayi yaaji dashi arika cin abinci. In sha Allahu koda sanyi yayi shekara arba’in ajikinki ko fiye da haka, zaki warke.

Hakanan Mazaje masu fama da matsalar Sanyin mazakuta, Idan sukayi wannan hadin zasu samu waraka da izinin Allah (SWT).


No comments:

INA MAFITA

Maganin Maza

ASSALAFY ISLAMIC MEDICINE CENTER