ILIMIN JIMA'I NA 01
RASHIN GAMSAR DA UWARGIDA / AMARYA INA
MAFITA
A kullum na duniya maza ma'aurata suna saduwa da
matansu, sai dai kuma abun tambaya anan shine, maza nawa ne suke iya gamsar da
matayen nasu a lokacin da sukayi kwanciyar ta jima'i? Maza nawane
magidanta suke da illimin sanin yadda zasu gamsar da matansu..?
Ko munki ko munso babu yadda zamu kaucewa magana
a kan jima'i domin shine ginsheken zaman aure kuma yana cikin manyan lamuran da
kan iya sa a samu zaman lafiyan ma'urata ko akasin hakan. Yana da kyau da kuma
mahimancin maza su fahimci cewa, duk wata mace tana sha'awar ganin cewa mijinta
yana matukar gamsar da ita yayi da suka yi kwanciya ta jima'i.
Sai dai kuma abun ban haushi, maza da dama suna
daukar cewa gamsar da mace a jima'ince shine saduwa da mace da karfi ko kuma da
mugunta ko jigatata, shine zai iya gamsar da mace.
Mafiya yawan maza basu da illimin
sanin cewa mace takan dauki lokaci mai tsawo kamin kawo (inzali), duk da yake da
akwai wasu matan da suke yinsa cikin karamin lokaci. Don hakane yake da kyau
maza su gabatar da wasanni ga mace kamin su afkamata.
Kamin mace ta kamu, dole ne sai an tattabamata mata wasu wurare ta hanyar
sumbata, wasa da nonuwanta, gabanta da makamantanmsu.
A wannan lokacin ne mace jinin jikinta yake bin
ko ina a jikinta daga nan kuma sha'awa ya motsomata harta nemi bukatar mijinta. Mundin namiji ya jefa matarsa cikin
wannan yanayi zai ji dadin yin jima'i da ita haka kuma ita kanta matan bazata
yi koken rashin gamsuwa bayan an gama, maza masu murza matayensu a lokacin
wasannin motsa sha'awa, mazane da suke sa matansu gamsuwa da zuwan kai cikin
sauki kuma akai akai. Kada kayi gaggawar shigar matarka, ka tabbatar ka dauki
lokacin kamar mintuna 25 zuwa 30 kana wasa da ita har sai lokacinda tayi laushi
da kanta tana bukatar ka shigeta.
Mata da dama dai sukanyi sha'awar gani
mazansu ne ke tubesu da kansu a lokacin da ake
tsaka da wasan, yadda kuma a yayi wasan kana tube mata kayan dake jikinta daya
bayan daya kamin kashiga wasa da muhimman wuraren dake motsa mata sha'awa. Da yake bazan yi bayani dalla-dalla na
yadda ake wasa da mace da kuma wuraren da ake wasan dasu ba a wannan shafin,
yanada kyau maza su fahimci cewa ko wace mace da inda ke tayar mata da
sha'awarta.
Wata da zaran an soma shan bakinta
sha'awata ya motsa, wata kuma wasa da gabanta, wata murza kan nonuwanta watama
kunnenta kawai za'a taba ta fara diga, dole ne kowani magidanci ya fahimci meke
tayarwa matarsa sha'awa a lokacin wasanni. Mahimmancin wasa da mace kamim soma
jima'i shine, zai sata ta soma fitar da ruwa wanda ruwan yana taimakawa shigar
azzakari cikin farjin mace da sauki.
Haka kuma yana taimakawa mace tayi zuwan
kai cikin sauki ba tare da ta dau lokaci ba. Girman azzakari, ko tsayinta bashi
ne abu mafi mahimmanci ba a wajen mace, abun da kawai yake sa mace ta samu zuwan kai da kuma gamsuwa a yayin
jima'i, shine yadda aka motsa mata sha'awarta a lokacin da ake wasa da ita
shine abunda yake sata nan take ta samu zuwan kai da kuma gamsuwa irinta
jima'i.
Babu saduwar jima'i mafi dadi wajen mace irin
tayi zuwan kai lokaci guda da mijinta, wanda bincike ya nuna cewa maza 100, 30
ne kawai suke iya yin zuwan kai lokacin daya da matansu, hakan kuma yana
samuwa ne ganin yadda suka lakanci jima'i da matan nasu.
Shi dai zuwan kain 'ya mace, shine
kololuwan jindadin kwanciyar jima'inta, kuma shine yake jawo gamsuwarta a
jima'ince, don haka da zaran wasu matan sun samu gamsuwa to sha'awarsu ta
jima'i kuma ta kare a wannen lokacin, duk kuwa da wasu matan da ake samunsu
suna iya zuwan kai kamar sau biyu zuwa biyar a kwanciyar jima'i guda, hakan
yana danganta ne da irin halittan macen da kuma yadda mijinta yake sarrafata a
jima'ince.
Shi dai zuwan kai 'yan mace ba kamar na miji bane, domin shi namiji
idan yayi zuwan kai abune da ake iya ganinsa a zahiri saboda yadda maniyi yake
fita daga azzakarinsa. Wassu na daukar cewa, ruwan dake
fita daga gaban mace a lokacin saduwa da ita Ruwa iri biyu ne yake fita a gaban mace a
lokacin da ake wasa da ita wani ruwa mai yauki ne yake soma fitowa, wanda yake alamta cewa ta soma kamuwa kenan, haka kuma idan
ana saduwa da ita kuma da akwai wani farin ruwa wanda yafi kama da madara shima
yana fita daga gabanta, shima wannan bashi ne alaman mace tayi zuwan kai ba. A
lokacin da mace tazo kawowa, a wannan lokacin kamanninta sukan canza,
numfashinta yana yawan bugawa da sauri, haka kuma jinin jikinta guduwarsa na
karuwa sosai haka kuma jijiyuyin jikinta zasu kara bayyana yayin da zata yi
wani kara ko kuka ko fadan wata kalmar dabata sanshi ba a yayi zuwan kan nata,
haka kuma mata da dama suna kankame mazajensu a lokacin da suke zuwan kan.
Da akwai yanayin
kwanciya na jima'i da yake taimakawa mata domin yin zuwan kai cikin sauki a
lokacin jima'i, sai dai kuma ganin babu shafuka da zamu kawo komai da komai a
wannan mujallar, nake baiwa ma'aurata su nemi littafi mai suna jima'i domin
ma'urata wanda zai fito nan bada jimawa ba a kasuwa.
Sai dai kuma kamin wannan
lokacin, ya kamata maza su fahimci cewa da akwai illa ga duk namijin da bazai
iya gamsar da matarsa ba a jima'ince, don haka ne nake bada shawara ga maza su
nemi sanin illimin yadda zasu
iya sarrafa mata.
**********************************************

No comments:
Post a Comment