- MA’ANAR SAIWOYI
Saiwoyi na nufin wasu jijiyoyi ne ƙananan da manya waɗanda su ke riƙe da bishiya ko tsirrai. A koda yaushe saiwoyi kan kasance ne a ƙarƙashin ƙasa amma a wani lokacin sukan fito waje ma’ana su kan turo ƙasa. A ɓangaren magungunan Hausawa na gargajiya su ma ba a barsu a baya ba, domin kuwa suna bayar da gudunmawa ta musamman wajen warkar ko kwantar da cuta a jikin Ɗan-Adam ko dabba. Wasu daga cikin saiwoyin da ake haɗa magungunan Hausawa na gargajiya sun haɗa:
Karnta:
www.assalafyislamicmedicinecenter@gmail.com
- SAIWAR KUKA.
Ana haƙo saiwar kuka ta ɓangaren gabas sai a jiƙa a sha tana maganin ƙarfin maza .
- SAIWAR ZOGALA
Ana haƙo saiwar zogala a haɗa da saiwar bini da zugu da lemon tsami da kuma barkono a jiƙa a sha, yana maganin sanyi mai kumbura jiki.
- SAIWAR TAFASHIYA
Mata masu ciki na amfani da saiwar tafashiya, su jiƙa su sha domin samun lafiya cikinsu.
- SAIWAR GAUDE
Ana haƙo saiwar Gauɗe a jiƙa a rinƙa sha, yana maganin ƙarfin jiki.
- SAIWAR RAWAYA
Ana jiƙa saiwar rawaya a sha, ko kuma a shanya ta bushe a daka a rinƙa soyawa da ƙwai ana ci yana maganin shawara.
- SAIWAR BAKIN GAGAI
Ana jiƙa saiwar baƙin gagai da kayana ƙanshi a riƙa sha maganin ƙarfin maza.
- SAIWAR SABARA
Ana ɗebo ko haƙo saiwar sabara da saiwar lemon tsami da ganyen tsamiya a haɗa a daka, sannan a jiƙa rinƙa sha, yana magann tamama (shawara) kamar yankan wuƙa.
- SAIWAR JEMA
Ana haƙon saiwar jema a wanke a zuba a randa ko ruwan sha, tana maganin mayu.
- SAIWAR DAYI
Ana haɗa saiwar dayi da farin goro a tauna sannan a haɗiye ruwan, tana maganin farin jinni. Bugu da ƙari idan aka tauna saiwar dayi ita kaɗai aka haɗiye ruwan maganin sammu (Makaru).
- SAIWAR TAFASA
Ana haƙo saiwar tafasa a dafa da jar kanwa tana maganin ciwon nono
- SAIWAR KUKA
Ana haƙo saiwar kuka wadda ta ratsa kan hanya, ana haɗa maganin kwarce da kuma maganin soyayya. Akan haɗa abinci da ita a ba yarinya ta ci, maganin mallakar zuciyarta domin soyayya.
No comments:
Post a Comment