Sunday, July 12, 2020

HAWAN JINI

CUTAR HAWAN JINI


Cutar Hawan jini ta yawaita matuka a cikin mutane harda al’umarmumta jinsin bakaken fata, kuma tana jawo mana illoli masu yawa.
Babban abin damuwa da bakin ciki shine, da yawa daga cikin al’umarmu basu da cikakken bayani game da wannan cuta; wasu kuma sun sani amma basa bada himma wajen neman magani.


MENENE CUTAR HAWAN JINI?


Ana cewa mutum ya kamu da wannan cuta ne idan an auna shi da na’urar awon karfin bugun jini (wato spygmomanometer) wadda ta nuna awon jininsa ya kai, ko ya wuce, dari da arba’in bisa casa’in (wato > 140/90mmHg) kuma awon ya dauwama a haka. Sai dai wannan adadi da aka ambata yana sabawa saboda bambancin shekaru, jinsi (wato namiji ko mace), halin da mutum yake ciki, da sauransu. A takaice dai, sai an je asibiti za’a iya tabbatarma mutum ko yana da cutar ko baya da ita.


MENENE YAKE KAWO CUTAR?


Ta la’akari da yadda wanna cuta ke faruwa ga mutane, an raba wannan cuta zuwa gida biyu.

Kashi na farko - Sama da kashi casa’in (>90%) na mutane dake fama da wannan cuta, har yanzu ba’a san takamaiman dalilin da za’ace shi ya kawo masu wannan cuta ba sai dai akwai wasu abubuwa ko al’amura da aka alakanta ga faruwar wannan cuta ga wadannan mutane na kashin farko.

Wadannan abubuwan sun hada da:

· Yanayin kwayoyin halittar dan-adam, ma’ana ana iya gadon wannan cuta.

  • · Jinsin dan-adam (anfi samu a bakaken fata)
  • · Yawaita shan gishiri fiye da kima.
  • · Yawaita shan barasa (giya).
  • · Kibar jiki mai tsananin yawa.
  • · Rashin motsa jiki, da dai sauransu.

Kashi na biyu - A wannan bangare, an gano wasu cututtuka na musamman da suke kawo wannan cuta. Cututtukan sun hada da:

  • · Cututtukan dake shafar kodar mutum.
  • · Cututtukan dake shafar kwakwalwa.
  • · Wasu daga cikin magunguna na bature.
  • · Wasu cututtuka dake shafar jijiyoyin jini, da dai sauransu.

TA YAYA AKE GANE ALAMOMIN WANNAN CUTA?


Wasu daga cikin mutanen da suka kamu da wannan cuta basu da wasu alamomi da suke ji, wasu kuma sukan ji kamar yawan ciwon kai, fargabar zuciya, raguwar gani ko gani dishi-dishi. Wasu kuma suna zuwa asibiti ne da alamomi na illolin da cutar ta haifar musu (za’a yi bayani nan gaba). Wasu kuwa sai sunje asibiti dalilin wata cutar, wurin bincike sai a gano cewa suna da cutar hawan jini.

Karin bayani a nan shine, ba wai ance da mutum yaji yana fama da daya ko wasu daga cikin alamomin can na sama kawai sai yace ya kamu da cutar ba. Wannan kuskure ne. Mutum ya bari sai yaje an auna shi domin a tabbatar masa ko yana da cutar ko bashi da ita, domin tabbatacciyar hanyar sanin mutum ya kamu da cutar hawan jini ita ce ta auna jinin da na’urar asibiti.


ILLOLIN CUTAR HAWAN JINI.


Wannan matsaloli zasu iya faruwa ga wanda bai dade da kamuwa da cutar hawan jini ba ko kuma ga wanda ya dade da ita. Sun kunshi:

  1. · Ciwon koda wanda zai iya jawowa ta daina aiki.
  2. · Raguwar gani ko makancewar ido.
  3. · Ciwon shanyewar wani bangare na jiki kamar rabin jiki (wato Paralysis).
  4. · Ciwon zuciya, da dai sauransu.

 

Sai dai abinda ya kamata a fahimta game da wadannan matsaloli shine, ba cutar hawan jini kawai ke kawo suba. Za’a iya samun su ta wasu cututtuka kamar ciwon suga (wato Diabetes Mellitus) da sauransu. Wadannan illoli sun fi faruwa ga mutanen da suke da wannan cutar kuma basa shan magani ko kuma basa sha kamar yadda likita ya umarta.

 

MAGANIN CUTAR HAWAN JINI.

 

Akwai magunguna kala-kala da ake bayarwa ga masu wannan cuta. Suna yin amfani ne wajen tabbatar da daidaitar awon jini na mutum ta yadda ba zai yi yawa har ya kai ga samar da wadancan illoli da muka ambata ba. Wadannan magunguna za’a same su idan anje asibiti wajen likita.

Haka kuma kula da wadannan abubuwa da zamu zana wadanda ke da alaka da wannan cuta suna taimakawa matuka wajen kiyaye kai daga samun wannan cuta ko rage matsalolinta ga wadanda suke da
cutar.


Abubuwan sune:

  • · Barin shan barasa.
  • · Rage yawaita shan gishiri a abinci.
  • · Motsa jiki akai-akai.
  • · Rage kiba mai tsanani, ta hanyar rage yawaita cin abinci fiye da kima, rage cin man kitse, motsa jiki da sauransu.
  • · Yawaita cin kayan lambu da ababen marmari kamar su lemo, yalo, karas, alaiyahu, zogale, rama, da danginsu.

 

KAMMALAWA DA SHAWARWARI.

 

Tunda mun fahimci wani abu daga wannan cuta, kamar abubuwan da aka alakanta ta da su, matsalolin da take jawowa da sauransu, to ya kamata mu tashi haikan, mu nemi kariya daga gareta kamar yadda Allah (SWT) da ManzonSa suka umurta, ta kiyaye abubuwan da ke iya jawota.

Ba karamin kuskure neba ga mai wannan cuta ya ki shan magani, wato yace ya warke, domin ba shi jin alamomin ta. A yanzu babu wani magani da ke warkar da ita gaba daya har abada, sai dai a sami saukin da zai bada dammar rayuwa kamar yadda mai Lafiya yake yi.

Tabbas, mun yi imani da bayanin Annabi Muhammadu (SAW) inda yake cewa “kowace cuta tana da magani”, amma muna fata Allah cikin rahamarSa zai fahimtar da likitoci maganin da zai warkar da ita nan gaba. Saboda haka sai a dauki wannan cuta a matsayin kaddara daga Allah, a kuma nemi lada daga wajenSa, a cigaba da shan magani domin a samu rayuwa cikin kwanciyar hankali kamar kowa.

Kada mutum ya tsaya a zuwa kemis kawai ya ki zuwa asibiti. Illar wannan shine, za’a iya bada maganin da bai dace da mutum ba, ko kuma wanda zai iya kawo masa babbar matsala ga jiki.

A kuma lura, kada a tsaya a yi ta shan magunguna na gargajiya, a ki zuwa asibiti domin wadannan magunguna basu da tabbas, kuma za su iya taimakawa wajen kawo matsaloli da zasu shafi koda, hanta
da sauran sassa na jiki.



No comments:

INA MAFITA

Maganin Maza

ASSALAFY ISLAMIC MEDICINE CENTER