KANKANCEWAR AZZAKARI/MAZAKUTA
Mutane da yawa suna shiga damuwa saboda a tunaninsu azzakarinsu ya kankance ko kuma a ganinsu bashi da girman da ya kamata ace yana dashi.
Wannan matsala ba a zallan Nigeria ko Arewa ake samunta ba.
Bincike ya nuna cewa a kasar India akwai wasu mutane da ake ce musu “Sadhu” wadanda suke daura abu mai nauyi a azzakarinsu don ya kara girma. Wasu ‘yan kabilar “Tropinama” a kasar Brazil kuwa sukanyi amfani da maciji ne mai dafi su sakashi ya cijesu a azzakarinsu, wai don ya kumbura ya kara girones
Hakazalika a Arewa akwai masu maganin kara girman azzakari a ko wani lungu da sa’ko. Sai dai a mafi yawansu kwalliya bata biyan kudin sabulu. Shi kuwa mai matsalar kankancewar mazakuta kullum cikin damuwa da tashin hankali yake.
Abinda nake so mu gane shine mafi yawan abinda ake tunani akan girman azzakari ba haka abun yake ba. Akwai matsaloli na kankancewar azzakari da aka sansu a kimiyya da ilimin Lafiya kamar su “micro-penis” da “Klenefelter syndrome” da sauransu. Sai dai mafi yawansu tun haihuwa ake samunsu ko kuma wata matsala mai tsanani. Irin kankancewar mazakuta da mutanenmu suke tada hankalinsu akai bai kai yadda suke zato ba.
Masana sunce girman azzakari yana kasancewa ne kusa da 9cm (3.5in) a lokacin da yake kwance bai mike ba. Sannan kuma ba matsala bace ya zama yayi kasa da haka ko sama da haka da kadan. Akwai abubuwa da suke kankantar da mazakuta na wani lokaci kamar idan ka shiga ruwa kayi ninkaya ko kuma in kana wajen da akwai sanyi.
Bincike ya nuna cewa girman azzakari a lokacin da ya mike yana kaiwa 13cm zuwa 18cm (5-7 inches). Masana sunce ba zaka iya karawa ko rage girman azzakari ta hanyar motsa jiki (exercise) ko magani (medication) ba. Kowani azzakari yanayinsa daban da saura. Azzakari yana kara girma ne tun daga yarinta sannan yakan gama girmansa ne a yayin da yaro yakai shekara 21.
Bincike ya nuna cewa maza da yawa basu gamsu da girman azzakarinsu ba, koda kuwa yaya yake. A wani bincike da Professor Kevan Wylie wanda kwararre (consultant) ne a bangaren ilimin lafiyar jima’i (sexual medicine) a jami’ar Sheffield ta kasar Ingila, ya nuna cewa a hira da akayi da mutane sama da dubu hamsin (50,000), kashi 45 cikin dari (45%) na maza zasu so a kara musu girman azzakarinsu.
Sai dai ba a nan gizo yake saka ba. Abin tambaya shine, menene tunanin mata akan girman azzakarin maza? Prof. Wylie ya cigaba da bayani a cikin rubutun da yayi bayan bincikensa cewa akwai bambanci tsakanin tunanin mata akan girman azzakarin maza da kuma na mata. Kashi 85 a cikin dari (85%) na matan da akayi hira dasu a wannan bincike basu da matsala da girman azzakarin mazajensu. Prof. Wylie yace gano abinda ke burge mata abu ne mai tsananin sarkakiya da wahala, sai dai mafi yawan bincike da akayi sun nuna cewa girman azzakari yana can kasa a layin abubuwan da mata suke so a tare da maza.
Ance abinda suka fi damuwa dashi shine tsarin rayuwar mutum ko mutumtakarsa (personality) da kuma ado na jiki da kayan sakawa da sauransu. Prof. Wylie yace abinda mata suka fi damuwa dashi shine iya soyayya da nuna soyayya da kyautatawa da tausasawa da kuma lura da abubuwan da suka fi faranta musu kuma suka fi daɗaɗa musu ko kuma suke tsananin so da buƙata a rayuwa da kuma lokacin jima’i koda basu ambaci cewa kaza suke so ba.
A dunƙule abinda zamu fahimta shine ba dukkan matsalar kankancewar mazakuta ce take zama matsala a wajen jima’i ko kuma gamsar da mace ba. Hakazalika sanya damuwa a cikin rai saboda tunanin cewa azzakarinka karami ne zai iya haifar maka da depression, shi kuma depression zai iya haifar da matsalar rashin iya gamsar da matarka da sauran matsalolin jima’i.
Babban abinda ya kamata mutum ya mai da hankali akai shine ƙoƙarin sanin hanyoyin gamsar da abokiyar rayuwarsa koda ace azzakarinsa bashi da tsananin girma. Hakazalika dole ya cire damuwa a ransa, domin depression yana kawar da sha’awah (libido) sai mutum ya zama baya iya mikewa, idan kuma ya mike baya iya jimawa a tsaye (erectile dysfunction). Don neman bayani akan Depression, ka nemi rubutun da mukayi akan Depression a wannan shafi.
A takaice zamu iya cewa ba koda yaushe ƙanƙancewar mazaƙuta ke zama matsala ba. Sai dai idan ta haifar da wata matsalar daban. Sannan, zamu fahimci cewa kamar yadda Prof. Wylie ya faɗa, ƙanƙancewar gaba, ba a koda yaushe yake kawo matsala wajen gamsar da mace ba, matukar mutum ya iya gamsarwar kuma yana mai da hankali wajen yin haka.
Idan kuwa matsalar ta tsananta, ya kamata mutum yaje yaga likita. Idan likita ya tabbatar babu matsala ta jiki sai dai matsalar damuwa da tunani, to zai iya turaka wajen sex-therapist. Abinda sex therapist zaiyi shine zaiyi hira ne da mai wannan matsala ya kuma ɗaurashi akan hanyar da zai gane cewa bashi da wata matsala sai ta damuwa da kuma hanyoyin magance damuwar.
Akwai hanyoyi da ake ga suna taimakawa wajen magance matsalar kankancewar mazakuta duk da ba wai kai tsaye suke magancewa ba, amma suna taimakawa. Waɗannan hanyoyi sune:
a. Aske gashin gaba da tsaftaceshi domin wasu masana sunce rashin tsaftace shi da barin gashin yana haifar da kankacewar. Tsaftar azzakari ba zai samu ba sai an samu tsaftar kayan sakawa, musamman kayan ciki (underwears). Yana da muhimmanci a rika canza boxers akai-akai. Abinda ake so shine idan ka saka yau, to kar ka barshi a jikinka ya wuce awanni 24 baka cire ka saka wani wankakke ba.
b. Rage qiba da yawan motsa jiki yana taimakawa masu matsalar kankancewar mazakuta. Ajiye tumbi yana sanyawa mazakuta tayi kamar ta kankance.
Akwai hanyoyin da ake bi wajen ƙara girman gaba (penis enlargement), sai dai duk ciki babu wanda binciken kimiyya ya tabbatar da cewa yana samar da abinda ake nema ba tare da matsala ba. Wasu sukan taimaka wa kwakwalwar mai wannan matsala ne ta saba da cewa bashi da wata babbar matsala sai ya kwantar da hankalinsa. Wasu hanyoyin kuma kamar surgery koda anyi, daga baya girman azzakarin yakan koma yadda yake daa ko kuma su haifar da matsalar da tafi ta daa.
Girman azzakari ba shine tabbacin mutum zai gamsar da matarsa ba, hazakalika kankancewarsa ba shine yake nufin ba zaka gamsar da ita ba. Akwai masana da suka ce tsananin girman azzakari ba abun so bane ga wasu mata, sai dai ma cutarwa. Mata suna da bambanci kuma hanyar gamsar dasu yana da bambanci. Ya zama dole ka zauna ka karanci matarka don gano abinda yafi gamsar da ita. Tattaunawa da ita ma ba laifi bane. Gamsarwa maudu’i ne mai zaman kansa. Idan Allah ya bamu daama, zamu tattauna akai in sha Allahu.
Allah ya bamu lafiya da zaman lafiya.
No comments:
Post a Comment