ASSALAFY ISLAMIC MEDICINE CENTER Muna Rukya, sannan kuma muna saida Magunguna na Musulunci da na Gargajiya, sannan kuma muna hada magunguna , musamman wadanda suka shafi na sihiri, Jinnu da sauransu. Muna hada mayukan gyaran jiki, magunguna da suke kara Ni'ima, girman Nono, Hip Up, Man Vaseline...etc kuna iya kiran Mu ko whatsapp: +2347016433333, +2347039620000 youtube: https://youtube.com/c/assalafyislamicmedicinecenter
Tuesday, June 9, 2026
CIWON HANTA
ALAMOMIN CIWON HANTA,DA KUMA MAGANINTS
Ciwon hanta na daya daga cikin manyan cututtuka da suke da wuyar magancewa a duniya amma da Yardar Allah duk Wanda yabi abun da zamu fadi za'a samu waraka da Yardan Allah.
ALAMUN CIWON HANTA
Akwai matsanancin ciwon kai da ciwon malariya da typhoid akai-akai, Haka zakaji ciwon jiki da rashin karfin jiki, ciwon ciki mai tsanani,Yawan haraswa dakuma tashin zuciya koda ruwa kasha,
Ido yakanyi yellow, da rashin dandano a baki, fitsari ya koma yellow, ko matsananci zazzabi da jin sanyi ,bayan gidan mutum yakan koma kalan kasa.
Ga duk Wanda yaji wadannan alamu sai yayi kokarin zuwa asibiti domin Gwaji A daina tsoron gwaji domin magance cutar tana farkonta yafi sauki akan sanda zata tsananta.
Masu ulcer dake yawan ciwon ciki da yawan haraswa da tashin zuciya suna magani ba sujin sauki suyi kokarin duba lafiyar hantar su domin takan hadu da masu ulcer sosai.
MAGANINTA
1. A samu garin habba cokali 10
2. Garin Sidir cokali 5
3. Garin tin cokali 5
4. Garin bawon kankana cokali 10
5. Garin Citta cokali 1
6. Garin tafarnuwa cokali 1
7. Garin Hidal cokali 5
8. Garin zogale cokali 3
9. Garin Yansun da raihan da kusdul hindi cokali 6
Sai a hadasu waje daya a samu Zuma lita biyu mai kyau sai a zuba ciki a juya a hadu sosai sai a dinga shan cokali uku sau uku a rana.
Fadakakarwa
A guji amfani da nama musamman Jan nama da sauran abun mai ciwon hanta baya bukata.
GYARAN FUSKA
Maganin kuraje pimples da habbatisauda
Domin magance matsalar kurajen fuska wanda ake cema pimples.
Za'a samo garin habbatisauda sai ahada da man simsim sai kuma ahada shi da garin alkama cokali daya, sai ashafa a fuska idan zaa kwanta, da safe kuma sai awanke fuska da ruwan dumi, da kuma sabulu, malam mutum zai cigaba da yin wannan har zuwa Sati daya.
Malam yace kash inama da ace bayan haka kuma kasamo zait habbatil baraka kana zubawa kadan acikin wani nauin abin shanka mai sanyi. Insha ALLAH dakayi mamaki.
MAGANIN KURAJEN FUSKA
Matsalar kuraje da tabon fuska sun fi shafar matasa, mata da maza.
Wani lokaci sai an sha wahalar magance kurajen fuska, amma sai tabo ya ki bacewa.
Rashin bacewar tabo a fuska na bata kwalliya.
Sau da yawa za a ga ba a son shiga taron mutane domin wadannan tabon.
Da yawan mutane sun gwada mayukan kantin, domin rabuwa da tabon fuska.
Wasu sun yi sa’a wasu kuma ba su yi sa’a ba.
A yau mun zo da bayanin yadda za a magance tabon fuska. Muna son a san cewa daya za a zaba daga cikin hanyoyin da muka lissafo, kada a hada su gaba daya.
Domin yin hakan zai kara lahanta fuska ne..
· A samu ganyen dogonyaro, sai a hada shi da kurkum, sannan sai a shafa a fuska. A jira tsawon minti 15, sannan a wanke da ruwan dumi.
· Za a iya shafa markadadden dankalin Turawa a kan tabo.
Hakan na magance kurajen fuska, sannan ya hana su sake fitowa.
· A daka tafarnuwa sai a shafa a kan tabo. Tafarnuwa tana wari, amma tana gyara fuska, sannan ta magance tabon fuska.
· a hada karas da tafarnuwa da zuma sai a shafa a fuska na tsawon minti 20 kafin a wanke.
· A samu hodar ‘baking soda’, sai a hada ta da ruwa, sannan a shafa a fuska zuwa minti 2 ko 3, daga nan a wanke fuska da ruwan dumi
Yadda za a magance tabo da kurajen
fuska...
.
Matsalar kuraje da tabon fuska sun fi shafar matasa, mata da maza. Wani lokaci sai an sha wahalar magance kurajen fuska, amma sai tabo ya ki bacewa.
.
Rashin bacewar tabo a fuska na bata kwalliya. Sau da yawa za a ga ba a son shiga taron mutane domin wadannan tabon.
.
Da yawan mutane sun gwada mayukan kantin, domin rabuwa da tabon fuska. Wasu sun yi sa’a wasu
kuma ba su yi sa’a ba.
.
A yau mun zo da bayanin yadda za a magance tabon fuska. Muna son a san cewa daya za a zaba daga cikin hanyoyin da muka lissafo, kada a hada su gaba daya. Domin yin hakan zai kara lahanta fuska ne.
.
A samu ganyen dogonyaro, sai a hada shi da kurkum, sannan sai a shafa a fuska. A jira tsawon minti 15,
sannan a wanke da ruwan dumi.
· Za a iya shafa markadadden dankalin Turawa a kan tabo. Hakan na magance kurajen fuska, sannan ya
hana su sake fitowa.
.
Ko a daka tafarnuwa sai a shafa a kan tabo. Tafarnuwa tana wari, amma tana gyara fuska, sannan ta magance tabon fuska.
Gyaran jiki
Sirrin yadda ake mallake Miji ya kauracewa zaman waje
“Kyautatawa game da tsare wa maza hakkokinsu ne babbar hanyar mallake miji.” Wata mata ce ta je wajen wani malami (mai tsoron Allah) ta ce masa “Allah Ya gafarta Malam so nake ka yi min aiki domin in mallake mijina.”
Sai malamin ya girgiza kai yana mai nuni da jan aikin da ke akwai. Ya ce mata zai yi mata aiki amma da sharadin in za ta kawo masa nonon barewa wanda ta tatso da hannunta.” An ce sa kai ya fi bauta ciwo. Matar nan ta yi shirya ta nufi dokar daji kuma ta yi sa’a ta iske wata barewa ta yi sabuwar haihuwa, sai ta samu wata itaciya ta haye sama ita kuma barewar da ’ya’yanta suna kasa. Sai ya kasance duk lokacin da barewar nan ta tafi neman abinci sai matar nan ta sauka ta dauke ’ya’yan nan daya bayan daya ta aje su gefe guda ta share musu wurin, ta dauke su ta mayar da su wurinsu na asali.
Duk lokacin da uwar ta dawo sai ta iske an share wajen sai ta yi mamaki, har ta kai matar nan tana jinkirta sharar nan har barewar ta dawo ta iske ta tana wannan aiki, haka za ta sa mata ido sai ta gama ta mai da su inda suke. Yau da gobe har ta kai matar nan tana shafa ’ya’yan barewar nan in suna shan nono har tana iya cire wani daga jikin nonon ta sanya wani. In gajarce muku labari saboda kyautatawa har matar nan ta zama tana sarrafa barewar nan duk yadda ta ga dama. A karshe ta dauko ’yar gorarta ta kara jikin nonon barewar nan ta tatsa ta cika ta tattara kayanta sai gida.
Bayan ta koma gida sai ta shirya ta nufi wajen malamin nan rike da gorar nono ta mika masa. Koda ya amsa sai mamaki ya kama shi ya tambaye ta yaya aka yi kika same shi?
Matar nan ta share wuri ta fada masa duk hanyoyin da ta bi har ta samu ta cimma burinta. Sai malamin nan ya gyara zama ya ce ta saurare shi da kyau da kunnen basira.
Ya ce “Har ga Allah duk abin da zai yi mata ba zai yi tasiri ba matukar ba ta bi mijinta ba ta kuma kyautata masa kamar yadda ta yi wa wannan barewa.”
Sai mamaki ya kamata ta ce “Ka fa san maza yadda suke da wuyar sha’ani.”
Sai malamin ya ce “Ta je ya ba ta nan da wata guda idan har ta aikata kwatankwacin abin da ta yi wa barewar nan ba, ta samu kan mijinta ba to ta dawo shi kuma zai yi mata aikin da za ta mallake shi har abada.”
Suka yi ban-kwana ta yi masa godiya ta koma gida. Bayan tsawon wata guda sai ta koma wajen malamin nan rungume da jaka wadda ta shake da kayan arziki ta mika masa kuma ta nuna farin cikinta ganin mafarkinta a yau ya zama gaskiya.
Daga karshe Malam ya ce mata “Wannan shi ne asirin da har abada ba zai kare ba, sai ma karin tagomashi na yardar Allah da za ki samu.”
Domin Annabi (SAW) ya ce “Duk matar da ta mutu alhali mijinta yana mai yarda da ita to za ta shiga Aljanna.” Da wannan nake kira ga matanmu su ji tsoron Allah. Wallahi zuwa wajen boka kafirci ne kuma duk wacce ta mutu a wannan tafarki wuta ce makomarta.
Allah Ya tsare mana imaninmu, Allahumma amin. .
Mu'jizar da dake tartare a cikin albasa
Amfanin Albasa a jikin Dan adam.
1.Tana Yaki Da Cutar Daji (Kansa) Sakamakon da aka samu daga binciken da aka yi, ya nuna cewar,albasa ta kasu daban daban, saboda an sansu da maganin cutar kansa, musamman ma yadda take girma. Bugu da kari duk dai dangane da binciken da ka yi, idan na mafani da ita akai akai, tana rage yiyuwar kamuwa da cutar kansa daban daban, kamar kansa ta colorecta, oral kansa, kansar mkogwaro, kansar ciki, kansar wurin da abinci ke biya wuce zuwa hanji, sai kuma kansar mahaifa.
2.Tana Yaki Da Cutar Daji (Kansa) Sakamakon da aka samu daga binciken da aka yi, ya nuna cewar,albasa ta kasu daban daban, saboda an sansu da maganin cutar kansa, musamman ma yadda take girma. Bugu da kari duk dai dangane da binciken da ka yi, idan na mafani da ita akai akai, tana rage yiyuwar kamuwa da cutar kansa daban daban, kamar kansa ta colorecta, oral kansa, kansar mkogwaro, kansar ciki, kansar wurin da abinci ke biya wuce zuwa hanji, sai kuma kansar mahaifa
3.Albasa na rage sikarin dake cikin jini Jini wanda ya kunshi sikari mai yawa(hyperglycemia) wannan yana kasancewa ne, lokacin da jinin da ke cikin sikari da ake kira (glucose), yayi yawa fiye da yadda jiki ke bukata, domin yin aiki da shi kamar yadda aka saba. Wannan yanayi shi ne ka sani da samar da matsala nan da nan da kuma wadda ke daukar dogon lokaci. Amfani da Albasa kusan kullun ya nuna cewar tana sa sikarin da yake cikin jini ya ragu, saboda ta kunshi wani sinadarin allyl prppyl disulfide, wanda yake taimakawa, wajen rage yawan glucose, ya kuma kara yawan sinadaran insulin.
4.Tana Kara Karfin Sinadaran dake taimakawa wajen yakar cutar Kamar yadda Anne Maune anda shi kwararre ne danagne da kayayyakin abincin, mai zama a Washington DC, ya bayyana cewar akwai poly phenolds a cikin albasa wanda yake aiki kamar sojojin da ke yakar cutar cuta da ake kira free radicals.
Shin kina da Matsalar da yake damunki?
- zuma cokali 5
- man tafarnuwa cokali 2
INA MAFITA
Amfanin Kanamfari Guda 11
Amfanin Kanamfari Guda 11 YADDA ZA'A YI AMFANI DA KANUMFARI WAJEN NEMAN LAFIYA 1.CIWON KAI (A), Yana maganin ciwon kai. A shafa ...
-
MAGANIN SANYI MAZA DA MATA 1. ALAMOMIN CIWON SANYIN MARA NA MATA / SANYIN MATA WANDA AKE YAƊAWA TA JIMA'I* 📗📗📗📗📗📗📗📗📗...
-
YADDA NAMIJI YAKE INZALI, HAKA ITA MACE TAKE YI akwai banbanci tsakanin inzali na mace Dana namiji domin yanzu matsalarda wasu mata ke ciki ...
-
HANYOYIN 10 MAGANCE INFECTION ‘Yan Uwana Mata barkan mu da sake saduwa daku a cikin wannan fili namu mai matukar farin jini, wato Sirrin G...






