Amfanin Hulba ga Lafiyar ki/ka
Yau insha Allahu za mu kawo muku bayani dangane da amfanin
Hulba ga lafiyar dan Adam. Hulba kamar yadda mu ka san ta, kalma ce ta larabci,
da harshen turanci kuwa ana kiran ta da 'Fenugreek'. Hulba wani tsiro ne
mai matukar amfani ga lafiya, kuma shekaru aru-aru da su ka shude al'umma ke
amfani da ita don samun waraka daga wasu matsalolin lafiya.
Jama'a na amfani da ganye da kuma kwayar hulba wajen samar da
magunguna tun a shekarun da su ka gabata. Hulba ta shahara a kasashe da
dama a duniya, sai dai anfi samun ta a wasu daga kasashen Larabawa musamman
kasar Misra, sannan ana samun hulba a kasar Sin da kuma Indiya.
A kasar Indiya su na kiran ta da, 'Methi' a yaren Hindu, a
yaren Telugu na Indiyan kuwa su na kiran ta da 'Menthulu'. Wani bincike da wata
kafar yada bayanai ta yanar gizo ta wallafa, ya nuna cewa, Hulba ta shahara a
kasar Indiya saboda amfaninta ga lafiya, ta yadda za ka iya kiran ta gidan kowa
da akwai.
A al'adance, mutanen kasar Indiya na amfani da kwayar hulba a
matsayin wani mahaɗin samar da magunguna, baya ga amfani da su ke da hulba don
samar da wasu hade-hade na inganta lafiyar jiki, da kuma yadda su ke amfani da
hulba don kula da lafiyar gashi.
Sai dai, binciken zamani na kwanan nan da masana su ka
gudanar a kan hulba ya nuna cewa, za ta iya samar da magunguna da hade-haden
inganta lafiya daga hulba, fiye da yadda jama'a su ka sani a baya. Daga cikin
amfanin hulba ga lafiya da masanan su ka gano, har da taimaka wa ma su ciwon
siga, ciwon ido, gyaran gashi da fata. Hakanan, ana amfani da hulba kan
matsalar basir, matsalolin ciki da sauran su.
Yanzu ga bayani daki-daki kan amfanin hulba ga lafiyarmu:
1. Hulba na hana Bushewar fata; Bincike ya tabbatar da cewa,
yin amfani da hulba na hana bushewar fata. Saboda haka duk mai fama da wannan
matsala ta bushewar fata zai iya amfani da hulba don maganin wannan matsala.
Yadda za a yi shine ya samu garin hulba, ya kwaba ta da ruwa,
amma kwaben ya yi kauri, sai ya shafa a fuskarsa, ya bar shi tsawon rabin sa'a,
daga bisani ya wanke.
2. Hulba na maganin Basir; Ga mutanen da ke fama da wannan
matsala ta basir, za su iya amfani da hulba su samu sauki cikin yardar
Ubangiji. Za a samu hulba a dafa, sai a sauke, idan ta huce sai a zuba zuma,
ake sha, musamman awa guda kafin a kwanta barci.
3. Hulba na maganin rashin ruwan nono ga mai shayarwa; A wasu
lokutan, akan samu mace ta haihu amma sai ta samu karancin nono. Yin amfani da
hulba zai samarwa da mai shayarwa ruwan nono, kuma zai taimaka wajen girman
jaririnta.
A kasashen da ke nahiyar Asia, mata kan yi amfani da hulba
don maganin matsalar rashin ruwan nono ga mai shayarwa. Masana sun ce, hulba na
taimakawa wajen samar da ruwan nono ga mata ma su shayarwa ne, sakamakon wani
sanadari mai suna 'phytoestrogen' da ta ke kunshe da shi. Ana samun wannan
fa'ida ta hulba ne, ta hanyar shan ta cikin ruwan shayi.
Ko kuma, mace ta samu 'ya'yan hulba ta dafa da man Ridi ta
dinga ci har tsawon kwana 3, sannan ta ke shafa man hulbar a nononta, In
Allah Ya so za'a samu biyan bukata. Domin kuwa za ta samu ruwan nono da zai
wadatar da jaririnta, kuma ya kasance cikin koshin lafiya.
4. Amfani da hulba na rage 'kwalastaral' (kitse marar kyau) a
cikin jini; Bincike ya tabbatar cewa, yawan amfani da hulba na taimakawa wajen
rage yawan kwalastaral a cikin jini, musamman marar amfani da ake kira 'bad’
cholesterol ko kuma LDL' da turanci.
5. Ana amfani da hulba wajen maganin cushewar ciki; Hulba na
taimakawa wajen saurin narkewar abinci, sakamakon haka sai ta ke maganin
cushewar ciki. Duk ma su fama da matsalar cushewar ciki ko kumburin ciki
sakamakon rashin narkewar abinci sai ya dimanci amfani da hulba, zai samu
afuwa, insha Allahu.
6. Mata na amfani da hulba don karin ni'ima; Idan mace
na fama da rashin ni'ima ko bushewar farji, za ta iya samun hulba ta yi amfani
da ita, kuma insha Allahu za ta dace. Yadda za ta yi amfani da hulba don karin
Ni'ima shine, ta samu 'ya'yan hulba da kanumfari da 'ya'yan habbatus-sauda da
kuma Zumarta mai kyau.
Za ta hada 'ya'yan hulba da na habbatus sauda da kanumfari
waje guda ta dafa su, idan sun dafu sai ta sauke ta jira ya huce, sannan sai ta
zuba zumarta a ciki, ta dinga sha. In sha Allahu za ki sha mamaki.
7. Hulba na taimakawa wajen rage kiba/teba; Kamar yadda mu ka
ambata a sama, mutanen nahiyar Asia, na amfani da hulba kan matsalolin lafiya
da yawa, to, game da matsalar kiba ma, su kan yi amfani da hulba don su samu
waraka. Yadda su ke yi kuwa shine, yawan sanya ta cikin cimakarsu.
8. Amfani da Hulba na kara inganta lafiyar koda; Masana sun
tabbatar da cewa, yawan yin amfani da hulba cikin abinci na kara inganta
lafiyar koda, ta hanyar sabunta kwayoyin halittar kodar, da hana su lalacewa.
9. Hulba na karewa hanta daga cutuka; Yawan amfani da hulba
na taimakawa wajen karewa hanta daga kamuwa daga cutuka. Masana sun ce, hulba
na wannan aiki ne ta hanyar fitar da sanadarai ma su guba, da ka iya yin lahani
ga hanta.
10. Amfani da hulba na taimakon ma su fama da ciwon
siga; An gano cewa, yin amfani da hulba na taimakawa ma su fama da larurar
ciwon siga. Masana sun ce, hulba na wannan aiki ne, ta hanyar daidaita sigan
dake cikin jini.
11. Hulba na taimakawa wajen sha'awar cin abinci; Ana amfani
da hulba wajen magance matsalar rashin cin abinci. Idan mutum na fama da rashin
sha'awar cin abinci, sai ya samu man hulba ya hada da zuma ya ke shan babban
cokali 2 sau uku a rana.
12. Ana amfani da hulba don karin kiba; Wannan ba zai zo wa
mai karatu da mamaki ba, idan ya yi la'akari da yadda mu ka bayyana a sama
cewa, hulbar na taimakawa wajen sha'awar cin abinci, mun san kuwa cin abinci na
da kyakkyawar alaka da samun kibar jiki. Saboda haka, mutanen da ke fama da
matsalar rama, sakamakon murmurewa daga wata rashin lafiya za su iya amfani da
hulba don samu waraka. Kuma za su iya amfani da hadin da mu ka fada a sama, kan
karin cin abinci don wannan fa'ida.
Sai dai, wani tsokaci anan shine, mai son yin amfani da hulba
don karin kiba, akwai bukatar bayan amfani da hulbar ya hada da cin abinci mai
Gina jiki, kamar wake da dankalin turawa,da kifi da sauran su, don kuwa hausawa
na cewa, ko da kana da kyau ka kara da wanka, kuma ko ba komai wadannan dangin
abinci za su taimaka wajen kara wa jikinka karfi. Baya ga haka kuma sai ka guji
cin nau'ikan abinci ma su maiko sosai.
13. Hulba na rage hadarin kamuwa da ciwon daji; Ba shakka
hulba na rage hadarin kamuwa da ciwon dajin mama, musamman ga mata ma su
shayarwa. Bincike ya nuna cewa, matukar mace mai shayarwa ta juri yin amfani da
hulba, baya ga kara ma ta lafiya tare da jaririnta, hulba na ba ta kariyar
kamuwa daga ciwon dajin mama (Breast cancer).
14. Ana amfani da hulba don maganin ciwon tari da mura da
kuma sauran ciwon sanyi da kan shafi makogwaro.
15. Hakanan, za ka iya amfani da hulba don maganin zafin jiki.
16. Hulba na taimakawa wajen samun lafiyar ciki, ta hanyar
maganin matsalolin ciki.
17. Mata na iya yin amfani da hulba don daidaita jinin al'ada
ga matan da jinin ke mu su wasa.
18. Ana amfani da hulba don maganin kaikayin gaba; Yadda za a
yi shine, A samu hulba a hada da gishiri a dafa sannan a jira ya huce yadda ba
zai yi lahani ga jiki ba, sai a zauna a ciki, zuwa wani lokaci, a kalla dai a
samu minti 30 a cikin wannan ruwan hulba. Haka za a yi har a samu waraka. Idan
kina bukata za ki iya hada shayin hulbar ki na sha, ko kuma bayan kin dafa da
gishirin, bayan kin debi ruwan da za ki zauna sai ki rage wani, ki jefa tsamiya
ki sha.
19. Hulba na taimakawa mata dake fama da bushewar gaba; Ga
matan dake fama da matsalar bushewar gaba, sai su samu man ridi su ke
zubawa a cikin ruwan dumi su ke zauna wa a ciki, sannan daga bisani sai su ke
yin matsi da Hulba, insha Allahu za a dace.
20. Hulba na maganin ciwon ciki bayan haihuwa
21. Ana amfani da hulba don gyaran nono; Bincike ya
tabbatar da cewa ana amfani da hulba don gyaran nono. Dalili kuwa shine, hulba
na sanya fata da tsokar dake kewayen nonon mace su buɗe, hakan sai ya sa nonon
ya ciko ɓulɓul abin sha'wa, musamman idan nonon ya kasance da girmansa amma ya
kwanta.
Abubuwan da ake bukata sune; garin hulba da garin Shammar da
kuma zuma.
Yadda za a hada.
Za a samu garin hulba da garin shammar. Ki ɗebi cikin ƙaramin
cokalin guda daya (1) na garin hulbar sai a zuba cikin kofi mai tsafta da aka
tanada , sannan a zuba garin shammar, shima cikin ƙaramin cokali guda,
sai a gauraye su waje guda. Daga bisani a dafa ruwa idan ya tafasa sai a kwara
a kan garin hulba da na shammar dake cikin kofin a juya su da cokali, bayan
haka sai a rufe kofin. Bayan kamar minti 10 sai a tace da rariya, bayan an
tace, sai a kawo zuma mai kyau a zuba a sha.
Daga bisani sai a shafa man hulba ga nonon. Wajen
shafawa akan nonon a tabbatar an murza man hulbar sosai akan nonon gaba daya
yadda zai shiga fatar nonon da kyau. Za a sha wannan hadin sau biyu a rana,
wato da safe da kuma dare, kuma duk lokacin da aka kammala shan shayin hakanan
za a shafa man hulbar a kan nonon, shi ma ya zama sau 2 kenan.
Yadda za ki gane maganin na amfani shine, ta hanyar jin
nononki na kara nauyi, alamar ya fara cikowa kenan. Allah Ya sa mu dace,amin.
Karin Bayani: A inda mu ka ambaci amfanin hulba ga lafiyarmu,
amma ba mu yi bayanin yadda za ayi amfani da ita ba, to mu na nufin mutum ya ke
amfani da kwayoyin hulbar a abinci, ko kuma ya rinka yin shayinta ya na sha.
Idan a shayi mutum ke son amfani da hulba, sai ya ke shan
kofi daya na shayin sau 2 a kullum, wato da safe da kuma dare.


No comments:
Post a Comment