Wednesday, May 27, 2020

RASHIN SHA'AWAR MACE, INA MAFITA!

RASHIN SHA'AWA

akwai matanda basayin sha'awa ko basa jin dadin saduwa ko ni'imarsu ta dauke, to yanda za'a magance wannan matsala shine sai kisamu.
*zangarniyar zogale,da ya'yanta gadaya
*karanfani
*citta
*masoro
*kinba
sai ki dakesu guri daya su zama gari,sai ki rinka shan wannan hadi a shayi safe da yamma,ki gwada ki gani, yana kara dadin da mai gida zai gamsu sannan kuma zaki rinka cin dabino(ajuwa) mai kyau tare da kwakwa zaki sha mamaki.
 
RASHIN SHA AWA AR NAMIJI A WAJEN MACE

Dukkan mace matar aure ko budurwa data samu kanta a yanayi na rashin sha"awar namiji ko kuma rashin jin dadin jima'i to gaskiya ta hadu da kalubale a bangaren zaman aure Hakika wasu matan tun suna yan mata suke kashe kansu da shan wasu magunguna marasa inganci da sunan ya rage musu sha awa wasu har jar kanwa suke jikawa da lemon tsami suna sha don ya rage musu sha'awarsu kuma wannan duk kuskurene idan har bazaki iya azumi ba to ki ajiye burin rayuwa kiyi aure domin ita Sha'awa ajikin mace ko namiji ba cuta bace amma rashinta kuma cutace bazaki gane hakanba saita faru dake To idan akace rashin sha awa ga mace ko rashin jin dadin jima i to ya hada abubuwa da yawa amma masana sirrin jima i suna takkaita bayanin kamar haka akwai wacce tana sha awar namiji hasalima ko zancen jima i tayi da namiji koda a wayane ko a chat zataji farjinta ya jike alamun sha awa zata bayyana a fuskarta zataji sha war namiji ya sadu da ita amma da zaran na miji ya saka azzakarinsa a farjinta saita rasa ina dadin yake

ita wannan tana bukatar kyakyawar kulawar soyayya a wajen mijinta ya kamata mijinta yasan hanyoyin sarrafa mace da sanin wurarenda mace takeso namiji ya taba ajikinta musamman lokacin jima i kuma soyayya itama tanada muhimmanci awannan lokacin wato tana saka mace jindadin jima i akwai wacce ita kuma kwata kwata bata sha awa ita ko za ayi wata daya ko biyu ba a tabataba batada matsala idan kin samu kanki acikin wannan halin akwai tambaya akanki
kina mafarkin namiji?
idan kina mafarki tofa aljanine domin zai hanaki jin dadin mijinki saboda shi yasadu dake kuma gaskkiya wannan matsalace kuma wani lokacin sihiri akeyiwa mace hakan take faruwa

kiyi kokari kici gaba da addu a kuma kina kwaciya da alwaa idan zaki kwanta ki karanta wasu ayoyi daga cikin qur ani sannan kina share shimfida kafin kwanciya kuma keda mai gida ku rinka addu a kafin ku fara jima'i insha allahu zakiyi mamaki.

hanya ta biyu Kisamu man habba da man zaitun saiki karanta ayoyin al qur ani musamman suratul baq ra da kula’uzai da kul-huwa kafa uku-uku ki tofa saiki dinga shafawa kuma kina sha cokali daya safe da yamma

hanya ta uku kuma ki samu turare mai kanshi wanda kanshinsa yake da dadi sosai shima kiyi karanta masa wannan wadannan surorin a ciki saiki dinga shafawa a wurare kamar haka:
1-Kan gashin giranki
2-Ramin kunnuwanki
3-Kofofin hancinki
4-Kan nonuwanki
5-Kan farjinki da kan dubura:

sannan sai kan yatsun hannayenki guda goma da kan yatsun kafafuwanki
guda goma saiki kwanta
to idan kuma mace bata mafarkin namiji kuma batajin sha awa to wannan kada kiya wasa dashan kayan karin ni ima kuma ku zama masuyin wasanni sosai kafin jima'i

sannan akwai kuma mace wacce tana sha awar namiji amma ta fiso ya saka mata yatsa a farjinta tafi jindadi idan ya saka mata azzakarinsa sai taji dadin ya ragu kuma irinsu zaka samesu da bushewar. farji to irin wannan itamma tana bukatar kulawa ta musamman daga wajen mijinta sannan kada kiyi. wasa da gyaran jiki da kuma tsaftar farji.
 
HANYA TA BIYU
Daskarewar sha’awa shi ne wani yanayi na rashin jin motsowar sha’awa ko rashin samun biyan buqatar sha’awa ga ‘ya mace lokacin ibadar aure. Da yawa ma su fama da wannan matsala na zatton ba su da sha’awa ko kuma sha’awar su ce ta qare, amma a haqiqanin gaskiya sha’awar su na nan lafiya kamar ko wace lafiyayyar mace illa dai daskarewa da sha’awar ta su tayi a dalilin wani abu da ya faru ko wani yanayi da su ka shiga mai nasaba da ibadar aure.

Abubuwan Da Ke {arancin Sha’awar Uwargida
Qarancin Ilmin Ibadar Aure: Yawancin ma’aurata na fada ma da’irar auratayya ba tare da isashshen ilmin yanayin zaman aure da kuma na ibadar aure ba. Haka kuma za ka taras an koya ma amarya komai na zaman gida, amma sai aininhin abin da zai kai ta gidan aure ne ba a koya ma ta ba. Yawanci abubuwan da a ke jin labarai wajen ‘yan’uwa da abokai ba su isa wajen tabbatar da samun nasarar ibadar aure ba musamman a daren farko. Wadan nan labarai illar da su ke ma ta fi yawa, sai an yi auren sai a taras duk abin ba kamar yadda a ka ji ya ke ba.

Shi ango a dalilin rashin isashshen ilmin ibadar aure, sai ya wahalar da amaryar sa, ita ma saboda rashin isashen ilmin sai ta bari ta sha wahalar ba tare da ta san irin yadda za ta yi ko wani tanadin da za ta yi don kauce ma aukuwar hakan ba.

Rashin Nasarar Daren Farko: Ga ‘ya mace, daren farkon nan shi ne komai: da shi ta ke ma yanayin ibadar aure fassara, shi ya sa in mace ta wahala kuma ya kasance wahalar ce kadai ba tare da ta sami motsuwa da biyan buqatar sha’awar ta ba to ibadar aure ba ta da banbanci da fyade a wajen ta, haka za ta ci-gaba da zama ta na kyamar ibadar aure kuma ta na yin ta a kan dole. Wan nan yanayin tunanin shi zai daskarar da sha’awar ta gaba daya har ya kasance ba ta jin motsawar ta a jikin ta kwata-kwata. Kuma ba za ta taba samun waraka ba har sai yanayin tunanin ta ya canza. Shi ya sa ya ke da matuqar muhimmanci ga mai gida ya karanci yanayin halittar ‘yammatancin mace don ya san ta yadda zai bi bai cutar da matar sa ba. Ita ma Uwargida ya na da kyau ta fahimci yadda halittar da namiji ta ke domin qarin faranta ran mai-gidan ta. Maganin aukuwar rashin nasara a daren farko shi ne ma’aurata, su sami cikakken ilmin ibadar aure tun kafin ranar auren su ta zo. Kuma iyaye a lura da yanayin yarinya, in an ga irin wacce ba ta san komai ba ne game da wannan fannin sai a sami ko wata yayar ta ko qanwar uwa da ta yi aure ta yi ma ta bayani yadda abin ya ke da kuma abubuwan da su ka dace ta yi.

Rashin aikawa da ‘yan aike ta fannin mai-gida: Akwai banbanci mai fadin gaske tsakanin sha’awar mace da ta da namiji, namiji sha’awar sa na saurin motsuwa, kuma in ya kusanci matar sa, nan da nan zai kai ga cimma biyan buqatar sha’awar sa. Yayin da ita mace sha’awar ta mai nauyi ce kamar jiqaqqen icce, yadda ba zai yi saurin kamawa ba in a ka sa shi a wuta sai an yi hurawa tare da sa makamashi da sauran ‘yan dubaru kafin ya kama, to haka ma sha’awar mace na buqatar makamashi da yan dubaru. Makamashin sun fara tun daga kyakykyawar qauna a zuci, kyakykyawar kulawa, kalamai ma su dadi da narkar da zuciya tare da sarrafa murya domin muryar namiji na da matuqar tasiri wajen motso da sha’awar ‘ya mace kuma ko wane dan’adam na da wani kalami, wani suna ko wata jimla wanda jin sa cikin irin yanayin da ya ke so na matuqar motso ma sa da sha’awar sa.

Maigida ya kasance ya na koda uwargidan sa a ko yaushe. Ya runqa yaba kyanta da kwalliyyar ta da irin tasirin da suke ma shi fiye da yadda su ke a zahiri. Qarya ta tsakanin miji da mata na daya daga cikin qarya ukku da Manzon Allah SAW ya halatta. Haka kuma ya yi hani da fada ma mace kamar yadda dabbobi su ke yi ba tare da aika dan aike ba. To ko wa su dabbobin ma s u kan aika da dan aiken, dubi zakara in ya na bin kaza har kiwon ‘ya’yan ta ya ke mata. Haka ma zaki taa dubara da wasanni ya ke neman zakanya kuma duk da haka ba lallai ne ta kyale shi ya sami abin da ya ke so ba a wannan lokacin sai ya qara lallaba ta wani lokacin.
San nan mai-gida ya kasance mai gyara kan shi da yin kwalliya domin iyalin sa. ‘Yan dubarun kuma su ne abubuwa na zafafa sha’awa da wasanni na jiki lokacin ibadar aure, mai-gida ya zama mai yin juriya don ganin ya faranta ma maidakin sa, burin sa ya kasance na ganin iyalin sa ta samu biyan buqata ne, ba wai ya nemi biyan buqatar sa kadai ba ya bar matar sa cikin qunci.

Kunya da rashin kazar kazar ta bangaren uwargida: Yawancin Matan aure su na cutar kan su da mazajen su sabada kunya lokacin ibadar aure. Sai ya kasance uwar-gida ta bar mai gida ya zamana shi ne wuqa shi ne nama, sai yanda ya yi da ita. Ita ba ta iya tabuka komai.

Ya kamata matan aure su cire kunya ta fannin ibadar aure, tare da halartaccen mijin ki ki ke to me ye kuma na kunya, duk wani qoqari da za ki yi don jiyar da kan ki ko mijin ki wani dadi lada ki ke samu.
Abin da ya sa da yawa mazaje su ke neman matan banza da karuwai sai don kawai su ba su da kunya ta wannan fannin, duk abin da namiji ya ke so su na ma shi.

Kamar yadda ki ka ga mijin ki na qoqarin yin duk abubuwan da zai hauhawar ma shi da sha’awar sa har ya kai ga biyan buqatar sa to ke ma haka za ki yi.
Bincike ya tabbatar da duk duniya ba namijin da ke son mace mai kunya lokacin ibadar aure, ko wane namiji na son mace mai natsuwa da hankali wacce za ta rikide ta zama kamar kwararriyar karuwa lokacin ibadar aure.
Duk yadda ki ke ganin ki na gamsar da mijin ki to gamsuwar nan za ta qaru ta zama ninkin ba ninkin in kema ki na samun biyan buqatar ki a lokacin ibadar auren ku.

Uwar-gida ta runqa nuna ta na tsananin sha’awar Mai-gidan ta, ta runqa nuna ta zaqu da son kasancewa tare da shi, wannan na tsananin faranta ran da namiji, kuma ya ga ya biya da sha’awar matar sa wannan ma na haifar da shauqin jin dadi a zuciyar da namiji.

Don haka a na ma iya cewa gara ki nuna ma namiji tsananin sha’awar sa da ki ke a kan ki nuna ma sa tsananin qauna domin su maza sun fi gane ma yaren sha’awa a kan yaren qauna ko soyayya, sha’awa itace soyayyar da su ka sani, shi ya sa da sun dai na sha’awar ki za su daina son ki.
Uwargida ta koyi sakkin jiki da maigidan ta, ya kasance duk lokacin da ya kusance ta ya ji ta ta narke ma sa.
Yanayin Tunani: Yanayin tunanin da ke kai kawo a cikin zuciyar uwar-gida musamman game da ibadar aure ko mijin da ta ke aure na iya daskarar da sha’awar ta.

In mace ba ta son mijin ta ko ta na jin haushin sa a bisa wani dalilin ko ba ya burge ta fannin mazantakar sa, wannan na iya daskarar ma ta da sha’awar ta. Haka nan ma baqin shauqi da ya mamaye zuciyar Uwargida; irin su tsananin huzni, tsananin tsoron wani abu ko wani mutum, jin haushi, rashin kwanciyar hankali, fargaba, da sauran su na iya daskarar ma ta da sha’awa. Don haka in mace ta na cikin wannan yanayi ya na da kyau ta yi qoqarin wanke zuciyar ta daga ko wane irin baqin shauqi don samun lafiyar ta da kwanciyar hankalin iyalin ta.

Haihuwa da kuma yawan haihuwa: Haihuwa na shafar ma’ajiyar sinadarai a ‘yammatanci ta yadda ba sa iya sarrafa sinadaran da ke motsar da sha’awa a ‘yammtanci. Sannan yawan haihuwa a kai a kai na sa jijiyoyin ‘yammatanci su sakki har wani lokacin riqe fitsari na yin wuya ga wa su matan. Wadan nan jijiyoyi kuwa su ne komai da komai da komai wajen gamsuwar da mai-gida ke samu uwar-gidan sa uwar-gidan sa. Don haka sai a dage wajen kula da kai da jiki lokacin da a ke dauke da ciki, lokacin jego da kuma lokacin shayarwa, musamman ma dai lokacin jego don a samu komai na ‘yammatanci ya koma dai-dai.
MAGANIN RASHIN SHA'AWA:
akwai matanda basayin sha'awa ko basa jin dadin saduwa ko ni'imarsu ta dauke, to yanda za'a magance wannan matsala shine sai kisamu:
- zangarniyar zogale,da  ya'yanta gadaya
- karanfani
- citta
- masoro
- da kinba
sai ki dakesu guri daya su zama gari,sai ki rinka shan wannan hadi a shayi safe da yamma,ki gwada ki gani, yana kara dadin da mai gida zai gamsu sannan kuma zaki rinka cin dabino(ajuwa) mai kyau tare da kwakwa zaki sha mamaki.

  KO KI DINGA SHAN ZUMA
safe da yamma cokali 2


INA MAFITA

Maganin Maza

ASSALAFY ISLAMIC MEDICINE CENTER