Thursday, July 23, 2020

Gyaran jiki a Musulunce

ASSALAFY ISLAMIC MEDICINE CENTER

WAJIBI NE UWAR GIDA KI GYARA JIKIN KI KAMAR YADDA MUSULUNCI YA TANADA

Mutane uku sune suke daukar nauyin rayuwar mace komai daraja da matsayinta dole wadannan sune kan gaba wajen mutunci da kimarta wanda wadannan mutane uku bata iya zabawa kanta koda daya daga ciki, abinda kawai take iya yiwa kanta shine kokarin rabuwa da kowanne daga cikinsu lafiya yayinda kowanne daga ciki yake tattare da nasa kalubalen,


Haka zalika kowacce mace akwai kaddararta a daya daga cikin su,


Iyayenta

Rabuwa da iyaye lafiya shine yafi komai muhimmanci a rayuwar mace domin shine tsani na farko da mace zatabi wajen samun rayuwar farin ciki


Mijinta

Miji kuwa dashi ake shinfida rayuwar duniya data lahira kuma miji shine wanda kalubalen zama dashi yafi girma awajen mace


‘ya ‘yanta

Haihuwa kuma itace mace domin a kowanne lokaci tana ajiye mace a gabar mutuwa kafin haihuwar sannan bayan haifuwa take sake shiga wata sabuwar wahala ta kula da jaririnta da kuma mijinta

A duk rubuce rubuce da nakeyi ban taba rubutu akan haihuwa ba yasa wasu jama’a ke ganin ana suya ana mantawa da albasa domin ta dalilin haihuwa mata da yawa sun fuskanci mawuyacin hali tareda miji wasu aurensu ya mutu wasu kuma da zaran sun haihu rashin yin gyara shine zaisa ayi musu kishiya kai bama yin kishiya shine matsalaba wulakancin da mace kesha idan wata matsala ta sameta har miji ya kara aure shine matsalar wasu kuma rashin haihuwar shine kalubalensu saboda haka yanzu zamu fara da wanda ita rashin haihuwar shine kalubalenta wanda kuma wasu matan toshewar mahaifa ko juyewarta ko dai matsalar maniyyi da dai sauransu shine yasa ciki yaki shiga,
Magungunan gargajiya sune kan gaba wajen Gyara wannan matsalar, dan haka ya dace da wanda ke fuskantar wannan matsalar tayi ta jarrabawa har Allah yasa ayi nasara, kuma daga cikin magungunan guda biyu da zaki jarraba

1. na farko zaki iya matsi da furen dabino wato zaki samu furen dabino ki barshi ya bushe ki dakashi ki hada da farar zuma kiyi matsi dashi da safe da yamma sai ki wankeshi wannan yana temakawa maniyin namiji shiga mahaifar mace


2. na biyu kuma zaki rinka cin kwan agwagwa wato zaki samu kwai guda daya ki soya shi amma da man tafarnuwa kuma zaki ci safe da yamma har zuwa sati daya shi wannan kuma yana wanke dattin mahaifa wanda yake hana mace haifuwa da izinin Allah

MATSALAR CIWON
NONO
koda yake kaso tamanin da biyar cikin dari (85%) na mata masu ciwon nono masu shayarwa ne amma ana samun wadanda basa shayarwa suna kamuwa da ciwon sakamakon amfani da magungunan turawa musamman na shafawa dan haka abu na farko da zakiyi dan kiyaye kanki daga ciwon nono shine rabuwa da magungunan turawa.

me shayarwa akwai hanyoyi da zatabi domin riga kafin kamuwa daga cutar misali yin bacci da nono a bakin yaro,
kodai kwanciya da rigar nono (brezia) ko kuma kwanciya rubda ciki. mace me manyan nono lokacinda take shayarwa ana bukatar ta rage duk wani abu dayake jijjiga nono kamar tsalle ko daurin kirji wadannan suna saka nono shan wahala daga bisani yayi ciwo.
bawa yaro nono daya abar daya yana kawo kankancewar daya sai kaga nono daya yafi daya ko kuma yawan kwanciya akan daya wannan shima dole mace ta kiyaye idan kuma hakan ta faru sai acigaba da maganin gyaran nono ahankali zai dawo kafin ki sake wani shayarwar.
sannan dole ki kiyaye da bawa yaro nono koda kina bada reno ki tabbatar yaronki yanasha kullum

domin rashin shan nonon yana kawo ruwan yayi yawa daga karshe yayi ciwo wannan shine kuskuren da wasu mata keyi idan sun bada reno sai ayi kwanaki ana bawa yaro madara kuma daga baya adawo bashi nono.
yawan shan nono wajen yaro yana kawo karancin ruwan nono ajikin mace daga karshe su motse ya zama fata ce kawai wannan ya kamata ki lura dashi idan kin samu wannan matsalar danyen ganyen zogale zaki dafa ki tace ruwan saiki hada alkama da waken soya da gyada kiyi garinsu kina zubawa acikin ruwan zogalen zaiyi kamar salala (sirki) saiki zuba nono ko madara kinasha kullum sannan ki dage dashan kunun kanwa dana alkama.


Domin magance matsalar ciwon nono kuma hanyoyi biyu kike bukata na farko garin hulba zaki zuba acikin ruwan zafi lokacinda zaki kwanta ki gauraya ki shafa akan nonon da safe ki wanke, ko kuma ki hada man ridi da man hulba da man kadanya kina shafawa akullum. 

To wannan shine karshen bayanin akan haifuwa da kuma matsalar ciwon nono yanzu kuma zamu koma bangaren gyaran jiki da yanda me jego zata dawo tsaf kamar bata haifuba.


KI FARA MATSE GABANKI KAFIN YIN KOMAI


Shima ganyen gamji yanada tasiri wajen tsaftar gaban mace wato yanda akeyi shine kisami ganyen gamji ki dafa saiki tace ruwan ki rika tsarki da ruwan har tsawon wata daya,


Bagaruwa ta hausa ita da tsintsiyar maza itatuwane da ake amfani dasu shekaru da yawa kina iya ki tafasa ko kuma kijika su da ruwa mai dumi kidinga tsarki dashi,


Ki sami aloevera da karo da kanumfari saiki zuba ruwa ki tafasa bayan kin tace anaso ki ajiyeshi har yayi sanyi kina tsarki dashi yana matse gaban mace

 
sannan idan kika samu ganyen aloevera ki matse ruwan saiki dauko man zaitun ki gauraya kiyi matsi dashi bayan kin wanke da ruwan dumi saiki sake sakawa har zuwa dare wannan zakiyi tayinsa shima yana matse gaban mace sosai,
 
Anaso ranar farko da jini ya  dauke saiki  hada ganyen magarya, garin hulba da  bagaruwa

Ki hadasu da tafarnuwa ki kisa ruwa amma kadan ki dafa idan ya dahu kitace saiki barshi ya huce sanan ki Samu auduga kina sawa a cikin ruwa kina wanke ko Ina na gabanki Ciki da waje ki tabbatar kin wanke ko ina anaso wannan ruwan ki rage kadan kuma ya zama yana da dumi sosai sai ki Samu wani auduga daban ki dangwala ruwan kisa a cikin gabanki ki barshi zuwa wani lokacin sai ki cire tun a nan zakiga kin ciko kin hade tsaf  wannan yanada muhimmanci ga mai jego.


warin gaba (Vaginal Odor)


Duk irin kwalliya da wasu matan suka iya idan akazo maganar al'auara saika rena tsaftarsu anaso gaban mace ya zama da kamshi budurwa ko matar aure kuma akwai dalilai bakwai dake kawo hakan

1 istimna.i wato idan sha'awarki ta motsa kiyi amfanida hannunki wajen gamsarda kanki ko kuma madugo (lesbian)

2  ya kasance bayan kin gama saduwa da miji bazaki wankeba kawai saidai kiyi kwanciyarki

3 dadewar wando (pant) ajiki ba'ason mace tarika barinsa yana dadewa

4 yin amfani da ruwan sanyi wajen tsarki Kodai da zaran kinyi tsarki bazaki gogeba ki saka wando da jikan ajiki

5 duk lokacin da zaki yi tsarkin bayan gida(kashi) ki hada shi da wannan wurin ki cakude da sunan wankewa hakan kan sanya wari ko doyi ya samu wurin zama a gabanki
 

6 tafiya ba wando ya zamana ke sanya wando (pant) ba sabonki bane kina iya zuwa ko ina haka ba tare da wando a jikinki ba wasu har unguwa suna fita ba tare da wando ba daga yan'matan har masu auren

7 ko kuma bayan kin yi wankan tsarki na al'ada ba ki wanke gabanki da sabulun tsarki ko baki amfani da miski domin gun yayi kamshi Domin magance matsalar sai a kiyaye wadannan dana fada a sama kuma ya zama ana amfanida miski akai kai


MATSI
Har yanzu dai muna nan akan maganar matse gaba dan haka me jego Akwai zunzurutun muhimmanci kisan wadannan abubuwa guda hudu:

1 alobera (aloevera)2 Karo (jirai)3 man zaitun (olive oil)
4 kanumfari (Cloves) 

ki sami alobera da Karo ki saka kanunfari ki tafasa saiki tace ki ajiye ruwan ya zama shine ruwan tsarkinki,



Idan kuma saura sa'a daya kije wajen me gida wato idan za ayi harka dama kin matse ruwan alobera saiki hadashi da man zaitun kiyi matsi dashi gam gam kenan ku jarraba 


YAJIN ME JEGO


Me jego kisan wadannan Baure da Dan kumasau da minanas domin suna daga cikin abubuwan dake temakawa mace musamman wajen cikowar gaba tareda ni ima da matsi musamman me jegoCikowar gaba da ni ima tareda matsi ciki da waje sune cikar mace,ta kasa idan kika samu wadannan to bakida matsala wajen gamsarda miji kuma wannan yajin yana amfani sosai awannan fanni musamman wadanda basuda halin ciccibin saniya kona akuya wasu kuma basa iya cin wannan naman shine ake amfanida wannan yajin wajen cin abinci kullum anaso ya zama yajinki ko a miya ko cikin abinci ko nama yana aiki 100%

kamar yanda kuka gani a sama sassaken baure da minanas sai Dan kumasau sune kan gaba wajen yajin saiki kara da sassaken gabaruwa kanunfari da sauran kayan kamshi na yaji amma dai wadancan na sama sufi yawa anaso aji alamarsu karara

Haka zalika yajin yana bukatar maggi da barkono kadan yanda bazai fitoba tabbas idan kika hadashi yanda yadace zakiga amfaninsa koda bakya jego matukar kinason cikowar gaba da ni ima tareda matsi

CICCIBIN SANIYA
 
Me jego yanada zunzuru tun muhimmanci kisan amfanin ciccibin saniya da kuma yanda ake yinsa domin ba sabon abu bane ganin ciccibi a wajen masu tallan maganin mata

Cin wannan nama yana ciko gaban mace yayi kyau tareda matse ta kana yayi ni,ima kuma ba sai lallai na saniya ba anayi dana akuya saboda haka gaban saniya kona akuya kowanne amma danyen shi saiki yanyankashi ki wanke ki dora akan wuta dama kin daka ridi wanda aka soyashi ki zuba zaki iya saka nonon akuya kona rakumi sannan kisaka garin kanun fari dan kuma sau saiki saka duk wani kayan miya yanda zai miki dadi saiki barshi saiya dafu saidai anaso kiyi yanda romon zai zama dan kadan shi wannan naman da romon duk zaki cinye

idan kuma kinaso kisoyashi saboda ki ajiyeshi wannan yafi wahala amma yafi aiki ana bukatar kisamu ridi da gyada ki soyasu sama sama saiki samu kanun fari da minanas da dan kumasau kihadasu waje daya ki dafa ruwan ya dafu sosai ki tace ruwan ake bukata lokacin soya naman domin idan kika yayankashi saiki zuba wannan ruwan saiki dora akan wuta kina jujjuyashi anaso kiyi yanda wannan ruwan yana karewa naman ya kusa soyuwa saiki saka man Man ayu ko man gyada ya karasa soyuwa shikenan kin gama kowanne lokaci kina iya cinsa

TSUMIN ME JEGO
Da farko anaso me jego kafin tayi 40 ya zama kulum zatasha tsumi akalla sau biyu a rana to amma saidai mutane da dama sanin kalar tsumi da me jego ya dace tasha yana basu wahala shiyasa nayi kokarin kawo wasu fitattun tsumi da suka shahara ki jarraba koda dayane kisha mamaki
? ki yanka rake kanana kanana kamar alawar yara sai ki saka a tukunya da ruwa ki saka kanumfari bada yawa ba fa da yar cittar ki itama ba mai yawa ba sannan ki bare dabinon ki cire kwallon ki jefar kwallon saiki dakashi ya zama gari saiki zuba aciki sai ki dora kan wuta ya dahu sosai sai ki sauke ki matse rake ki cire totuwar raken sannan ki tace ruwan sai kuma maida shi kan wuta
Ana iya saka mazalkwaila a ciki sai ta narke sai ki sauke kisa a fridge yayi sanyi shikenan kin hada
 
 Sai tsumin baure wanda akwai Hanyoyi da yawa da ake tsumin wanda mace idan tasha ita da kanta zataji tasamu ni ima kuma wannan karonma mun jarraba wani tsumi don me jego koda budurwa me shirin aure ta rikeshi kullum,zaki samu sassaken bauren da yayansa da minanas da kanunfari da dabino da malmo da kukuki
Wadannan anaso ki dafasu bayan sun dafu saiki tace ruwan sai kuma ki zuba mazarkwaila da Zuma kadan sannan kisake mayar dashi kan wuta ya tafasa saiki sauke shikenan kin gama kuma wannan koda kinada ciki zaki iya shansa

To atakaice wannan shine gyaran me jego wanda zai mayar da me jego ta dawo sabuwar amarya, Godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki da ya bamu damar kammala shi….



No comments:

INA MAFITA

Mu'jizar da ke cikin Zaitu

Amfanin Man zaitun Ciwon Ciki: Duk mutumin da yake ciwon ciki sai ya samu man zaitun kamar cikin cokali ya hada da garin habbatus saud...