Sunday, May 31, 2020

Cututtuka guda goma (10) masu halakarwa

CUTUKKA GUDA (10) DA AKE DAUKAN SU TA HANYAR JIMA'I, KIN KUWA SANSU?

 

Akwai cutuka da dama da ake dauka ta hanyar jima'i masu matukar lahanin gaske ga lafiya.

Ga kadan daga cikinsu :


 

1.Gonorrhoea: Ciwon sanyine mai ta'adi wanda yakan kama mace ko Namiji ta hanyar jima'i da wanda ke dauke da qwayar cutar,masu aure ko wadanda basu da aure.

Tana da alamu kamar haka

  • Tana haifarda fitar farin ruwa ga al'aura,wani lokaci suna da wari kamar na danyen kifi.
  • Tana sanya fesowar quraje ga matse matsi ko a gaban mace,ga qaiqayi ko yaushe hannu a cikin wando.
  • Tana shanye ni'imar mata ya kasance mace bata da wani ni'ima na zamanta 'ya mace.
  • Tana zuqe girma da kaifin takobin namiji,takobin mai gida zai kasance baya da kaifin yankan ko albasa balle nama.
  • Tana janyowa mace kyama ga mijinta.

Idan ba'a yi saurin maganceta ba to tana hana haihuwa(sterile)

tana tsinke maniyin namiji ya koma ruwa zalla(watery sperm fluid)

tana sanya ciwon gabobin jiki da yawan ciwon kai,dama qugin ciki

 

2.CHLAMYDIA : kamar ciwon sanyi yake amma ya banbanta kadan da sanyi kuma kwayar cutar dake kawo su ba iri daya bane.
Yana haifarwa mace zubar fararen ruwa,watarana harda jini,da qaiqai da zafin saduwa da kuma yayin fitsari,shima idan ba'a dauki mataki ba to yana hana haihuwa ga mace ko namiji (infertility)

 

3.Syphillis : Da Hausa ana kiransa da suna tunjure,ya janyo qurajen gaba ga mace ko namiji,ko kuraje ga dubura,ko baki,tana shafuwar qwaqwalwa da idanu da kunnuwa da zuciya.
Za mu tattauna kan syphililis a post dinmu na gaba.

 

4.H.I.V/AIDS : Dan qanjamau,yana janyo rama,gudawa,quraje a cikin baki,quraje ga al'aura,ga kasala,tari da yawan rashin lafiya da makamantansu

 

5.HERPES SIMPLEX VIRUS,waton wasu qurajene zasu iya fitowa a wajaje daban daban kama daga cikin baki,ko akan le66a ko a cikin hanci ga al'aura ko maqogwaro,suna da zafi kuma suna mata jin ciwo a yayin saduwa.

 

6.Candida Balantis : Wani qurji ne dake fitowa akan zakari ko kaciyar namiji ya girma,ya janyo zubar ruwa yayin fitsari da jin ciwo har a cikin jiyojin zakari.
Ga zuqewar zakari ya shi a cike ya koma kamar na dan shekara biyar.

 

7.Candidiasis : wata cuta ce da fungal ke haddasawa tana da wahalar al'amari dan maganita na asibiti yana bada reaction sosai da janyo wasu matsaloli dan anti fungal ne ake bada wa na sha dana shafawa.akoi ma nau'in cutar da ake kira vulvo viginal candidiasis,tana kama mata inda gaban mace zai rinqa fashew kamar ana sa reza ana yanke shi,zai yi ja ,ga zafin gaske.

Wannan cutar tana iya haddasa manya manyan quraje ko qanani ga al'aura ko dubura ko cikin baki,mahiyawa takan shafi masu ciwon H.I.V

 

8.HEPATITIES B DA C : waton ciwon anta ma na dauka ta saduwa da mai ciwon ko idan jinin mai ciwon ya gauraya da wanda baya da ciwon kota annura ko hatsari.

 

10.Trichomoniasis.

Duka dai ana daukar wadannan cutukkan ta wajen saduwa da mai ciwon.

To Ya ake kare kamuwa da cutukkan ?

  • A guji yin jima'i barkatai.
  • A kiyaye tsafta.
  • A daina saduwa da iyali lokacin al'ada
  • A daina sa gwanjo ba tareda an wake su ba,dan akan dauko kayan da karuwai masu curuta a jiki akawoma Hausawanmu.

Idan an ji alamun ciwo to a yi gaugawar neman magani.

A rin saka sutura mai tsabta kuma akiyayi zama da under wear ko gajeren wando na tsawon kwana biyu ba tareda an canza ko an wanke ba,dan akoi qazammu.

A daina shiga bayan daki kowane aka samu.

Idan ma za ayi jima'i da mai ciwon to a saka kariya.


No comments:

INA MAFITA

Maganin Maza

ASSALAFY ISLAMIC MEDICINE CENTER