Saturday, July 4, 2020

SINADARIN MA'AURATA

SINADARIN MA'AURATA



A wannan karo zamu yi bayani akan wasu daga cikin dangin kayan marmari da sinadarai da ma’aurata zasu iya bawa sha’awarsu – wato abinci da sinadarai masu karama ma’aurata lafiyar jima’i da ni’ima.

1-KANKANA (watermelon)
Kankana na daga cikin kayan marmari da ma’aurata zasu iya more amfaninta a gadonsu. Kankana nada sinadari mai yawa na CITRULLINE. Kashi 92 cikin 100 na kankana ruwa ne ,sauran kashi 8 na sinadarin ne. Amfanin wannan sinadari shine – yana sanya hanyoyin jini a cikin jiki su saki jiki. Hakan nasanya karuwar gudanar jini ga al’aura da kuma sauran jiki. Sakamakon haka nasanya karfin mazakuta da ni’ima tsakanin ma’aurata a lokacin saduwa. Yana karama mata ni’ima da nishadi sosai. Wannan sinadari yafi yawa ga bayan kankanar (fari). Duk da haka, akwai sinadarin mai yawa a cikin tsokar kankanar. Tasirin sinadarin yayi kamada na VIAGRA – maganin karfin mazakuta. A yanzu hakadai, masana-kimiyya na nazari akan samarda sabon irin-kankana wanda zai samarda sinadarin mai yawa a cikin kankana domin amfani dashi kamar magani wajen al’amarin jima’i. Asha Kankana minti 30 kafin a fara saduwa. Haka kuma yana da kyau ga lafiya mutum yamaida kankana abincinsa.

2-AYABA (Banana)
Aiba na taimakawa sosai wajen kara sha’awar miji da mata. Tana kunshe da sinari-maikara-sha’awa “bromelain” (an enzyme). Haka kuma tanada romon sinadarai masu sa kuzari da lafiya.

3-DANYA (almond)
Danya na daga cikin manya-manyen abincin ma’aurata. Tana tsokano sha’awar miji da mata. Haka kuma tana kara karfin maza. Za’a iya amfani da manta a zuba cokali 2 a sha a shayi sau 2 a rana.

TAFARNUWA (Garlic)
Tafarnuwa nada sinadarin “allicin”. aikin sinadarin a jikin mutum yayi kama dana kankana. Mutum na iya amfani da kafsol din tafarnuwa (garlic capsules) idan yana gudin yawan warinta. Hakan zai rage warinta akan cin tafarnuwar kai-tsaye. Amma yafi inganci ayi dubara aci tafarnuwar a wani abinci ko kuma wata hanyar. Idan kafsol za kayi amfani dashi toh sai asha guda 2 minti 30 zuwa 40 kafin saduwa. Kada kayi amfani da tafarnuwa lokacin zuwa Masallaci ko cikin jama’a, zaka iya cutar da jama’a. Zaifi ayi amfani da ita da dare , sa’annan awanke baki da brush da toothpaste.

YAJI (Chilli pepper)
Da yawa daga cikin mutane na tunanin cewa yaji bayada wani amfani sai kawai kawo matsalar zafi da basir. Wannan zance ba haka yakeba. Idan yaji nada illa ta wani bangaren toh kuma yana da amfani wani bangaren. Yaji na taimakawa wajen son cin abinci (good appetizer) idan mutum yayi amfani dashi ga abinci. Bayan haka, yaji yana da sinadari mai yawa na CAPSAICIN, sinadari mai tasiri kamar na kankana da mukayi bayani a baya. Yana hura wutar sha’awa ga ma’aurata. Haka kuma, Idan muka lura, akwai magungunan ‘da’a na gargajiya kamarsu YAJIN-MAZA da YAJIN-MATA da muke jin sunansu a kasuwa. Sirrin wadannan magunguna ya dogarane da sinadarin yajin,

GARGADI:
Kada kayi ta cin yaji da yawa don kaji yana kara lafiyar jima’i. Yana iya haddasa maka da matsalolin ciki ko basir. Ayi amfani dashi a farfesun nama na kayan-ciki, kaza ko na kifi. Idan kanada olsa (ulcer) ko wata matsala da yaji, ka guji yaji, toh kaji !!!

WASU DAGA NAU’IKAN ABINCIN MA’AURATA
A takaice ga wasu daga cikin sauran abincin mai-gida da uwar-gida: kifi, kaza, madara, kwakwa, kwai, hanta, citta, abarba, gyada, wake, karas, choculate da sauransu. Musani cewa motsa-jiki (exercise) nada matukar muhimmanci wajen cikakkiyar lafiyar jima’i da kuma lafiyar mutum ga baki daya.
Allah yasa mu dace, Amin.



No comments:

INA MAFITA

Maganin Maza

ASSALAFY ISLAMIC MEDICINE CENTER