AMARE DA MASU NIYYAR AURE
wannan wani hadine na musamman wanda ake bukata amare suyi.ko masu niyyar aure.
Da farko sai asamu tatacciyar zuma mai kyau a aje gefe daya sai asamu :
- DabiNo (ajuwa).
- Garin hulba cokali 3.
- Sai asamu man habbatus sauda dan misra maikyau sai garin ridi cokali 5.
- Sai gyada itama cokali 5.
Sai a hadesu wuri daya su hadu.sai arinka sha cokali 3 safe da yamma.
Ko kuma a samu dabino (ajuwa)a hada da nonon rakumi da garin alkama cokali 4.sai a hadasu wuri daya a damasu a rinka sha sau daya arana da daddare.
Kokuma a hada kwa-kwa da dabino maikyau arinkaci sau daya arana.
bayan nan sai a hada madara da kankana mai kyau amman kankanar za'a jajjagata sai a hadata da madara a rinka sha safe da yamma.
Wacce ta rasa Budurcinta wato kamar bazawara ko kuma budurwa da akayiwa ( fyade ) ko kuma Wata hanya daban.
Mata da yawa suna aure cikin fargaba idan suka hadu da ( kaddara ta fyade KO kuma saduwa da namiji ) kuma hakan yayi sanadin rabuwarsu da budurcinsu don sun san maza da yawa sun fahimci hanyoyin da zasu gane mace idan ta rasa Budurcinta kuma Daga ( DAREN FARKO ) ango zai iya Fara canjawa amarya soyayyar sa harma wasu suna fadawa zuciyar su bazawara suka auro wato wani ya rigashi kwanciya da ita"_
Inda wannan ta faru dake Zaki iya tsarki da*
Ruwan dumi
Bagaruwa
Na tsawon Wata guda sai kuma matsi shi kuma zakiyishi saura sati biyu aurenki
KAYAN HADIN
ki daka garin zogale ki tankadeshi.
Ki samu man ka danya ( Ana samu a wajen masu maganin gargajiya.
Ki samu man zogale ( Ana samu a wajen masu *_Islamic-medical-centre_*.
Ki samu Karo shine wanda ake tawada dashi kuma ana wanke hula dashi ( Ana samun sa wajen masu kayan koli ).
Ki samu man shanu ( anansamunsa a wajen masu sa yarda nono).
*duk ki hada su wajen daya ki kwaba su suyi kamar sa'oi 5 zakiga sun hade sai Kiyi Matso dashi kuma Zaki iya rabashi uku gida 3 wato Kiyi matsi dashi Sau uku a cikin sati biyu.

No comments:
Post a Comment